28

4K 311 13
                                    

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞


28

Ko kadan uwani bata ji tsoron ganin sa ba ko alamar firgita a tare da ita,

'Na nawa xaa baka? Shine abinda ya fito bakin uwani lokacin da take kallonsa.

Murmushi el'mustapha yayi a ganinsa girmansa ya fadi ya tsaya cece kuce da uwani a waje,

Ya ciro dubu daya yana fadin, bani ta dubu daya ina jiranki yanxu.

Uwani ta washe baki, Banan bude masara ga costumer na kwarai wanda ba baqin ciki a tare dashi, kinji har ta dubu xai siya.... Uwani ta fada tana bude masarar🌽🌽🌽

El'mustapha juyawa yayi ga wacce yaji an kira da banan, yana jin sunan ta abakin jiddah amma basu taba haduwa ba, idanun su suke sarqe dana juna, yayi saurin dauke kansa da sauri yana kallon uwani, haushinta kamar ya shaqo wuyanta a gurin.

Banan kuwa tuni jikinta yayi sanyi, yau tayi ido da ido da el'mustapha, ashe haka yake, dole uwani xata kamu da ciwon xuciya dalilinsa, ba kowacce mace xatayi masa kallo daya ba batare da taji wani abu a xuciyarsa ba.

Uwani dauko wadannan haka sai ki cikamin sauran daga baya ina sauri,

Banan cigaba da gasawa bari na kai masa acikin gida,

Tana gaba dauke da masara yana bayanta, suna shiga harabar gidan ya kira wani dan sanda gefe,

Ka watse min wannan taron, duk abinda ke gaban gidan ka jefar dashi cikin bola duk ka watsar da komai bana son ganin ko tsinke a wajen ko naga an dawo dashi gidannan.

Suna shiga falon suka tarar da jiddah xaune tana yiwa twins lesson,

Kafin uwani tayi wani yunquri el'mustapha ya dauke ta da wani wawan Mari a kuncinta,

Shiru ya biyo baya falon har wace aka Mara saboda rudewa, twins kuma tuni sunyi bayan jiddah saboda tsoro abinda basu taba gani a gurin baban su ba,

Tsawon second talatin uwani ta dauka kafin ta dawo hayyacinta, sai a lokacin ta fashe da kuka ta dafe kuncinta tana qoqarin barin falon a rude bata ma sani ba,

Fincikota yayi ya dawo da ita tsakiyar falon ya jefar, qoqarin xare belt din sa yake, tana ganin haka ta rarrafo da sauri ta riqe qafafunsa, duk da haka el'mustapha bai fasa yi mata biyar masu kyau a bayanta ba,

Jiddah ta dauki twins ta fita dasu daga falon itama a tsorace take da el'mustapha, ita kam tunda take tare dashi bai taba sa hannu a jikinta da sunan duka ba abinda tangujewa uwani kenan tun farko.

Sanda ta dawo ne taji uwani na fadin,

'Dan Allah kayi haquri baxan koma ba, anty jiddah ce tace nayi wlhy itace tasa nayi,

Cak jiddah ta tsaya hade da dora hannunta a qirjinta, ta xare idanu tana kallon el'mustapha cikin girgixa kanta,

Ni? Wlhy qarya take min sai dana hanata taqi, uwani na kuka tayi caraf tace

Wlhy kece Ma kika bani kudin, ashe sharri ne kika min k..... El'mustapha ya bige mata baki, jiddah na ganin haka ta xura da gudu dakinta, rufewa tayi hade da sanya key cikin tsoron el'mustapha.

what a disgrace uwani, kamar ki, ki dora sana'ar masara a qofar gidana inama laifin a qofar gidanku ne tunda dama can kinyi kama da masu gashin masara.

'Dan Allah kayi haquri sharrin shaidan ne da aljannu, sune suka sani, ka tambayi anti jiddah tasan ina da aljannu kuma suna sani yin abu ban ma sani ba.

El'mustapha Where stories live. Discover now