Dai-dai 'kofar gidansu yayi parking...yaro suka samu suka aika gidan Dan neman iso. Koda suka shiga wajen Iya suka sauka, daman nanne wajen da sukavsaba sauka duk da wannan ne zuwansu na biyu...amma ko dad d'in shine yazo nan yake sauka. Sa'kon da mom ta bada akawo ya bata.

Sosai tayi murna, nan ta sa yaro ya kaisu gidan su Jummai Dan su Dijen na can, anan suka tare, Dan inna ta hanata zuwa ko ina, tace su zauna a gidan su.

Sungaisa da inna sannan a ka basu d'aki Dan su ke bance. Tsawon mintuna ba Wanda yace 'kala a cikinsu, ganin hakan yasata mi'kewa da nufin fita, har take bakin 'kofa ta juyo sautin muryarsa na fad'in " ke". Ko juyowa batai ba, amma ta tsaya,

" Waya baki izinin fita, ko ance na gama magana da kene?" Ya fad'a fuskar nan a had'e.

Kallonshi tai taga ma latsa-latsansa yake a Waya, kamar bashi yai maganar ba," lallai ma wannan mutumin " ta fad' a a zuciya, a zahira kuwa cuni baki tai tace " ai naga baka da abin fad'a ne, shiyasa, ni kuma inada ayyukan yi a gabana"

Da ido ya bita da wani irin kallo kafin yace " OK, kin ga makwancina ne ko yaya?"

Murmushi tai tace " ni duk ban gane wannan yaranba, kamin wandabzan fahimta"

" OK" ya fad'a yana mai dusuwa wajenta, ganin hakan yasata fara Ja da baya tare da runtse idanunta, Dan atunaninta ko dukanta zai, sai dai abinda ta zata ba hakn bane, domin jin nunfashin sa tai dai-dai hancinta tana sha'ka, bud'e idan ta tai, ganinshi kamar ya shige jikinta yasata gwalo ido tare da fad'in " malam meye haka kuma?"

Jan iska yai tare da fuzgar da ita yace " zan mikibyaren da zaji ganene" ya 'arasa fad'a tare da d'ago ha'barta.

Ture hannunsa tai tace " malam ka saurara, Dan ni ba irin ka bace "

" zaji Iya gayan ni d'in waye to?"

" d'an iska man" ta fad'a azuciyarta, amma a fili sai tace " nima ban sani ba, sabida yau na fara ganin ka ai, kaga banyi zaman da zan tantance ko kaid'in waye ba" ta 'Kara sa tana murgud'a baki.

Mamaki ma ta bashi, " wai yau ta fara Ganin sa" , lallaima yarinyar nan ' yar raining wayo ce.

Kallonshi ta yai yace " good, amma ki sani wannan auren da zasuyi za kiyi auren zaman u'kubane, domin ba zaki ta'ba jin fad'in saba, sannan kisani ni *MUHAMMAD ASHRAF* ba zan ta'ba sonki ba amatsayin matata, ba kuma zan ta'ba zama da keba amatsayin hakan,Dan haka tun wuri ki shirya zaman 'kunci da da nasamun aurena, samawa kanki lafiya shine kice a fasa auren bakki sona"

Cike da takaici ta kalleshi tace " nima d'in ai basanka nake ba, kasani zanyi wannan auren ne Dan farain cijin iyayena, zanyi *BIYAYYA* a garesu sa'banin kai da kaka sa, inason farin cijin mahaifana, kai ma kana da man kon zuwa kace bakka so, ba sai najeba, kasani bazan ta'ba zaman u'kubane ba, domin ban taso da ita ba, sai dai mu zauna da ita tare ni da kai". Tana gama fad'ar haka ta dur'kusa ta fice daga d'akin.

Cike da mamaki ya bita da kallo, lallai ma yarinyar nan, 'kwafa kawai yayi shima ya fice daga d'akin, Imran ya tadda inda sukai parking d'in motarsu tsaye shida Jummai suna hira har da dariya, wani malolan ba'kin cikine ya zuyar ceshi, daman indai har jar araina mutaneni to Imran ke janyo ta.

Yana 'Kara sawa ya bud'e murfin motar ya shiga ciki, dai-dai lokacine Dije ta 'karaso, tana fad'in " au daman kuna nan inata nemanku?"

Imran yai murmushi yace " muna nan, tun d'azu muke jiranku, amma shiru, Ana can Ana d'ibar fure ko"

Dije tace " kai yaya na, ba wani fure, ai line ma dai kukai kama da masu d'ibar fure, kiwa yaga tsayuwarku yasan da wadata a'kasa"

" kai 'kan wata, banda sharrifa" ya fad'a yana darya.

"Allah da gaske nake" itama ta fad'a.

Jummai ce tace " ke dama aikin saba da sharrinki na tsiya "

" to 'karya nai ne, aku kuturu" Dije ta fad'a.

Jummai tace " to to yau kika fara 'karyar"

Har Dije ta bud'a baki zatai magana suka ji ance " dallah ku matsamin anan, shasahasahn kawai"

Gaba d'ayansu suka kalli wajen da maganar ta fito, ta'be baki Dije tayi tace " in mutum bai son ji ya bar wajen mana" ta 'karasaba tana murgud'a baki.

Habawa mai Imran zaiyi in ba dariya ba, kafin yace " kai 'kanwata kar bakin ya cire fa?"

Dariya tai tace " ai ni nama yi fushi dakai, tun da ka tafi baka sakya zuwa ba"

" afuwan , tuba nake kinji" ya fad'a yana had'a hannayensa waje guda.

Shiko Ashraf ganin sun maidashi kamar wani dutse yasa ya koma motar tare da Jan morfin motar da 'karfi. Dije tai murmushi tace " kanka akeji"

Imran ganin ran Ashraf ya 'baci yasa shi yanke maganar da yakeson yi mata, Dan yasan kad'an da aikin shi ya tafi ya barshi anan wajen. Kud'i ya fito dasu tare da mom'kawa Jummai yace " kiyi ha'kuri da wannan ba yawa, ayi hidimar bikin"

Jummai ta kalli kud'in tace " a'a yayan mu, basai kun bada komiba, an rigada an gama komi ma"

"na sani, amma Dan Allah ku amsa"

" shikkenan , an gode, Allah ya 'Kara bud'e"

"Ameen" ya amsa, sannan sukai sallama.

Comment and

Share....

*Miss Gentle ta kuce.....*

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now