biyayya.... 65-66

Start from the beginning
                                    

Dije ta miqe afusace tayo kan auta tace" ni sa'ar kice dazaki dingamin dariya" ganin hakan yasa auta artawa aguje tayi qasa.

Dije ganin hakan yasa tayin qwafa tare da fad'in " yarinya zan kamakine ai batsira kikaiba".

Toilet ta fad'a ta watsa ruwa kana tafito, wata dogowar riga tasa ta atamfa amma tamata kyau duk da bawani ado garetaba saidai tsiyar Dije wani d'ankwalin ta d'akko daban tad'ora akai, duk dacewa auta nayawan gayamata bata kyau intai wannan had'in gambizar amma ina ita batagani.

Saida ta qara hutawa sannan ta sakko qasa, auta ta tarar zaune afalo tana kallon wani series film a MBC2, matsawa tai daf da kan table d'in dake tsakiyar falon cikin sauri da azama tasa hannunta ta d'auke remote d'in.

Auta ganin hakan yasa ta miqewa tare da qarasawa wajen Dije tace" aunty plz dan Allah karki kashe" dan tafahimce mai dije zatai da remote d'in.

Dije tai wani qayataccen murmushi tace" ai wllh saina kashe badai ni kikewa dariyaba"

Auta ta tsugunna tare da kama kunnenta tace" plz aunty sorry" ta qarasa cikin marairaici fuska.

Dije tasaki wata dariya tace" yarinya ni zaki yiwa wayo"

Auta tace" a'a auntynmu ta yaya bada kanki asare kije gida kice ya fad'i"

Dije taja tsaki tace" yarinya kin qara wani laifinma ai, laifi biyi"

Kafin auta tai magana Mom da sakkowarta kenan tace" a'a lafiya meyafaru kuma daga dawowa?"

Auta tai caraf tace" mim kinga fa wai kallo nake shine saita kashe haka kawai"

Mom ta kalli Dije tace" d'iyata meyafaru?"

Dije ta gyara tsaiwa kan tace" yawwa mom kingafa rashin kunya tamin shine dan nace baza'akai tashar nanfa take min gwalo wai dole sai ankalla"

Mom ta riqe baki tare da kallon auta tace" rashin kunyar take har takai haka, matar yayan naki ki kekewa haka"

Auta ta marairaici fuska tace" wllh ba haka bane mom, nifa ba abinda namata Allah ma shaidane"

Mim tace" dalla ni rufen baki, maza ki 'bacen daga gani"

Auta ta miqe tare ta turo baki, har tayi taku d'aya Dije tace" mom qyaleta zoki zauna badan halinkiba yarinya"

Mom tai murmushi dan tanayiwa wannan yarinta tasu dariya sosai, sai suyi fad'a su shirya ka rantse sa'annine, dataiwa Dije maganama catai ai tafi jin dad'i akan tazauna ita kad'ai, kuma yadda ta fahimce Dijen ita d'in mai saiqin kaice dan san shiga jama'a ba ruwanta dakowa.

Nanfa auta tajuyo tare da murmusawa takoma tazauna.Mom ce tace" musu sunci abinci kuwa?"

Auta ta girgiza kai tace" a'a mom daman kwa cikina tun dazu yake kuka"

Mom tace" dalla can rufen baki, ke kam kinzama acici wllh"

Dariya dije tai tace" kamar kinsani mom, kuma yanzu fa naga taci biscuite har guda biyu"

Mom tace" ai zakiga abinda yafi hakama, wannan ai mijinta yashiga uku"

Hannece ta katsemusu hirar tasu da fad'in" Hajiya angama abincin"

" Yawwa Hanne sannu da qoqari, ajera a dinning" mom tafad'a cike da fara'a afuskarta.

Dije ce tabi bayan hannen tare da fad'in" bara na temaka miki ko"

Batajira amsartaba ta kwaso kayan abincin tayo waje, a dinning d'in ta jerasu kamar yadda akeyi.

Suna gama cin abincin Dije ta d'akko jakar makarantarta tare da zaro littafin english ta miqawa mom

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now