Page Forty Two

362 53 4
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

Zeeneert@wattpad

*Page Forty Two*

Aunty Khadija tayi dariya tace "Aini yaban mamaki" daganan kuma setahau yima Mami fadan miyasa bata fadama Muzammil din akwai bako dazaizo ba kawai tashirya zata je tadauko shi. Tace irin kananun abunnan suke jawo misunderstanding dakuma zargi yashiga tsakani sabida haka tayi kokari tagyara next time.

Kiran layin Muzammil Mummy tayi akashe. Seta mika ma Mamin wayar tace takira Sadiq din taji suna ina.

Karba Mami tayi tayi searching number Sadiq din takira,ringing din farko yayi picking bakin shi daukeda sallama. Amsawa Mami tayi inda yayi picking voice dinta yace 

"Mi Ladi." Mami batasan sanda tasauke nannauyar ajiyar zuciyaba jin voice dinshi Normal,tace "Na'am Sadiq" Sadiq yace "look at her wai Sadiq....keda yakamata kice Na'am Mi Man?" Sadiq yayi maganar yana ambatar "Mi Man" din imitating her voice dasaida yasa Mami dariya tace  "kaifa bakada dama" sannan curiosly takarada "yanzun kana inane?" cikin barkwanci Sadiq yace "Still at the park waiting for Mi Lady" and Mami didn't take him seriously dan jin yanda mood dinshi is normal seta dauka Muzammil din yaje yadaukeshi ne.

Tace "Nifa banason wasannan tell me where are you I'm here all worried baku iso gidaba" Sadiq shiru yayi nadan wasu dakiku yana nazari kafin can curiosly yace "kin turo azo adauke ni ne?" Mamin find the question weird because he sounds serious anma sedai batason bashi amsa yazamanto abunda take zargine,bataso yasake having impression cewa familynta baswasonshi to the extent dahar zasu barshi atasha yajima haka

Seta wayance dacewa "Amsar tambayata kenan?" Sadiq yace "okay what do you want to know?" Mami tace "so nake insan a ina kake" Sadiq yace "I'm at the park" Mami tace "Okay toh ganinan zuwa kakara hakuri kaji koh?" murmushin yake Sadiq yasaki yace "karki damu take your time. You know i can wait for you even if it'll take you decades b4 you come" and Mami couldn't help but blush.

kashe wayar tayi tana kallon Mummy tace "Har yanzu yana tasha babu wanda yaje daukanshi"

Maman Khady tace "Uhummm aini nasan za'a iya rinawa. Yanzu seki tashi kije kidauko shi dawuri dukda ma daga yanda naji kuna magana bana tunanin yanada saurin daukan zafi irin Alhaji Ooo(Muzammil take nufi)" Mummy her face expressionless tace "Don't drive alone. Kice Mallam Shu'aibu yakaiki" Mami tace "Toh" sannan tayi sauri tafice a parlourn dayake already veil din abayan data saka yana kanta.

A harabar gidan tasamu Mallam Shu'aibu inda tace yakaita tasha. Cikin mintuna kalilan suka isa park din,inda ake lodin masu tafiya Maiduguri Mami tace Mallam Shu'aibu yakaita.

Suna isa tahango Sadiq zaune kan wani bench akarkashin bishiyan dake kusa da inda ake parking motar dake lodi ayayinda yadan jingina jikinshi da bishiyar yalankwasar dakanshi gefe guda deep in his thoughts. Yanda yayin kamar wani maraya ko almajirin dayayi bara besamu tuwo ba hakanan kallo daya zaka mishi kagane cewa he's so tired and at thesame time somewhat disturbed.

Mami batasan sanda hawaye yacika idanuntaba. Wani irin tausayinshi ne taji yakamata lokaci guda. So he's just been pretending and acting strong sabida kartaji wani iri bawai don yaji dadin abunda yafaru baneba and it seems her effort wurin hanashi tunanin datake zargin zai iyayi din has gone in vein because by just the look on his face tasan meyake going in between his chest. Jiki sanyaye tabude motar tafito ayayinda tanufi inda yake.

Seda ta tsaya akanshi yaji kamshin perfume dinta sannan ya ankara da'ita,Mami takawar dakai gefe ta share hawayen ta dake kokarin zubowa tanajan numfashi sannan tadawo da dubanta gareshi tayi folding hannu akirji trying to act normal tace "Tunanin mekakeyi haka haji Sadiquuu?" Murmushin yake Sadiq yasaki yace "Tunanin Maryama" asanyaye Mami tace "Dakuma yanda tashanya ka kanata jiranta koh.....?" Sekuma ta rausayar da kai gefe tace
"I'm sorry i know i kept you waiting for long but believe me it wasnt intentional"

CAPTAIN MUZAMMILDonde viven las historias. Descúbrelo ahora