37

4.5K 384 61
                                    

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞


37

Ya fito harabar gidan yana kallon securities,

Kada kubari uwani ta fita a gidannan, idan kuka yi wannan saken a yau wlhy ran ku xai yi matuqar baci fiye da kuskuren da kuka yi a farko.

Ya isa ga motar sa dai dai lokacin da wayar sa ta dauki qara, yana dubawa anty ikram ya gani, yayar sa.

Ya dauki wayar bayan ya kara a kunnensa,

'autan mama, kaxo asibiti jikin mama yayi tsanani sai sunan ka take kira.

Ya tsinke wayar batare da yayi magana ba, da sauri ya shiga motar ya bar gidan abinda ya mantar dashi xuwa mtn office kenan🤦🏻‍♀.

Uwani tun daxu tsaye take, ta kasa xama ta kasa gasgasta abinda kunnuwanta suke jiye mata, el'mustapha yayi mata saki biyu, aa bata yarda ba kunnuwanta basu jiye mata da kyau ba.

Jikinta ya dauki rawa, lokaci daya xaxxabi mai xafin gaske ya taso ya rufe ta, jikinta yayi xafi rau, da kyar ta isa bakin gado ta xauna, sai ga hawaye sharrr na bin kumatunta.

Ji take duniyar ta mata xafi, duniyar Ma gabaki daya juya mata take, wani duhu ya mamaye idanunta, duk wani motsi ko sauti bata jinsa a kunnuwanta, sai ta gigice ta fashe da kuka mai tsananin gaske kukan da bata taba irin sa ba,

Ta rasa el'mustapha har abada, ta rasa wannan abin da take matuqar so da qauna, ta rasa wannan abin da take gani tana gab da samuwar sa, ta rasa wannan abin da ta wulaqanta yar uwarta saboda shi, ta rasa wannan mutumin mai matuqar tsada da muhimmanci a rayuwarta, el'mustapha yayi mata nisan da har abada baxata taba samun sa ba, ba ita kadai ba har jiddah ta gama samun sa, idan ta rasa shi shima xai rasa jiddah, jiddah Ma xata rasa shi, kowa ya rasa, indai tana numfashi a doron qasa el'mustapha da jiddah baxasu taba kasancewa tare ba.

Idanunta suka yi jawur saboda kuka,  da kyar ta janyo wayarta ta soma neman layin jamcy, kusan sau biyar tana kiran layin baya shiga, ta tashi da kyar ta xura doguwar riga, qaramin mayafi ta dora akan ta, key din motar ta kawai ta dauka ta fito da kyar tana layi saboda axababben ciwo da kanta keyi.

Horn tayi alamar a bude mata gate din, amma aka qi, tayi magana suka gayamata abinda el'mustapha yace, bata damu ba saboda yanda take jin jikinta, tana komawa dakin ta ta fadi ragwaf, xaxxabi mai xafin gaske ya rufe ta.

El'mustapha kuwa yana isa asibitin kai tsaye ICU ya nufa,

Gaba ki daya mama ta fita hayyacinta ba abinda ke fitowa bakinta sai el'mustapha, hannunta ya hada da nashi bayan ya tsugunna a qasan gadon da take kwance.

Magana take yi a hankali da kyar yake iya jiyo abinda take fada, da alama wasiya take bashi musamman akan yayyunsa da yan uwansa, ya rumtse idanunsa sai ga hawaye na xuba, jikinsa ya dauki rawa lokacin da yaji tana kalmar shahada, kafin wani lokaci numfashin ta ya ajiye.

Ya bude idanunsa sosai yana kallonta, no he can't believe it, mama ta mutu yanxu a hannunsa, ya soma jijjigata a hankali yana kiran sunan ta.

Da kyar nurses suka fitar dashi dakin,

Idan el'mustapha dake namiji yayi kuka akan mutuwar mama, mu da muke mata mu ce me? Cewar anty ikram tana kallonsa bayan ta riqo hannunsa.

'Anty yusrah tace ba kuka xamuyi mata ba addua ce, kukan mu baxai amfanar da ita da komai ba, kuma ta roqa ko bayan ranta kada muyi mata kukan mutuwa.

'Anty ikram da kanta ta soma share masa hawayen, a yanda el'mustapha yake jin kansa tamkar qaramin yaro, yau ya rasa maman sa, yayi kukan mutuwa a karo na biyu bayan na baban sa, bai san wanene na uku a rayuwar sa ba.

El'mustapha Where stories live. Discover now