Page Thirty Five

973 69 28
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad

*Page Thirty Five*

Ko kadan tsallakeshi da Mamin tayi bai batamai rai ba ai inda sabo yakamata ace yasaba tunda batun yau tafara showcasing wadannan halayen nata na rashin nuna kulawa agaresa ba,tun kafin sutafi Sweden tafara hakanan ko bayan dasuka tafin ba abunda yacanza from the way he wanted them to be Communicating amma taki bashi hadin kai sam,so what she did today is much expected daman. Abu dayane yabata mai rai kuma bakomai bane face daga call din Sadiq datayi agabanshi tana wannan serene murmushi da dariyartata,kalar murmushi da dariyarda yake tunanin duk duniya bawanda takema irinsa seshi kadai.

It's that one kind of laugh and smile saying so much about the bond they share(Murmushi da dariyace dake bayyana abubuwa dadama akan wanda akeyima ita; How special that person is to the smiler,So much impact that person has on the smiler dakuma farin cikin dake wanzuwa arayuwar smilern all because of that one person. Atakaicedai murmushi da dariyace da kallo daya za'ayima wanda akeyima ita agane cewa suna sharing wani irin special bond da alkalami bazai iya rubutawa)

Muzammil wani irin kishi yaji ya dabaibayeshi lokaci guda,dukwani farin ciki dayatashi dashi ayau din seya nemeshi ya rasa,yaji dokin ganinta dayakeyi din ma yadaina. Wai daman bayanshi akwai wanda Mami zata taba farin cikin ganin kiransa awaya kawai irin haka? Gaba daya seya rasa me yake mishi dadi!

Yaji kamar yabi bayan Mamin yakwace wayar yaciwa Sadiq mutunci yakumayi watsa watsa da wayar yanda bazasu sake samun damar yin communciating ba amma yasan this is not the right way and time,moreover people are watching gakuma su Abba dake gefe dabayason sugane halin daya shiga donhaka seyayi kokari yayi getting glimpse of himself dukda kuwa fara'arsa yaki komawa irin nada

Yaceda Ammi da Al'amin suje waje motoci nacan ayayinda ya karasa kusadasu Abba yafada musu the same thing. Shiyayi musu jagora ayayinda Sojojin dasuke basu tsaro suka Mara musu baya gabadaya harsuka isa Inda motocin suke. Motoci hudune a parke,biyun hilux din sojojin ne ayayinda biyun tsakiyan kuma hadaddun motoci ne na zamani. Musamman Muzammil yasa suka taho da extra mota daya apart from wanda yake tafiya gurin aikinsa dashi sanin cewa nashin ba lallai ya dauki dukansu suzauna comfortably ba. Dakanshi ya karasa gaban motar dayake hawan yabude ma Mummy da Abba gidan baya suka shiga ayayinda yace da su Ammi suje sushiga daya Motar.

Mami daketa hira da Sadiq awajen airport din hankali kwance tun sanda suka fito tayi mai sallama tace zasuyi communicating daga baya ayayinda taje tajona su. Seda suka shiga motocin bakidaya harda sojojin dazasuyi musu rakiyar sannan Muzammil yasakai ta Windown da Abba kezaune yashiga yimasa bayanin batare zasu komai Damaturun ba shisai Sunday yakwana biyu baishigo Maidugurin ba so he has a lot of pending work dayakamata ya kuladasu.

Abba yace "Ba komai Son. Allah yakaimu Sunday din amma wadannan mutanen naka dasuka
samu a tsakiya fah?" Abba yayi maganar ayayinda yake nuna hilux biyu dasuka sa motocin dasuke ciki a tsakiya,daya agaba daya abaya.

Muzammil yashafa suman kansa yana murmushin yake dankuwa har lokacin his mood is off kawai daurewa yakeyi dankar su fahimci halinda yake ciki yace "Raka ku zasuyi Abba" Aise Abba yahau banbami yace "Suraka mu sukaimu ina? Cemaka akayi dan kwalliya akahadaka dasu dazakace subarka anan susurakamu? For goodness sake they're to always be by your side for your protection sabida haka kadebi mutanenka kuyi tafiyarku muzamu karasa gida yanda mukazo. Motoci da Drivers dinda kabamu ma sun isa Allah yayi albarka" Muzammil disagreeing with Abba yace "Kuma kuna bukatan tsaron Abba,infact more than me tunda hanya zaku hau sannan anganmu tare anan which clearly means you people might be in danger too" Abba yabudi baki zaiyi magana Muzammil yatari numfashinsa cikin sigar roko yace "Please Abba,I insist. Kamanta acikin gari nikadai nake yawo abuna a Damaturu? toh anan din ma mostly hakanne barekuma yanzuma bawai nikadai zaku bari ba" yanuna two Soldiers dinda ke tsaye a bayansa su basushiga motocin ba cikin son sake kwantar da hankalin Abba yace "Wadannan biyun ma sun isheni and the Car I requested from the Barracks will be here any moment from now so there's really nothing to be worried about" Abba ganin Muzammil yadage seyace "Toh aishikenan tunda kadage. Allah yasa hakan shiyafi alkhairi" Muzammil yayi murmushi achievingly yace "Amin ya rabbi" sannan yadubi Mummy yace "Safe journey Mummy" Mummy na murmushi tace "Thank you Son" sannan yajada baya yashiga dagama Drivern hilux dinda ke gaba hannu kan yafara tafiya.

CAPTAIN MUZAMMILDonde viven las historias. Descúbrelo ahora