60

5.2K 493 81
                                    


On your birthday, I wish you a year with loads of fun, excitement and beautiful memories. Happy birthday Girlfriend Baby Bello🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂


60


Pringles din fa?

El'mustapha ya tambaya yana kallonsa,

Baxan ci ba sai gobe,

Yace tor shikenan, ya riqa hannunsa suka nufi dakin sa,

Daddy yau tare xamu kwanta ne?

Ya gyada kai yana kallon yaron,

Ya xauna yana dialing number jiddah, tana fara ringing yaji an kashe gabaki daya, ya dafe kansa, arham ya kwanta jikinsa yana fadin,

Daddy baka sakamin kayan barci ba, kullum momy sai ta sakamin kafin na kwanta.

El'mustapha ya tashi cike da damuwa yace cire kayan kafin na dauko ma kayan barcin naka,

Bai jima da fita ba ya dawo yana fadin,

Meyasa baka cire kayan ba arham,

Daddy ni bana iya cirewa,  el'mustapha ya xauna yana cire masa kayan, ya saka masa na barci ya dubesa har yanxu jikinsa akwai xafi, suka kwanta.

*

'Washe garin ranar koda suka tashi jiddah ta gama komai na breakfast ta ajiye masu, ta shigewar ta dakin ta rufe., koda suka yi wanka suka fito ta gama komai amma bata falon.

Arham ya sami lfy amma ba qarfin jiki, ga maganin sa a falo amma bai san kansu ba, ya dauke sa suka yi breakfast, ya dawo yana buga qofar jiddah taqi budewa.

Yayi juyin duniya yana rarrashinta amma tayi masa banxa, tunanin sa jiddah bata ci abinci ba tun jiya kada wani abin yaxo ya same ta.

Ya kira anty ikram ya gayamata itama tayi kiran jiddah taqi dauka kuma taqi ta kashe wayar,

Cikin damuwa ya qara xuwa bakin qofar, kome kike ji jiddah ki fito kici abinci ba danni ba please,

'Ko alamar motsinta bai ji ba, yaji kamar ya bige qofar dakin.

Kusan goma na safe anty ikram taxo gidan, tayi magana tayi rarrashi ta dawo fada duk jiddah bata bude qofar ba, idan har suna son ta sun damu da rayuwarta saboda me xasu dawo da uwani.

Anya yarinyar nan tana da rai kuwa ko motsin ta bana ji cewar anti ikram tana kallon el'mustapha.

Yace lafiyar ta qalau sister tunda baki ji kukan airah ba kinsan ta da fitinar tsiya, ni ban sani ba ko jiddah taci abinci ne?

Kaima da laifin ka el'mustapha, yarinyar nan an maidata saboda me xaka ce ta dawo, baxaka iya shirya wannan yarinyar ba tun da safe sai da sukayi dambe da mai aikina wai bata kai mata ruwan wanka ba, ban sani ba ko na dauki mai aikin ne saboda ita, kawai sai ta fara dukan yarinyar mutane,

Ta juya a fusacce tana fadin ko menene laifin kane idan ma son yarinyar kake tun wuri ka cire sonta a xuciyarka na gayama baxaka taba maida wannan yarinyar ba wadda tayi yunqurin kashe yar uwarta da gudan d'anka ai da yanxu babu arham banda taimakon Allah.

Yace sister tafiya kuma xakiyi keda na ki.... tayi saurin katse sa,

Xaka bani headache ne el'mustapha, laifin kane wannan karon bansan me kake so nayi ma ba, nayi magana taqi budewa so kake nayi ta tsayuwa? Idan naje gida xan gwada kiran number ta inta dauka xan mata magana.

Yayi shiru baiyi magana ba ta fice ya xauna yana shafa kan arham,

Daddy meyasa mummy bata fito ba,

El'mustapha Where stories live. Discover now