Ba musu Dije ta ansa tasa, ai kam tana kallon kanta a madubi tace" kai tar nake yanzu alqur'an"

Auta tace" yawwa ko kefa aunty, daga yanzu haka zaki dinga yi in ba   haka ba zan dai na shigowa nan 'ban garen kuma na ga yawa mom cewa wari da wari ki ke sawa, kin san mom ba zata ji dad'i ba dai"

Gir giza kai tayi tace" haba kar muyi haka dake autan mom, na dai na kinji" ta 'Kara sa ta na ri'ko hannun ta.

Auta tai dariya tace" yawwa aunty na ko kefa yanzu ki zo mu sau ka 'kasa Ana wani shiru a TV mai kyau na san kema za kiji dad'in kallon sa"

Nan dai suka sakko 'kasan sai da Dije taje haura d'akin mom ta gai da ta, sosai mom taji dad'in hakan nan take tambayar ta " komi dai lafiya ko"

Dije tai murmushi tace" lafiya lau mom ba komi komi qalau"

" to masha Allah haka akeso Allah ya yi muku albarka"

Da " ameen" Dije ta amsa mata, sannan ta sakko falon Dan suyi kallon.

Koda ta 'karaso auta tace ta kalleshi ta tace" oh 'yar gidan mom shine kika wani shige ki ka ma'kale ai gashi nan har an wuce wajen da na keson ma ki kalla"

Dije ta matso tar da CA kwu meta tace" haba dai wayyo Allah shikkenan na rasa"

Auta ta tun tsure da dariya kafin tace" wai aunty zaki karya ne, da wasa nake miki fa yanzu za'a fara film d'in"

"Au kice tsoka na ta ki keyi, shikkenan"

Nan dai suka hau kan kallon su, idan akai abinda za ai dariya sai dai kaji dariya na tashi daga falon.


Sai wajen uku suka tashi daga falon shima mom ce ta tsawa tar musu Dan ta lura tunda suka zauna basu tashi ba bare ma suyi sallah fad'a sosai ta musu akan hakan.

Koda suka idar da sallar ma zama sukai aka shiga sharhin film d'in da aka kalla, sai da Laure mai aiki ta le'ko ta sanar dasu kiran mom da ta ke musu sannan suka fita.

Tana zaune a falon suka ''karasa had'e da sallama. Gefan ta suka zauna tare da cewa" mom ga mu"

Mom ta kalleshi tace" ehh ai na gan ku, abinda kuka tsiro da shi kenan zama yin kallo da kuma surutun da bazai anfani ku da komiba har kuka manta da sallar dake ga ban ku, meye anfanin kallon ba bautar ubangiji? Da kallon da sallar wanne ne a gaba?, ko abinci ba ku ci ba kuna aikin Abu d'aya ko?"

Duk suka had'a baki wajen fad'in" sallar ce mom "

"Au da kun sani ma kuke zaune, to zan sa a d'auke kayan kallon sai naga ta tsiya"

Auta tai karaf tace" please mom kiyi ha'kuri, ba zamu kuma ba Dan Allah"

Mom ta kalli auta tace" yimin shiru daman ai ke kin fi kowa baki, shiga sa ma na 'kagu ki kuma school hankali na yafi kwanciya ba ruwa na da haya niya"

" kai mom au har kin gaji dani " auta ta fad'a tana zun'buro baki.

Mom tace " ai bakin baiyi tsini ba sakya zun 'buroshi sosai"

Ai kam me Dije zatai in ba dariya da ta shiga 'kya'kya tawa, ita kan ta mom d'in sai da tai, ganin hakan yasa auta mi'kewa tare da sakin magul macin kukan ta ta haura part d'inta.

Ganin hakan yasa Dije mi'ke wa itama tabi bayan ta, tana shiga d'akin ta han gota a kan gado ta koda kai tana kuka.

Dije ta 'karasa tana 'ko'kari d'ago ta tare da fad'in" kai Dan Allah auta ai sai kisa muji kunya daga magana sai kuka wasa fa mom take miki"

Auta ta d'ago a fusa cen ta tace" ba wani wasa bacin kema dariyar ki kemin waye ba zai yiba to"

Dije tace" shikkenan naji nayi laifi kiyi ha'kuri to bazan kuma ba kinji"

Gyad'a mata kai kawai tayi, nan kuma aka shiga wata sabuwar hirar.

Sai wajen biyar da rabi Dije ta tuna da duty d'inta cikin han zari ta mi'ke tare da cewa auta" bara naje na dawo ki zauna anan fa in kika biyoni ba 'ka rasa miki labarin ba zanje na d'an gyara d'aki na na manta ban tatta Tara kayan da na cire ba"

Tana gama fad'a r haka ta fice da sauri, ita kam auta 'kwafa tai kana tace" duk yadda akai akwai abinda kike 'kullawa aunty ko kike boyewa amma zan gano shi da kaina"

Tana gama fad'a ta janyo system d'inta ta kunna wani film tare da sa earpiece wai Dan kar mom ta jiyo ta dan ita in za tai kallo sai ta 'kure volume.



*******Zaune yake  cikin office d'insa yana duba wasu ta kardu da P.A d'insa ya bashi. turo 'kofar akai tare da yin " sallama"

Ba tare da ya d'ago kai ya kalli mai sallamar ba ya amsa masa.

Imran ya kalli Ashraf yace" wow kai gaskiya kayi wani fresh kai kaga yadda ka zama kuwa, amma Dije ta Iya kiwo wllh"

Ashraf ya d'ago daga aikin da yake tare da Jan tsaki kafin yace" wllh Imran ka fita idona, ban son iskan ci, daman can haka nake banza"

Imran ya 'kyal-'kyale da dariya yace" wllh 'karya kake, da da kake fingi-fingi kamar a hure ka fad'in 'kasa wan war za kace wani ba kai fresh ba ji wata 'kiba da ka fara shu kawa fa kai har da....."

Bai bari ya 'Kara sa ba ya jefe shi da biron dake hannunsa " kai dai wllh kayi a sara" ya fad'a yana mai ci gaba da aikin sa.

"Wace a sara kuma, ai gaskiya nake fad'a, ko ba haka bane, ina ga baka kallon kanka a madubi ne"

" dalla ya isheni haka" ya fad'a yana mai mi'kewa tare da har had'a takaddun waje d'aya, yana gama had'a su ya zari key d'in motarsu ya fice tare da fad'in" maye kaci kan ka da kan ka"

Dariya Imran ya shiga tun tsirawa shima ya fice daga office d'in .

A bakin mota ya tadda shi yana shirin shiga d'aga murya yai yace" d'an ji rani man ai yau gidan mom na nufa zanje na kwashi girkin amarya"

Ko kallon inda yake bai yiba ya tada motarsa tare da bata wuta.

Ganin hakan yasa Imran yin 'kwafa shima ya shige tasa motar yana fad'in" dad'in abin ma ina da ita, wai yau da nasha kashi da hannun ka"

Vote
Comment and
Share.....pls.

*Miss Gentle ta kuce.....*

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now