Tuno da wannan yasata soya doya da qwai daman tarigada ta dafata, itama kadan tai sai cheeps da tasoya shima kad'an.

Nan ta jera komi a dinning, tana gamawa ta d'ebe nata ta haura sama abunta, saida tashiga tiolet tai wanka sannan ta zauna cin abunta.

Ashraf kuwa koda ya sakko saida idanuwansa suka sauka kan dinning d'in murmushi kawai yai tare da nufar qofar fita.horn biyu yai bai kuma sakya yiba.

Dije kam tana zaune tana katyawa taji qarar harm hakan yasata ajjiye doyar ta miqe tare da sakkowa qasa.kaitsaye gate din ta nufa nan tashiga qoqarin bud'e mai, saidai fa tasha wuya dan gate d'in babbane ga nauyi.

Ashraf kam yana kallonta ta mudubi yadda take uban zufa da nishi, saidai ko d'ar baijiba saima wata dariyar mugunta dayai, saida yazo dab da ita sannan yabawa motar wuta, itakam yana fita ta maida qofar ta rufe tare da riqe kwankwasonta game da fad'in " wash! Allah kaban ikom juriya da wannan ibadar tawa kabani ikon samun nasara acikinta taqarasa da ameen"

Komawa tai saman sai tajima gaba d'aya abincin yafita daga ranta, hakan yasa ta tattara ta sakko qasa, dinning ta nufa nan ta bud'e flask d'in ganin ba'a ta'ba komiba yasata tattara kayan a fridge tasa doyar da cheaps d'in nan tasakya gyara kitchen din sannan ta dawo falon, kan dugowar kujera tahau tare da miqewa kanta nanfa bacci yai gaba da ita.








Imran ne zaune gaban mom nasu Ashraf bayan sun gaisane yake miqamata duk wasu takaddu na dije akan makarantar koyan girkin dazata fara zuwa.

Mom ta kalleshi tace" ni da nafara tunanin ko abarahima tunda yanzi hutun baifi sati biyu ba, kaga mai zata koya"

Imran yace" a'a mom kibarta kawai tafara zuwa, inyaso mai lesson din ba sai ace yadinga zuwa weekend ba, koya kika gani?"

Mom tace" ehh hakanma yayi, kokuma yadinga zuwa kwana hud'u ba zamuyi magana da ita da kuma mommyn ku"

Imran yace" shikkenan, yanzu ko gobe ma zata iya fara zuwa, ni zan kaita sai nabada amanarta duk da narigada na gama magana da ita mai koya matan"

Mom tace" bakomi Allah yakaimu, ai nace da son din yazo zamuyi magana dashi"

Nan dai suka tsaida magana akan goben zata fara zuwa sannan yamata sallama.

Koda tagayawa dad yayi farin ciki tunda abin ai naqaruwane koba komi hakan zai temaka mata wajen jan ra'ayin mijin nata, nan yamata fatan nasara"



Da dare Ashraf yazo wajen mom kamar yadda tace" dashi" bayan sungaisane take tambayarsa lafiyar diyar tata"

Duk da cewa baison yatakeba, amma sai yakada baki yace" tana lafiya, tacema nagaidake"

Mom ta fad'ad'a mirmushinta kan tace" ina amsawa, yawwa son dama maganace akan makarantar da nakeso tafara zuwa kuma tana da matuqar mahimmanci, dan haka gobe zata fara zuwa idan ka koma inaso ka bata waya zamuyi magana"

"Ok mom, amma nifa banda lokaci kuma kinsan driver......"

Bata bari taqarasaba takatseshi da fad'in " kaga daman bance kai zaka kaitaba Imran zaiyi komi, ka huta mai aikatau"

D'an sosa qeyarsa yai aransa cayake" ashe ita da magulmacin ne " afili kuwa cayai" sorry mom"

Batace mishi qalaba saima dad'a jaddadamai datai akan"daya koma yabata wayar zasuyi magana" nan sukai sallama.

Koda yabar wajen Mom ba gida yanufa ba, gidansu Imran yawuce, nanma saida yajima danma Imran d'in ya fatattakeshi, amma asan ransa baiso komawa yanzuba.

Sai wajen goma saura sannan ya d'au hanyar gidan.Dije na kwance bacci yayi gaba da ita sosai, dan yau kusan a falon tayini, jin qarar motarsa yasata miqewa da sauri, nanfa tafita, haka tashiga jan qaton gate d'in harta bud'e mai.

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now