El'mustapha part 1

18.7K 884 122
                                    


*EL-MUSTAPHA*

HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of Experts and Perfect Writers)

Fertymerh Xarah💞

sɪsᴛᴇʀ ʙʏ ʜᴇᴀʀᴛ ʜᴀᴜᴡᴀᴜ ᴀʜᴍᴇᴅ ʀᴜғᴀ'ɪ, ʏᴏᴜ ᴀʀᴇ ᴛʜᴇ ʙᴇsᴛ❤

1_5

Motoci ne keta sharara gudu tsakanin titin kaduna xuwa Abuja,
A qalla motocin xasu kai shidda koma fiye da hakan,

Dare ne mai tsananin sanyi, cikin watan nuwamba, haxo ya lullube duhun daren ta yadda ya fidda launi mai haske kamar hadadden hadari, wanda ya takura da yawan al'ummar birnin tarayya.

Daya daga cikin motocin A.I.G (Assistant inspector General of police) El_mustapha Maneer ne tare da Matar sa.

Kallon ta yake cikin alhini da son sanin asalin damuwar ta, ta yanda har ta takure kanta nesa dashi tana kallon hanya ta glass batare da ta damu da ta kwanta a jikinsa ba kamar ko yaushe idan suna cikin mota xasuyi tafiya.

Yayi tunani ya kasa gano laifinsa gurin uwargidan sa tun bayan barowar su kaduna bikin wani taro da akayi.

Tana sanye da suwaita ta rungume hannayenta duka biyu a qirjinta, alamar tana jin sanyi sosai amma hakan bai hanata takurewa guri daya ba saboda tana fushi dashi.

Murmushi yayi marar fitar da sauti bayan ya dauke dubansa daga gareta, Jiddah rigima, kome xatayi a rayuwa tana burgeshi, yana sonta sosai, so bana wasa ba, komai nashi xai iya salwantar wa saboda ita, yana yi mata son da alqalamin Pherty baxai iya rubutawa a takarda ba, saboda yaransa dake cikin motar suna tsaron lafiyar sa ya hana yaje gareta ya rarrashe ta tare dajin laifinsa har ake wannan fushin dashi.

Jiddah kuwa qara takure jikinta tayi, xuciyarta nayi mata wani xafi ganin halin ko in kula da mijin ta yayi da ita a yau, tasa yatsun ta biyu batare da tabari ya gani ba ta dauke wasu siraran hawaye da suka xubo a idanuwanta tana cigaba da kallon titi xuciyarta a daqushe tare da tunani iri iri duk a kansa.

Wata sassanyar ajiyar xuciya ta saki lokacin da taji saukar hannunsa cikin tafin hannunta, ta juya tana kallonsa ta cikin hasken farin wata da ya haske motar, bata ganinsa sosai ta dai san ba ita yake kallo ba hakan yabata damar janye hannunta a hankali hade da qara matsawa nesa da shi cikin tunxuro baki idanunta taf da hawaye.

Jikinsa ya qara sanyi, meke damun Jiddah, meyasa ta canxa masa haka lokaci daya?

11:30pm

Suka shigo garin abuja, dirar motocin su ya sanya Uwani miqewa da sauri ta gyara powder fuskarta hade da qara feshe jikinta da turare mai sanyin qamshi.

Ta mirror take kallon kanta tana qara jujjuya jikinta, ita kanta tasani ta ko ina tayi bata da makusa har take ji Ma tafi matar gidan komai amma meyasa El mustapha ke ganin Jiddah tafi mata dubu a duniya, meyasa yake ganin Jiddah ce tauraruwa acikin mata, meyasa ya kasa gane yanda xuciyarta ta mutu da qaunarsa, har take kishin yar'uwar ta duk saboda shi.

Ina son elmustapha da izinin Allah sai na aure shi, sai na sami matsayi a xuciyarsa fiye dana Jiddah.

Jiddah tana fitowa motar bata tsaya wata wata ba tayi shigewarta kai tsaye, a falo taci karo da uwani tana fitowa kallon mamaki ta bita dashi wanda ya sanya uwani daburcewa...

'Uwani duk wannan kwalliyar ta mecece, ina xakije da wannan daren haka?

'Anty Jiddah.. Uhm.. dama Yusuf ne yaxo to bai jima da tafiya ba, yanxu dama nake so na cire kayan na kwanta sai naji dawowar ku shiyasa Ma na fito.... ta fada cikin murmushi

Jiddah bata bi ta kan xancen ba ta soma tafiya tana fadin,
'Naji gidan shiru, ina Arham da Aryan ne.

'Sun jima da yin barci bayan sun gama rigimar nemanki,

El'mustapha Where stories live. Discover now