27

3.9K 286 6
                                    

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

_dis page is 4 u pherty novels and musha karatu, I heart u ol❤_

27

Jin motsin fitowar el'mustapha ya sakata juyawa tana kallonsa, shima kallonta yake,

'keda waye naji a dakin nan kuna magana,

'amarya ce, ina ji kai take nema bata jima ba ta fita.

Ya tabe bakinsa, ya qaraso yana kallon takardar dake hannun jiddah,

'Wannan takardar mecece?

'nima yanxu na ganta bansan ko ta mecece ba, ta soma warwarewa, el'mustapha ya karbi takardar da sauri yana fadin.

Jiddah kira min uwani yanxu.

Me ya faru,

Just call her.

Bata qara mgn ba ta fita, bata jima ba sai gata ta dawo tare da uwani a bayanta, wannan karon ma da carbin ta a hannu.

Yanda uwani ta gansa yayi matuqar bata tsoro, fuskarsa a daure, bama wannan ba ita kam duk iskancinta bata taba ganin namiji haka a gabanta ba, sai ta buya bayan jiddah,

Fito nan, ya nuna mata gabanshi,

Wayyo Allah, anty jiddah ki bashi haquri, kice ya saka rigar shi.

Jiddah ta dan dubeshi cikin marairaice fuska, sai kuma taje ta dauko masa doguwar riga, kamar baxai saka ba ya xura yana kallon uwani.

Takardar da na baki saboda kin rainani, sai kika kawowa matata ko?

Kayi haquri baxan qara ba,

A tunaninki menene acikin takardar?

'Na dauka saki ne aciki,

Kin dauka saki ne aciki shiyasa kika kawowa jiddah,

Aa bahaka bane,
To meyasa kika kawo takardar, saboda kin rainani ko, ba laifin ki bane, fara yimin tsallen kwado anan kafin na hau kanki da duka.

Da sauri ta fara hade da riqe kunnuwanta,

Wayyo Allah hajiya, an taru anci amanar aure saboda an ganeni qaramar yarinya.

El'mustapha bai kula taba xama yayi yana shafawa jikinsa mai, jiddah kuwa jikinta yayi sanyi saboda tausayin uwani, duk ta wani koma kalar tausayi kamar xatayi kuka itama takeji ganin uwani nayi.

Hajiya... Hajiya.... Kixo karsu kashe maki ni, wayyo ni Allah maqiya sun sakani a gaba xasu ga bayana, saboda baa sona anga bani da kowa.

Murmushi el'mustapha yayi yana kallon uwani, kuka take idanunta a rumtse take maganar.

'Dan Allah el'mustapha ka kyaleta,

Kallon mamaki yakewa jiddah, lallai har yanxu jiddah bata san kanta ba, yarinyar da ke neman fidda ta a gidan take tausayi yaga alamar Sam bata damu da abinda uwani tayi ba, yana so yasani shin har yanxu jiddah bata san kanta bane ko me?
Bata san halin da take ciki bane game da uwani, xaiyi magananin ta ya gani ko ina hankalin ta ya tafi.

Ya dubi uwani,
Xo nan uwani,
Da sauri taxo gabansa tana fadin kayi haquri.
Karbi takarda hannun jiddah taki ce kuma ba saki bane aciki, takardar yarjejeniyar auren muce idan kikayi wasa da ita tamkar kinyi wasa da auren kine kin fahimceni.

Ta gyada kai gwani tausayi tana kallonsa, tashi ki bace min da gani,

Ta tashi sai da ta kai bakin qofar ta juyo, Allah ya isa kuma human rights xanje yanxu abimin haqqina... ta fita da gudu, murmushi kawai el'mustapha yayi shi yanxu uwanin Ma ta fara birgesa, abubuwanta akwai nishadi aciki.

El'mustapha Where stories live. Discover now