Page Fifty Three

404 60 27
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

Zeeneert@wattpad

*Page Fifty Three*

Wayarsa yajanyo yashiga kiran layin Muzammil din bawai don ya tsira da ransa kawaiba sedan sanin cewa if daga shi har Muzammil in suka cigaba da acting adamant then basu kadai bama,mutanen nan family dinsu ma bazasu bari ba amma sedai Muzammil din beyi picking ba. Haka yacigaba da kira ba kakkautawa waiko in the end Muzammil din zai daga danshi jikinshi yana bashi bawai baya kusada wayar baneba picking ne bayason yi sabida kilan yyi suspecting dalilin kiran nasa.

Aikuwa hakan ne,Muzammil na kwance a daki gabadaya hankalinsa atashe yake gameda abubuwan dasuka faru yaudin gakuma jimamin decision dinda za a iya yankewa akanshi goben tunda bawai yanada tabbacin parents din Khadijan zasu fadi gaskiya baneba,dangwanda Sagiru ma kiran Chief of Armyn yashigo,kin picking yayi dagangan dan jikinshi yana bashi Chief of Armyn yasamu labarin abubuwan dasuke faruwa ne and it could highly be party chairman dinnne suka sanardashi in form of threatening him shine yakira yabi order dinsu and shikuma tunda yasakai baya tunanin akwai wanda zai iya stopping dinsa ayanzu inva wani ikon Allahn,haka yana gani call din Chief of Armyn yadinga shigowa anma yaki picking. Shi ba abun ya kashe masa wayaba yagane cewa dagangan ne yakekin dagawa..........,

The following day after 11am kadan Alhaji Abdullah da Sagiruuu suka iso gidan,Allah yataimakesu sun samu jirgin dayazo Maiduguri  a safiyar yau. A parlour iyayen suka hallara gabadaya sekuma Muzammil,Mami,Khadija da Sagiruuuu. Daddy yasanarda shi halin da ake ciki sannan yaceda yaran kowa yamaimaita abunda yafada jiyan and they did,Khadija cedai kadai tunda tafara magana taketa muzurai da in ina gakuma shan kwana,wasu daga cikin maganganun data fada a jiyan ma dukyau tayi musu rufi,kana ganinta kaga marar gaskiya duk a tsorace take tareda tararradin abunda zaifito daga bakin mahaifinta dan tsaf jiyan Hajiya Naja'atu takirata tasanar daita yanda sukayi.

Alhaji Abdullah dai kunya,bakin ciki da takaicin Khadijar kamar yayi yaya hakanan besan sanda yayi kanta yana fadin "Zakiyi shiruuu kibar shirga karyar nanne kosainayi miki lahani!!!!!" Khadija aibatasan sanda tayi tsalle tafara neman hanyar guduwa ba hankali tashe ayayinda tasaki kuka tana bawa mahaifin nata hakuri,tasan halinshi sarai yanzu seyayi mata dukan kawo wuka amma dukda haka bedena bintaba,can sega Sagiruuu ma yatashi yana kokarin tayashi. Dagudu Khadija taje ta boye bayan Mummy tana ihu tareda rokonta tatayata bama su Sagiruuu hakuri dama sauran yan parlourn

Dakyar Daddy da Abba suka riko Alhaji Abdullah suna bashi hakuri

Alhaji Abdullah da idanunsa suka canza launi sukayi jazir tsabar bacin rai yace "Dan Allah kubarni in daki banza kona huce takaicin kunyata ni da bakin ciki da take kunsamin akoda yaushe. Tasan munsan komai anma still agabanmu kara shirga karyar takeyi? What does she mean? Tadauko ni irin uwarta ne dazan boye laifinta in lakawa wani?" Sekuma yasake harzuka zeyi kanta....

Daddy ne yayi saurin kamo shi wannan karan yana bashi hakuri ayayinda yajashi suka zauna kan kujera cikin sigar lallashi yace "se ana hakuri ana kaiwa zuciya nesa Abdullah. Yarane ka haifesu baka haifi halinsuba sannan duka baya gyara yaro" Alhaji Abdallah dake huci har lokacin yace "Toh ni bansan mezan mata tagyaruba! Nayi kwaban,nayi lallashin,nayi fadan amma duk abanza! Yanda kasan zuciyar kafiri haka nata zuciyar yake!akullum batada wani buri daya wuce ta kuntatamin ta tozartani a idon duniya" Alhaji Abdallah yayi maganar yana nuna Khadija daharynzu ke kankame da Mummy da yatsa bitterly,yace "i don't know what i did wrong to deserve such a Daughter! Ai wannan dai'ita gwara baka haifa bamaaa!" Sosai Alhaji Abdallah yabamasu Daddy tausayi anma dukda haka jin kalamansa akan Khadijar se Daddyn yahau kwabarsa,yace "Kul Abdullah ba'a yiwa yaro baki. Hannunka baya taba ribewa kacireshi kayar! Regardless of everything Khadija is your Daughter. Akullum anaso mu iyaye mudinga yiwa ya'yan mu kalamai masu dadi sannan basai kayi wani laifi ko don Allah bayasonka bane zai baka Ya'ya marasa ji but rather he's testing you and he only tests those he loves. Kokari zakayi kacinye wannan jarabawar bawai kadinga questioning fate dinka ba,kagode ma Allah ma ba duka ya'yan bane suka taru suka zama daya. Koba komai inwannan ya bata maka kanada mai share maka hawaye. Khadija ba takura da tsangwami take bukata ba face abita ahankali akuma sakata a addu'a" sosai maganganun Daddy sukayi tasiri akan Alhaji Abdallah haryaji yana regretting actions dinsa,yace "Nagode sosai da shawarwari Alhaji Muhammad zankuma yi kokari in yi amfani dasu insha Allah anma sede hakan bazai sa intaya Khadija baku hakuri ko inhana a hukuntata ba dankuwa nima decision dinda nayanke akanta tun kafin intaho gida ba fasashi zanyi ba as i feel this's the only solution to solve all this. Ayi mata hukunci daidai da laifinta,intakama akira hukuma nema duk i won't stop you sannan bazanji haushin kuba. Ai ita taja! Kome akayi mata shitayi deserving" Abbe ne yagirgizakai wannan karan,yace "Maganar a hukuntata ma duk baitasoba Abdullah. Ai anriga da anzama daya. Yanda Muzammil da Mami suke Yaranmu haka Khadija ma take 'Ya agurinmu. Abun baiyi munin dahar za akai ga wannan gabar ba tunda Alhamdulillahi Mami is still hail and healthy. Amatsayina na mahaifi na yafe mata kura kuranta duk ranar da taji cewa bata kyauta ba seta nemi Yanuwanta tarokesu suma su yafe mata dankuwa ba'a tursasa wani yayafe ma wani" yajuya yakalli Khadijar ayayinda yashiga yimata fada sosai akan tabi duniyar asannu takuma bi ahankali tacanza ways dinta. Bayan Abba yagama Daddy ma yayi nasa sannan Mummy. Maman Khady dake zaune gefe inbanda hararar Khadijan da karkada kafa babu abunda takeyi dan ita sam decision din baimataba,taso a hukuntata dede da laifinta acire wani batun family agefe,da ita batasan da cewa su Family din bane tayi musu wannan aika aikar hartake kokarin illata ma nephew dinta rayuwa? Dandai kawai tanajin  kunyar idanun Alhaji Abdallah da Sagiruuu ne da ba abunda zai hanata questioning decision dinsu Abban,aiwannan anbata lasisin gobema ta kara ne dan ita bataga akwai alamun yarinyar ta saduda haryanzu ba.

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now