Page Sixty Nine

1.1K 103 79
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

*Zeeneert* @ wattpad

*BARKA DA JUMA'A CM FAM* 😍

*Page Sixty Nine*

Misalin karfe biyun rana bayan an idar da sallar Juma'a aka daura Auren IMAN IBRAHIM AHMAD da UMAR MUHAMMAD TUMFURE sekuma na MARYAM ALIYU TUMBIDO da UMAR MUHAMMAD TUMBIDO kowanne a bisa sadaki daidai gwargwado dukda kuwa both families are rich sabida albarkar Auren ake nema.

Kankuma kace me yar karamar hayaniya ta tashi a tsakanin mahalarta daurin Auren tunma kafin agama shi anata maganganu kasa kasa....

Shikuwa kuwa Ogan baima gane badashi aka daura aure da IMAN ba seda yaji an ambaci sunan Mami attached to his! Alokacinne previous daurin Auren da akayi yafara revibrating akansa!yagane sunansa da na mahaifin wanda aka aurawa Iman dinne iri daya anma last name ba dayaba!toh wai meyake faruwa ne? Dasauri yadago yakalli sashin da iyayenshi suke looking so confused and stunned and at thesame time yana neman karin bayani,addu'a yake aransa in mafarki yakeyi toh kada Allah yasa yafarka but that serene smile da Abba da Daddy suka bashi,kamo hannunshi da Sageeru yayi yana girgizawa excitedly ayayinda yake fadin

"Congratulations Man! You got Mami for the 2nd time!"

Yasa yayarda dagaskene ba mafarki yake yiba kamar kullum! Burin daya jima yanayine yake kuma gani abune mai yuwuwar faruwa yau yacika akuma lokacin daya gama cire rai da samunsa!

Besan lokacin da ya gurfana kasa yayi sujudush shukur ba ayayinda kukan farin ciki ta kufcemai. It was a moment of bliss dashi kanshi bazai iya fassara farin cikin daya tsinci kanshi acikiba! He don't know how everything turned out this way and he isn't even curios! All that mattered to him is at last yasake mallakar Mami bashi kuma da wani hanyar dazai nuna farin cikinsa da mika godiyar sa ga ubangiji daya wuce wannan! Ko a aurensu na fari be tsinci kanshi a irin farin ciki dayake ciki yanzu ba! Kodan wancan din yazo da kalubalene? Kodan yanzun yanada tabbacin Mami na sonshi and she'll be happy about the wedding too?For sure this's a moment he'll forever cherish and be grateful for! Haka yacigaba da kukan goshinshi akasa batareda ya damu da dubbanin mutanen dake gurin ba,yanda aka tsaya ana kallon shi,the flashes of camera swooning all over ayayinda yan jarida,yan uwa da abokan arziki ke kokarin capturing moment din dukda kuwa dayawa a wadanda suka halarci dauren auren are curios as to how daurin Auren yakoma biyu?miyasa ba'a daura Auren Iman da Muzammil ba instead kowa aka daura masa da wani daban bayan kowa ba abunda yagani a invitation dinda akabashiba kenan but seeing how happy Muzammil is at the moment ensures that whatever the reason for the changes might be is for the better! Wasu kuwa duk a tunanin su duka mata biyun aka aurawa Muzammil lokaci guda kasancewar sunansa dana Abba daya kusan iri daya karshen ne kawai ya banbanta!

Daddy ne ganin celebration din Muzammil din bana kare bane yasa Sageeru da Captain Abbas su daga shi ayayinda suka kulda cikin Jama'a suka fice a masallacin anatayi masa murna da Allah yasanya alheri.

Kankace me labarin fasa Auren Iman da Muzammil dakuma daurawa da akayi da other parties ya baza ko ina,yan jarida,masu aiki a gidan radio da social media bloggers ansa mu abun yadawa. Acan Yola labarin be isa garesu da wuri ba anacan anata kacaniyar biki. Fa'iza ce tafara gani. Ta kunna data zatayi posting pictures dinda suka yiyyi yanzu bayan angama yi musu kwalliya tayi arba da hoton Muzammil da aka dauka alokacin dayake sujudush shukur a wani page with a caption

"Jama'a kunada labari kuwa? Ashe ba'a daura Auren Iman yar gida Army chief da Commander Umar Tumbido ba? Instead aka aura masa Cousin dinsa Maryam Aliyu Tumbido wannan shahararriyar chef dinda tayi fice itakuma Iman din aka hadata da tsohon saurayinta?

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now