24

3.9K 299 12
                                    

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

_Oh ni Bintu ashe haka Uwani keda masoya all over, sai xancen ta kuke yi, to kubarta haka kada ku cinyeta ku hana mata qiba a gidan mijinta_🤤

24


Tun da kina ganin ban miki gata bane uwani kije ki hada da kanki, ta wannan fannin banda kwari akai, ta fada cikin takaici da kishin uwani, lallai yarinyar nan bata da kunya.

Uwani ta dafe qirjinta tana fadin ni xuciyata ke min xafi anti jiddah duk na nemi abu ban samu ba sai ta dinga min xafi.

Ina ji wannan karon kam idan kika fadi anan, nan xaki cigaba da kwanciya ba wanda xan saka ya kaiki asibiti, abin naki ya xama rainin wayo tunda baki da kunya, ta tashi ta fice fuuu, uwani ta bita da kallo to ko anty jiddah ta fara kishine, bari na lallaba matar nan har a daura auren kada ta bore ta fasa.

El'mustapha yana dakin sa kwance, komai na jiddah mamaki yake basa yanda ta jajirce ga wannan auren, shi kansa yasan qarfin hali take yi amma yasan jiddah sa game dashi bata da haquri akan kowace mace, lallai uwani ta taki sa'an auren el'mustapha sai dai kam xaman ne bamusan yanda xata kaya ba.

El'mustapha shiru kawai yayi a saman gado idanunsa a lumshe har lokacin da jiddah ta shigo dakin,

Kallon sa take tana jin wani sonsa da kishinsa, wai yau el'mustapha ta xai xama mijin wata, watan Ma uwani, batare da tayi magana ba ta juya ta nufi kitchen domin hada breakfast, duk abinda take el'mustapha na kallon ta, yasan kishine ke dawainiya da ita, da shine ya bijiro da aure nan da yanxu yasan babu xaman lafia a tare da jiddah sa.

Dakin dasu banan suke a bayan gidan ta nufa, maaikatan sai gaidata suke cikin girmamawa yara da manya, cikin sakin fuska take amsa masu kamar yanda ta saba, tsofaffin Dany take barkwanci da su kuwa suna tabawa suna dariya kamar wacce bata da damuwa a tare da ita.

Ni kam tun jiya banga banan ba, lafiya dai ko.

Ai banan bata lafiya hajiya tun jiya tana fama da xaxxabi.

Subhanallah amma shine ba wanda ya sanar dani, ta shiga dakin tana fadin tasha magani kuwa.

Banan na kwance xaxxabi take, tun lokacin da taji ana maganar uwani xata auri el'mustapha, ta riqo hannu jiddah jikinta yayi xafi rau sai makyarkyata take,

'Anty jiddah wai da gaske uwani xata auri Alhaji?

Eh mana yau ake daurawa Ma, me akayi.

Banan ta fara hawaye sosai, anty jiddah kar ki barta ta aure sa dan Allah.

Meyasa banan
Saboda ita muguwa ce, bata da tausayi bata dace dashi ba.

Jiddah ta share mata hawaye, ko kadan bata da kyankyami akan masu aikinta, ta riqo banan sosai, tace uwani ta canxa kuma xakiyi mamaki kada kisa damuwa a tare dake, uwani kuma taimakonta xanyi dalilinsa ta kamu da ciwon xuciya.

Banan tayi shiru kenan itama idan anti jiddah taji dalilin el'mustapha ne bata da lafiya itama xata barta ta aure sa, no baxan iyama anti jiddah haka ba xan cigaba da boye mata koda kuwa sonsa xai xama ajalina cos nasan el'mustapha baxai taba son Irina ba, ina Ma ko sau daya ne na ganshi, tunda nake gidannan ban taba ido da ido dashi ba sai dai kallo daga nesa.

Tashi ki shirya yanxu xaa kaiki asibiti kinji banan.

Ba musu kuwa ta tashi ta soma shiryawa, jiddah na fitowa sashen kitchen din ta tanufa,

Har ta gama shirya masa breakfast wani abu na nan a qirjinta ya tokare mata,wai ita ce da kishiya a yau, anya tayi Saar xuwa duniya kuwa, ko da yake itace ta jawa kanta, amma ita da xuciya daya tayi taimakon kuma tasan baxata taba tabewa ba.

El'mustapha Where stories live. Discover now