55

4.9K 415 54
                                    

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞


55

Saukar su Nigeria ke da wuya, motocin gidan El'mustapha suka iso airport.

Cikin masu tarbar su jiddah harda su anty ikram da yusrah,

Cike da tsananin mamaki suka rungumeta suna kallonta qasa da sama, kamar bata taba samun wata lalura tare da ita a qafar ba.

Welcome back jiddah, Allah ya qara lafiya mai amfani cewar Nabila tana kallonta cikin murmushi.

Jiddah kallonta tayi tana fadin kin goge laifin ki na rashin xuwa duba ni a Germany, kika xo tarbata, naji dadi sosai Allah ya bar xumunci.

Amin ta fada cikin murmushi.

El'mustapha yayi gaba da baby rungume a jikinsa, Allah kadai yasan irin farin cikin dake xuciyarsa.

Suna iso wa gida sunyi mamakin samun mutane haka duk yawanci daga gurin aikin el'mustapha ne sunxo taya sa murna, kuma sosai ya nuna farin cikin sa,

Shiru jiddah tayi tana kallon gidan bayan ta fito, ba abinda ya canxa daga gidan yana nan yanda ta barshi, Alhamdulillah take nanatawa a xuciyarta yafi a qirga na murnar dawowar ta gida cikin qoshin lafiya tare da dimbin nasarori da ta samu.

Ji tayi an rungumeta, ko baa fada ba tasan twins din tane,

Welcome back mummy, we miss you,

Ta sunkuya tana kallonsa cikin tsananin tausayinsu yanda suka rungumeta sosai a jikinsu,

Mummy baxaki qara xuwa ki barmu ba ko? ta gyada kanta tana murmushi.

Da kyar suka barta suka nufi inda el'mustapha, sai tambayar sa suke baby waye, ya kyale su.

A falo suka yada zango, hajiya kam a gajiye ta nufi dakin baqi, duk falon ya cika da yan uwa cikin farin ciki.

Mummy baby waye a hannun daddy cewar aryan,

Arham yace mummy kice daddy ya ajiye ta ya dauke ni, tun daxu bai cirani sama ba nayi masa oyoyo.

Aryan yace mummy  wheel chair dinki yana dakin daddy, kixo ki xauna ni xan riqa tura ki.

Banda murmushi ba abinda jiddah keyi, falon kuwa sai dariyar yaran ake yi.

Banan tayi sallama ta shigo, da murna ta isa inda jiddah ta rungumeta tana mata sannu da xuwa,

Jiddah ta amsa sama sama,

Tace anty jiddah me kike so na kawo maki, nayi maki girki Kala Kala irin wadanda kike so.

'ki barshi anjima xanci.

Batare da tunanin komai ba banan ta juya tana kallon el'mustapha dake ta surutu da twins, ta saki ajiyar xuciya kamar wacce ta dade tana neman abu bata samu ba sai yau,

Tace yaya me xan kawo maka ka ci, kafin yayi magana jiddah tayi caraf tace ya qoshi ki tashi ki tafi idan yana buqata xan neme ki.

Banan ta tashi jiki a sanyaye ta nufi kitchen kamar xata dauki wani abin, leqen sa ta soma yi, Allah ya jarabceta da son el'mustapha ta kai har bata iya boye feelings dinta akansa, ina ma jiddah xata fahimce ta, ina Ma jiddah xata bata dama kamar yanda ta baiwa uwani saboda baxata taba nadamar aura mata el'mustapha ba, bata da niyar cutar da jiddah ko wani abu nata xama take so suyi na amana, amma jiddah taqi ta saurara mata kamar Ma ta tsaneta a yanxu.

Allah ka cire min son wannan bawan Allah idan ba alkhairi bane.

Yusrah ta tashi tana fadin, anty ikram xan tafi ina so na dauko su amira skul,

El'mustapha Where stories live. Discover now