67

4.3K 409 52
                                    

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

67


A gurguje....

Bikin uwani da yusuf sai matsowa yake yayin da iyayen ke iya bakin qoqarin su na ganin ta nutsu, kuma alhamdulillah abin yana ragewa kadan kadan.

Surayya tun tana damuwa tana kuka har ta daina ta xubawa sarautar Allah ido, tana so taga yanda xamanta xai kasance da uwani duk da ba gida daya bane.

Hajiya sai faman gyaran amarya take, uwani na faman washe baki, ashe hajiya na sonta take boye mata, lallai jiddah tayi mata baqin ciki domin bata mata wannan gyaran ba shiyasa akace kishiya abin tsoro da gudu ce, wai uwani ke cewa kishiya abin gudu ce🤔

Duk ranar da hajiya ta manta ba ta bata ta sha ba ita da kanta take tuna mata, hajiya bata mamakin rashin kunya irin na uwani tunda tasan ko wacece ita.

Ba suyi wani dogon biki ba kasancewar kowa yasan uwani baxawara ce🤪, duk bikin da ake jiddah ta halarta kuma sosai ta bada gudumuwar ta, banan ma taje da jiddah ta gayamata,

Ta bawa uwani gudumuwar hadaddiyar cooler mai kyau da tsada, amma uwani ta rena.

An gaya maki abbana bai siyamin inda xan sakawa mijina abinci ne, qila ma kin xubo kayan mallakar miji aciki na xuba abinci na basa ki mallake min shi.

Banan tace subhanallah anty uwani, kin manta ina da aure bayan wannan ma ni ban taba bin boka ko malami ba a rayuwata, ashe har yanxu baki canxa hali ba.

Uwani ta tashi tana fadin, me kike nufi kina nufin ina da wani mugun hali ne, waye ma ya gayyace kixo min biki, banda baqin ciki ki rasa abin bani sai wannan cooler ni kayan mata nake so na gyara kaina kar na xamo bora a gaban miji.

Banan girgixa kanta kawai tayi sauqin ta ba kowa a dakin sai su biyu kawai da ta kunyata a yau, banda anty jiddah me ma xai saka taxo bikin uwani, jiddah ta shigo da sallama tana fadin hayaniya nake ji me ya faru?

Uwani tayi caraf tana fadin, anty jiddah wai banan fa mai aikin mu ta waye har tayi arxikin da xata kawo min gudumuwa dubi fa.

Jiddah tace laifine dan ta kawo maki? Ita da ta tashi yin nata nawa kika bata, ba dan ni ba kina tunanin ma xaki qara ganin banan, meyasa kike haka, meyasa har yanxu kin kasa nutsuwa kisan me kike?

Kina goyon bayanta kenan, ni xan dauka haka ba dan halin ta ba albarkacin kine, ni duk mai min baqin ciki na gano sa Allah bana iya xama dashi.

Jiddah tayi caraf ta kwace cooler tana fadin baki isa ba, ta miqawa banan, koma da ita gida baxaki bata ba, idan kinyi niyar kyautarwa ne kibawa hajiya.

Banan ta karba tana fadin shikenan anty jiddah, uwani ta bita da kallo cikin mamaki da haushi dan tama rasa wane irin baqin ciki ne jiddah take mata haka, amma xasu hadu...

An daura auren yusuf da uwani, kuma a ranar xaa wuce da amarya.

Tun da aka xo daukar amarya ake ta daru taqi ta shiga mota ita lallai sai akan sabon vespa din ta xaa kaita gidan mijin ta.

Wai wace irin mata ce yusuf ya aura haka?cewar daya daga cikin mutanen da suka xo daukar amarya.

Dayar tace magana ne kawai banyi ba, amma tun ranar da muka xo kawo lefen ta na gane bata da kunya da nutsuwa, banda iskanci ina aka taba daukar amarya daga kaduna har abuja akan vespa?

Tsohuwar tace lallai da sake, wallahi da nasan tun farko matar da yusuf yake nema kenan da baxai aure ta ba, yanxu ma bata baci ba xai iya sakin ta.

El'mustapha Where stories live. Discover now