36

4.4K 360 63
                                    

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞


36

Bayan sati biyu

Cikin kwanakin da  jiddah tayi ta dawo wata iri, tayi kuka har ta godewa Allah, bata da wani tunani a xuciyarta yanxu sai na mijinta da twins nata.

'Ashe gaskiya el'mustapha yake gaya mata game da uwani, uwani ba mai qaunarta bace, yanxu ne ta gano abinda el'mustapha ke nuna mata a lokacin yake son ta gano, kenan yasan uwani qaryar ciwo take masa domin ta cutar da rayuwarta, she didn't deserve dis hatred from uwani.

Ta soma kuka mai fitar da sauti, mai nuna alama da baqin cikin dake tattare da xuciyarta, tayi nadama kuma ta tsani uwani a rayuwarta, tana jin baxata taba yafewa uwani ba, yau gashi ta dalilin uwani ta kasa sarrafa qafar ta daya, ta raba ta da ya'yanta da mijinta, ta raba ta da jin dadin ta, an kawo ta an girke inda babu kulawa cikin qartin maxa, ta kwana dasu ta yini dasu, basu da aiki sai shan barasa da chacha, sallah Ma a xaune take yin ta shima wai sai sanda suka ga dama suka kawo mata abinci da ruwa take yin rarrafe ta shiga toilet da kyar tana kuka.

Yanxu kuma taji cikin yayi mata wani iri, ya qara nauyi, motsin da yake yi a da yau kam bata jisa ba,

Ya Allah ka raya min abinda ke cikina, ta maida kanta jikin gwiwowinta tana kuka sosai.

Tana haka goga ya shigo, shi dai Allah ya sanya masa tausayin jiddah, sati biyu da yayi tare da ita ya gane tana da sanyi, tana da nutsuwa da kamun kai sosai yanda take ta rufe jikinta da hijab a duk lokacin da xasu shigo.

Bata da rawar kai duk sanda xasu shigo sai ta gaidasu kuma kome suka ce bata masu gardama illah ta gyada kanta wannan dalilin ya saka kurma jin tausayin jiddah a karo na farko a rayuwarsa daya taba tausayin wata halitta.

Ya xuqi sigari yana kallon jiddah,

Tunda uwata ta haifeni ban taba tausayin kowa ba sai ke, saboda sanyin ki da haqurin ki na lura ke Sam baki da hayaniya, sabanin wasu mata da muke kawo wa nan, daga masu tsiwa sai yan iska ni kuma tattakasu nake, na sa belt na xane shegu idan kuma yarinya ta matsamin na dauke ta da alburushi wanda ya kawo ta yamin maganar banxa na kashe shi haka nake kurma game da kissa.

Jiddah ta sunkuyar da kanta tana share kwallah,

Saboda cikin da ke jikinki xan tausayamaki, na dauko maki tsohuwa a cikin gari xata kula dake kullum na maidata dan baxata xauna dake ba, idan kina jin fitsari ko kashi ki daina rarrafawa ita xata kula da komai, waccan shegiyar matar da ta bamu ajiyar ki itace xata biyata dan ubanta, ta biyamu ta biya wannan tsohuwar tace yau xata xo ta kawo kudin, in kuma qarya take min wlhy cikin ta xan farke har cikin gidan mijin nata, yama kika ce sunanki.

Hauwa ta bashi amsa kanta a sunkuye dan bata qaunar ganinsa ko kadan.

'Yauwa sunan uwar babana ce amma ana ce mata kuluwa dan haka kuluwa xan riqa kiranki dan ni bana girmama kowa a rayuwata, uwata Ma kai tsaye nake kiranta da Ladidi, ya juya ya fice yana tangadinsa na maye, jiddah tabi bayansa da kallo tana sharar kwallah.

Baa jima ba taji uwani a gidan, tana jin su suna kururuwa sunga kudi.

Ina kika sami kudin bayan kince baki dasu,

'Na mijina ne na dauko jiya bayan ya fita😀

Kinyi qoqari, saura na waccan tsohuwar dana gaya maki tana kula da kuluwa, dubu dari biyu ne kudin ta.

Uwani ta bata fuska, batayi magana ba saboda tsoron kurma tasan tsab xai iya dukanta a gurin idan ta musa, sai tace idan xata dawo xata xo dasu.

Suka bude kudin suna dubawa suna jin dadi.

El'mustapha Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt