Page Twelve

491 51 16
                                    


👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad

*You might not be able to understand somethings indai baki/baka karanta Rayuwar bintu ba. This's the continuation of that book though a different story line somehow. Abunda kadai zan iya fada muku shine this book is connected to Rayuwar bintu. To get a better glimpse of what I'm writing currently I advise you read Rayuwar Bintu first. Thannk you and happy reading*. 😍

*Page Twelve*

°°°
Ranar Friday bayan antaso daga sallar juma'a Muzammil dasu Khalil nazaune a parlournsu Muzammil na nuna musu videos din graduation day dinsa dasukasashi agaba kwanada kwanaki suna rokonsa sunason sugani wanda hakan yasa yau suna dawowa daga masallaci yadauko system dinsa yasaka musu suka baje a tsakiyar parlourn suna kallo ayayinda shikuma yake zaune kan three seater yana surfing through the internet da wayarsa.

Mami ne tashigo parlourn bakinta dauke da sallama. Azuciya ya amsa ayayinda su Khalil suka amsa a fili,Fa'iz yadago daga kallon system din da yakeyi yace "Adda Mami Hamma yanuna miki videos din gama makarantar sa?" Mami tagirgizakai alamar A'a tana murmushi sannan takarasa gefen Muzammil da haryanzu yake zaune kan three seater tazauna after putting alot of courage tace "Kukawo nan mugani, Its something i've been wanting to watch in reality sekuma Allah beyi ba" Mami takarashe maganar a sanyaye ayayinda tadubi Muzammil dahar lokacin bedago ba tace "Ina wuni Hamma?" Kallo daya yamata his face expressionless yace "Lafiya Lau" sekuma yatashi yanufi hanyar dakinsa yanacema su Fa'iz insun gama gani sukawo masa System dinsa.

Binsa da kallo Mami tayi awkwardly harya bace mata dagani kafin daga karshe jiki sanyaye tadawo da dubanta kan System dinda su Fa'iz suka daura mata akan cinyarta tun sanda tace sukawo system din suyi kallon tare,dukyanda Mami taso tamaida hankalinta tayi kallon gabadaya takasa dole daga karshe tahakura tatashi takoma sashinsu batareda tashiga gurin su Ameera wanda shine asalin dalilin zuwan nataba.

Dayanma Ameer yakarbo masu Mami kayansu daga laundry,haka Mummy tatasa su gaba adaki tace kowa tashirya kayanta cikin trolley dinta danba lallai the following day susamu time dinyiba tasan zasuce zasu fita yiwa yan uwansu da abokan arziki sallama because Sunday early morning zasu wuce Damaturu insha Allah. Suna cikin shirya kayanne Aunty Ilham da Deenah suka shigo. Mummy data kasa ta tsare sesu Mami sungama shirya kayansu kafin tabar dakin tadubi su Aunty Ilham tace "Yauwa Yan matannan,zuwanku yafimin zuwan gwamna wallahi. Maza Ilham zoki tsayamin akan yarannan karkowa tatashi seta gama shirya kayanta zanje inyi na Yayanku"dariya Deenah da Aunty Ilham suka saki,Aunty Ilham tace "Toh Yaya Bintu" Deenah tace "Ina wuni Mummy?" Mummy fuska daukeda fara'a tace "Lafiya Lau Deenah" sannan playfully takarada "Kindai gujemu kinkoma Yar Mama Fadi" Deenah tasaka hannu tarufe fuskarta tana dariya tace "Bagashi nazo yanzuba Mummy" Mummy tayi dariya tace "Toh yayi kyau" sannan tafice adakin.

Deenah takarasa bakin gado gefen Mami tana fadin "Yanzu ku dagaske tafiya zakuyi jibi bazaku jira mutafi rana daya ba?" Mami tace "Adda Deenah school is on session fah,we've missed alot" Deenah ta harareta tace "Don't start talking like Ameera now" dariya Mami tasaki tace "Toh nadena" Ilham tadubi Mami tace "Ameera tashigo ne yau" Mami ta girgizakai tace "No bata shigo ba dazu dai nace mata zanje sekuma nazo bankarasa gunta ba" Ilham tace "Okay. Inaga sabida kince zakijene yasa bata shigo dinba yet" Mami tajinjinakai tace "Inaga" Ilham tagyara zamanta tace "Sagiru yaje sashin Mama Fadi jiya munjima muna hira dashi,shine yakecemana tare zaku tafi Damaturu so Deenah complained,tace this is their first time coming to Yola dasunan hutu kuma harsuka jima haka amma ba inda suka fita gashi har hutun yazo karshe shine Sagiru yayi suggesting why not we organize a picnic and go for outing gobe dayanma at least we'll get to celebrate Muzammil's graduation da bamu samu munyi a South Africa ba due to abunda yafaru,we can get to give him the gifts we wanted to yasan zaiji dadi sosai and we agreed upon it immediately,akuma take nakira Ameera nafada mata.

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now