Dije ce ta kalleta tace.
" wai ku baku da aikin komi ne sau kwanciya, kwana biyu nan danai sai naga ko fita ba kwayi, mu kwa acan sai ka fita ka siyo abinda ranka ya keso, har tsokana ma mukeyi, nan kwa shiru ba dad'in zama"

Auta ta mi'ke zaune tace.
" cab, ai mu nan dad baya barin mu fita, kwllh inason irin rayuwar nan, kayi abinda ranka ya keso, inama dad ya barni na koma gidanku"

" cab, yanzu ke sai ki bar wannan 'katon gidan, ki tafi 'kauye?". Dije ta fad'a.

" hmmm sai dai mu in ba'a barni ba"

" lallai, ai kam zakiji dad'in can wllh"

Auta tace " aunty bani labarin 'kauyenku, da irin tsokanar da takeyi a can"

Nan fa su Dine aka mi'ke 'kada aka shiga baiwa auta labari kala-kala, cikwa har abinda tawa Ramai.

Auta kwa sai kwasar dariyarta ta keyi, kafin tace.
" aunty amma wllh kin Iya cin zaki, cab, amma wannan Raman taji wuya, to kin maida mata da kud'in?"

Dije tai murmushi tace " na bawa Jummai, ta maida mata, ban saniba ko ta kai oho"

" cab Allah sarki wannan mata" auta ta fad'a.

Sun dad'e suna hirarsu, kafin Dije ta mi'ke tace.
" uhmm bara natafi nima najr na kwanta, amma fa sai dai kizo ki rakani, kinsan ni ban Iya bud'e wannan abun ba"

Auta ta 'kyal'kyale da dariya tace " kai aunty, very soon zaki Iya, amma Allah ki daina cewa wannan abun"

Dije tace "ni bance ki zagenba, da yaranku, in zaki rakani to?"

Auta ta gwalo ido tace " kai aunty banda sharri,,nifa ban zage kiba, turanci nai, ba wani yarenba, kema zan dinga koya miki, kafin dad yasaki makaranta, muje na rakaki, nazo na kwanta, bacci nakeji"
Tana kaiwa 'karshe tai gaba, itama Dijen binta tai abaya.

Dai-dai 'kofar d'akin nata ta raka ta, batace mata 'kalaba ta juyawarta. Ita kam Dije sauke nun dashi tai tare da tura 'kofar a hankali.

Yana zaune yana operating d'in system, gabansa kofine dake d'auke da coffee a ciki, ta shigo, bai ko kalli inda take ba, Dan yasan ba zai wuce ita ba, itama ganin ko samun mutum ya shigo baiyiba yasata yin hanyar d'akin da auta ta nuna mata amatsayin nata.

" keee"
Bata juyoba, sai dai ta tsaya cak awajen.

" bada ke nakeba"
Ya fad'a fuskarsa atamke.

Juyo watai ta kalleshi taga hankalinsama akan abinda takeyi yake, murgud'a baki tai kana tace.
" ai naga ba haka su mama da baba suka fad'a ba, taya za'ai nasan dani kake"

D'ago kansa tai ya kalleta yace
" to ni na fad'a daga yau, Dan haka da zarar kinji ance " kee" to ke nake nufi, Dan bakina bazai Iya furta wannan  sunanba"

Tai 'kwafa tare da juyawa.

"Keep, ba canai kizo ba"
Ya fad'a ahasale.

Juyowa ta sakya yi, tace.
"Ni kuma kunnuwana basu da lokacine sauraran wani banzan shirme, naga baka da aiki agabankane, ni kuma inajin bacci, shiyasa"
Tana 'karasaba ta shige d'akin, tare da turo 'kofar.

Mamaki sosai ta bashi, tunda yake ba'a ta'ba yimai irin wad'annan abubuwanba, amma bakomi
" zanyi maganinki yarinyar" ya fad'a.
Ci gaba da aikin NASA yayi, sai da ya gama komi, sannan ya sauka 'kasa, Dan daya shigo mom bata nan, take anguwa, kuma basu gaisaba.
A d'akinta ya sameta tana jera kaya a wadrop " mom sannu da aiki?"

"Yawwa my son, ya gida, ya 'yar tawa, since dai ko lafiya lau ko?"

" kai mom, bakomi fa, duk muna lafiya, har kin dawo?"

" ehh, daman na d'anyi siyayyane" ta bashi amsa ata'kaice.

" OK, barin he gidansu Imran" ya fad'a.

" ah my son, ya kamata ka zauna kai da matarka, ku tattauna, in akwai abinda bata ganeba ka mata bayanin, kasan kan gidan namu dai ko?"

Ba asan ransaba yace.
" OK"

Yana fad'a ya mi'ke tare da ficewa daga d'akin. Sashensa ya koma, kan bed ya hau ya kwanta, ba tare da yabi ta kanta ba.nan bacci yai awan gaba dashi.


Bashi ya farkaba sai wajen magrib, toilet ya fad'a ya watsa ruwa tare da yin alwala, kana ya fita masjid.

Koda ya dawo, zaune ya taddata a falon nashi, tana kallon wani Indian film, mamaki tabashi " wato har tayi za'kewar da zata kunna kallo"

Gaban TV d'in ya 'karasaba tare da kashewa, ganin haka yasa Dije kallonshi tace.
" haba malam ya da 'yar haka, yanzu aka wucenifa, kuma gashi ba'a dawowa baya.?"

Tsaki yaja, kafin yace.
" kallo aka kawoki, meyasa baki taho danaki kayan kallon ba daga gida, wannan nawane, Dan haka kar ki sakya samin 'kazamin hannunki akai"

" amma ai d'aki nane ko, tunda nima anan nake zaune"

Matsowa yai dab da ita yace " ba'a Gina d'akin da kud'in ki ba, Dan haka nawane ba naki ba"

" naji, amma ai inada 'yanci na kalla nima dai ko"

" au hakanefa, abinda ba'a sababa, anzo anga kayan alatu, to dai kar adinga d'aukar Ana siyarwa"

" Allah ya kiyaye, ai wllh ni ba 'barauniya ce ba, sai dai in Kai"

"Keee, ki shiga taitayinki, ni ba sa'an wasanki bane, kinji ko, maza 'bacemin daga gani"
Ya fad'a cike da tsawa da hargowa.

Cijin sauri ta bar wajen, tana kaiwa 'kofar d'akin ta tace.
"sai dai mushiga taitayin mu gaba d'aya, ni da kai, kuma kallo dai bazan fasaba wllh" ta 'karasaba tana mai murgud'a baki.

'Kwafa yai tare da fad'in.
" zan kama kine, saina babballaki yarinya."

Vote
Comment and
Share......

*Miss Gentle ta kuce.....*

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now