Page Forty Six and Seven

373 49 12
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

Zeeneert @wattpad

*Assalamu Alaikum CM Family. Bear with me pls. A previous page nace acanza door handle and then Khadija was later able to enter the apartment with the ex key na door handle din. Kunsan dan adam da mantuwa😁so just assume gyara handle din akayi ba canzawa akayi ba and we move.......... to those that are yet to read ma already nayi editing wurin a wattpad. Thank you so much for the love and support*

*Commander, Mami da Alhaji Sadiquuuu na godiya* 😍😘

*Page Forty Six*

Abunda Khadija bata saniba shine duk wannan abun Mami na biyeda ita abaya,ashe tun sanda alarm dinta ya buga Mamin ta farka takuma ga shadown mutum yatashi daga gurin kwanciyarsu a kasa yafita a dakin. Da fari bata damu da son sanin wanene yafita ba because it could be meshi yafita biyan wata bukatarsa a parlour ko kitchen ne but then her curiosity kept quenching her! takasa samun nutsuwa harsaida tasa hannu kan bedside drawer ta kunna hasken fitilar wayarta ayayinda taleka shimfidar yan Kannen nata tana haskawa. Ganin Khadija is the only person missing batasan sanda tasauko daga kan gadon cikin sauri ba tazari hijabi tabi bayanta. Gabadaya se zuciyarta ta dugunzuma kan cewa bawani bukatar dare bane yafitar da Khadijar a dakin. She's definately after something.

Aikuwa tana isa parlourn idanunta yasauka kan Khadijar na kokarin fita a sashin nasu. Binta tadingayi abaya ahankali yanda bazata taba noticing dinta ba harsuka isa sashin Muzammil din tabude kofa suka shige,dataga ta nufi hanyar dakin Muzammil seda zuciyarta takusa fitowa ta kirjinta tsabar tashin hankali. Taji kamar ta juya kada taje taga abunda zuciyarta bata tsanmanta ba dan tasan indai hakan tafaru sedai adebeta a sume ayanda takejin bugun zuciyarta yanzu haka but then kalaman Waleeda sesuka shiga yimata yawo a kwanya!

"Itake binshi take kokarin cusa kanta agareshi shi sam bata gabansa! tasha kokarin lalata masa rayuwa anma yaki bata hadin kai!"

Dawannan tunanin Mami tasamu karfin gwiwar cigabada bin Khadija harsuka shiga dakin Muzammil,ita tayi sauri tashige bayan labule ta labe tana leken Khadijar. Bakin gado ta sashin da Muzammil ke kwance taga Khadijar tanufa tazauna gefenshi  tanayi mashi wani irin kallo cikeda sha'awa,can tadaga hannu takai fuskarshi kamar zata fara shafashi kome tatuna seta fasa. Mami seda numfashinta yakusa daukewa ganin abunda Khadijan ke shirin yiwa Muzammil hakanan batasan sanda tasauke wani nannauyar ajiyar zuciya ba tana lumshe idanu ganin ta fasa.

Setaga tatashi da sauri ta karasa bakin carpet din dakin tashiga kokarin ciro wani abu a cikin bra dinta. Can segashi tafito da wani abu cikin tsumma,Warware tsumman tayi and the laya vividly appears! wani irin zare idanu Mami tayi ayayinda zuciyarta tacigaba da bugun uku uku fiyeda na dazu! Tashiga maimaita kalmar Innalillahi wainna ilaihi rajiun acikin ranta tana kallon ikon Allah! Akan idanunta Khadija ta daga carpet din dakin tasaka layar tasashin da Muzammil ya farka abunda zaifara takawa kenan sannan tamaida carpet din ta ajiye tagyarashi tsaf kamar yanda yake daaa. Tafi three minutes tsaye gurin takalli inda ta saka layar sannan tadaga kai ta kalli Muzammil dake ta aikin baccinshi ayayinda take sakin wani irin murmushin da itakadai tasan ma anarsa kafin can tajuya tafice a dakin. Mami seda ta kara kusan five minutes acikin labulen gudun kada mistakenly Khadijan tadawo sannan tafito. Karasawa tayi bakin carpet din tadaga inda taga Khadija tasaka layar tacirota cikin sauri ayayinda ko ina na jikinta ke bari. gani take ko sakan daya layar ta kara agurin zatayiwa Muzammil illa! This's the first time data fara ganin laya da idanunta sede a fina finai kuma sudinma bawai tataba yarda da al amarin bane,tadauka anasakawa ne kawai a wasan kwaikwayon dan akayata labarin tayanda mutane zasu so su kalla bawai don hakan yana faruwa agaske! Bata taba yarda akwai mutanenda sabida son duniya da son zuciyarsu zasu iya dukufar da rayuwar wani tawannan fanninba anma segashi yau tayi mugun gani da idanunta! Kuma ba akan kowa ake shirin yiwa aika aikarba se dan uwanta dukda kuwa dabadan kaddara ta gitta sunhada dangatakar ba babu abunda zaisa tadinga addressing dinshi as such! Dan Ummi da Daddy! dago hannunta tayi ayayinda tashiga karema layar kallo wondering what keeping it here means! Yanzu da bata farka ta biyo bayan Khadijar ba what would've happened?what damage could it have caused in Muzammils life da ace ya tsallaka koya taka? wani bugu da zuciyarta tafarayi ne yasa taji batamason imagining what would've happened. What matters is she was able to stop Khadija from her evil acts kuma dagayau tadau damarar yin hakan harsaitaga karshen makircin ta. Badan halin Muzammil ba, only for martaba da farin cikin familynta.

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now