tace " a'a".

Kawu ne yace " in an kwana biyu za suzo har da Iya"

Da 'kayar aka 'ban'bareta daga jikin Iya, ita Allahn katafar bazata rabu da iyaba, sai da kawu ya daka mata tsawa, sannan tashiga taitayinta.

A mota ma, kuka kawai takeyi, Jummai da Imran ne suke ta rarrashinta, amma kamar Ana 'karawa wuta fetur. A haka har suka kusa isa.

Awa d'aya ne ya kaisu gida, Dan a hankali yake tafiya, 'bangaren Ashraf aka kaita, Wanda dama mom tasa an dad'a gyarashi. " ( Dije yau dai gaki a gidan Ashraf)"

Mom ce da kanta ta shiga ta musu maraba, nan ta gabatar musu da abinci da abin sha, sosai Jummai taji dad'in tar'bar da mom ta musu. Ganin irin kukan da dije ke yine yasa mom 'kin tafiya, har saida ta dinga bata baki, da 'kyar tai shiru.

" lallai ba shakka Dije ta shigo hannu na gari" Jummai  ta fad'a a ranta.

'D'aki guda aka warewa Jummai Dan kwana, Dan mom tace " bazata koma ba sai tayi kwana biyu, Imran ya mai data"

jin hakan yasa Dije dagewa akan abarsu su kwana tare, haka mom ta ha'kura ta barsu.

Shikam Ashraf koda mom ta gayamai abinda ke faruwa, dad'i yaji, Dan dama shi bai shirya ganin wannan wawuyar yarin yarba.


******

......washe gari kam, da sassafe mom ta tura auta tace " take ta taho dasu ayi breakfast.

Har 'kasa su Dije suka gaida su mom, Wanda harda dad, da oga Ashraf. Ciki da farin ciki suka amsa.


Bayan sun kammalane dad ya fad'a yu musu nasiha, kallonta Ashraf yai yace " zan fara da kai, Dan Kaine babba, inaso kaji tsoron Allah ka ri'ke marainiyar Allah hannu bibbiyu, ka ri'ke ta tsakani da Allah, ba cuta ba cutarwa, nasani bawai Santa kakeba, kuma itama haka, wannan auren duk ba san juna kukeba, amma kar hakan ya baka damar da cutar da vaiwar Allah, kuma idan kukai  ha'kuri za kuci eiba mai yawa, ga amana nan na baka, banyarda ka wula'kan ta ta'ba, idan kai hakan kamar ni kaiwa"

Ya juya ya dube Dije yace " Khadija, kiyi ha'kuri da halin da zaki tsinci kanki, ita daman rayuwar aure haka take, zakiga 'kalubale da yawa acikinta, Wanda sai anyi ha'kuri dasu, kiyiwa Mijinki biyayya, banda rainasa, banda bayyana sirrinsa ku , kinji"

Gyad'a kai kawai tayi, ba tare da tace komiba. Amma aranta fad'in take " wllh yamin ba dai-dai ba, saina rama, sai ai ta cewa inyi ha'kuri, inyi ha'kuri" 

*Ni kam nace " oh su Dije ba yafiya kenan"*

Nan dai mom ma ta fad'a yi musu tata nasihar, daga visa ta umarci Ashraf data nuna musu kan gidan, ba 'karamin haushi yaji ba, amma ya dake.

Duk inda suka shiga baya jiran sun gani ko basu ganiba yake wucewarsa, gashi wani gurin elavotar ce, sukuma ba Iyawa sukeba, sunaji suna gani suke binsa da gudu- gudu kamar jela. A haka har aka gama za gaya gidan.

'D'aki suka koma, Jummai ta kalli Dije tace " alqur'an gidan nan da girma yake sai kace ba aduniyar yakyaba, wai cab"

Dije taja nunfashin tace " Anya su kawu ba sai damu sukai ba Jummai, kalli fa kigani, irin wannan 'katon guri haka"

Jummai ta tuntsire da dariya tace " kema dai wllh, taya zasu sai damu, alhalin suna sanmu, kuna mutumin nan abokin baba ne, taya hakan zata faru, kin san ance su ' yan birni da manyan gida suke, kin tuna gidan mai unguwa ma, duk da dai bai kai wannan ba, ko a had'uwa"

Dije tace " hmmm Allah na taoratafa, koda na ga girman gidan, amma ina tausayawa mutan gidan nan"

Jummai tace " akan me"

Dije ta sauke nun gashi tace " akan sharaman, alqur'an suna yabawa aya za'kinta"

Jummai tace " ai sun sami 'Kari, ba gakiba kin dad'u"

" Allah ya kiyaye, wllh ko d'akin nan albarka bazan iyaba" ta fad'a cike da zaro ido waje.

" dalla nima da wasa nake miki, ai su 'yan birni suna da masu aiki" Jummai ta fad'a.

" hakane fa" Dije ta fad'a, nan dai suka ci gaba da hirarsu.


******
Kwanan Jummai biyu a gidan sannan ta tafi, koda zata tafi har da 'kwallarta, itama Dije haka, da 'kyar sukai sallama kamar kar su rabu. Mom kwam kaya ta loda mata masu yawa, tace " tayi tsaraba dasu"  sosai sukai farin ciki da kulawar da mom ke basu kamar 'ya'yanta,

"wannan mata akwai karamci" Jummai ta fad'a a azuciyarta.

Imran ne da kansa ya maida ta gida, ko samun sallama da Ashraf batai ba, Dan ba kiran da mom ba tai maiba amma wayar sa akashi, shikam baya sann ko shiga gidan ne, har yakaishi ga had'uwa da dije, shiyasa da Imran ya matsamai suje su kaita ya'ki, ya kuma 'ki zuwa suyi sallama, sai kud'i ya bada a bata.

Duk wannan kwana biyu  da dije tai agidan batasa Ashraf a idontaba, in ka cire ran da dad ya musu fad'a, duk da itama acewarta " bata damu da taganshin ba, in Dan itace ma, yai ta zamansa kada ya kuma shigowa gidan"

Bayan tafiyar Jummai, auta ce ta shigo,  gefan gadon d'akin ta samu ta zauna, kallon Dije tai tace ".

Vote
Comment and
  Share......

*Miss Gentle ta kuce....*

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now