Page Thirty

617 74 33
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad

*page Thirty*

Washegari tun sassafe hilux biyu na sojojin dazasu raka Muzammil da Abba Yola suka iso gidan,alokacin Abba da Muzammil na zaune kan dinning a can sashin su Mami suna breakfast,daman in Abba nagari can Muzammil yake cema Uche yakai musu abincin inyaso shiyaje yasamoshi Abban suci tare. Abba najin karar shigowan motocin sojojin yadubi Muzammil curiously yace "Do we really have to go with them?" Muzammil yasauke kanshi kasa ahankali yace "I'm sorry Abba. It's a rule,i can't go out of the town without them" Abba yasaki murmushi yace "I'm not complaining Son,tambaya kawai nayi" murmushi kawai Muzammil yasaki bece komaiba,aransa yana ayyana da ace yanada power dinda zai iya yakice wannan rule din da tuni ya yakiceshi danshi kanshi bawai yanason tsaron nasu baneba kawai dandai bayida yanda zaiyine.

Anyi la'asar bada jimawa ba suka shiga garin Yola,koda suka isa family house din straight fadar Abba Babba suka wuce,Abba da Muzammil suka sauka,sojojin ma suka sauka duka suka karasa cikin Fadar suka gaisa da mutanen ciki sannan sojojin suka ma Muzammil sallama suka wuce masaukin su dasuke sauka duksanda suka zo Yolan ayayinda sukabar Muzammil da Abba anan fadan kan the following day su zasu wuce Maiduguri dan Muzammil anan Yola zekare satin zuwa ranar friday yabi flight yasamo su acan Maidagurin. Atakaice dai Muzammil besamu shiga gida ba seda aka idar da sallar maghrib. Koda yashiga gidan parlour bakowa se TV da AC daketa aiki,
Parlourn yacanza from yanda yakeda,ansaka sabbin furniture's na zamani ankuma canza painting din gabadaya.
Dakin Ummi Muzammil yawuce yatsaya abakin kofa yayi knocking harsaida tabashi izinin shiga sannan yatura kofar bakinshi daukeda sallama,da mamaki Ummi ke kallonsa daga sama harkasa,baki sake tace "Kaikuma saukar yaushe?" dankuwa dagashi har Abban bawanda yasanar dawani cewan suna hanya yau,Su Ummi dai sunsan Abba na Nigeria kuma dole zezo Yola kafin Yakoma.

Muzammil ya karasa Inda Ummi ke tsaye ya rungumeta yana fadin "Bayan la'asar dinnan muka shigo gari,munacan fadar Abba babba dasu Daddy seyanzu nasamu shigowa" Ummi tace "Shine kadauko hanya baka sanar dakowa ba?" Muzammil yasaketa yana murmushi yace "Bagashi na iso lafiya ? And I'm not alone Ummi,tareda Abba mukazo" Ummi da gabadaya farin cikin ganin Dan nata yakasa boyuwa kan fuskarta se murmushi takeyi tace "Aishikenan,amma ya akayi ko karar motocin mutanen naka banjiba?" Muzammil yace "basu karaso nanba,suna ajiyemu a fadar Abba Babba suka ajiyemu suka wuce masaukinsu" Ummi tace "toh sannun ku da zuwa maraban kuda isowa"
Muzammil yayu dariya yace "Yauwa Sannu Ummi,ina wuni?" Ummi tace "Lafiya lau,Ya hanya? Yakuka baro mutanen Damaturun?" Muzammil yace "Kowa lafiya lau Ummi suna gaishe ku" Ummi tace "Masha Allah" sannan curiosly takara da "Tareda Abban naku kukashigo ne yanzun?" Muzammil yagirgizakai yace "Aa,na barosu a masallaci tareda Daddy inaga sesunyi sallar isha zasu shigo" Ummi tace "toh yanzun azubo maka abincine kozaka jira Daddyn ku su shigo muci gabadaya?" Muzammil yace "Zanjira sushi go,it's been long we eat like a Family" sekuma yashiga kallon kofar dakin Ummin jin har lokacin bejiyo hayaniyarsu Fa'iza kosu Fa'iz daga dakunansu ba yace "Ummi kekadaine agidan wai?" Ummi tace "A'a Sa'adah na dakinsu,Fa'iza da Fa'iz nedai baswanan,dazunnan Ameer yamaidasu makaranta. Kasan insunfara jarabawa Hostel suke komawa se weekend suke zuwa gida" Muzammil yace "No wonder! Shiyasa naji gidan tsit" Ummi tayi dariya tace "Sune masu hayaniyar daman" Muzammil yayi murmushi yace "Yaushe suka fara jarabawar?" Ummi tace "Tun last week" Muzammil yace "Allah yabasu sa'a,kafin nakoma zanyi kokari inleka su mugaisa danbazankai next week weekend agariba"

Ummi tace "Allah yabada iko" Muzammil yace "Amin"

Fa'iz da Fa'iza anan MAUTECH suke karatu. Atsarin Daddy Ya'yansa Maza awaje suke karatu ayayinda Mata kuma anan gida Nigeria and Fa'iz is his only son dake karatu a Nigeria wanda kuma ba laifin Daddyn bane,shi Fa'iz dinne yanuna hakan yakeso sabida irin shakuwar dake tsakaninsa da twin sister dinsa Fa'iza. Ashekarar dasuka gama secondary school Daddy yasama ma Fa'iz admission a London itakuma Fa'iza a nan MAUTECH,ana kawo musu labari Fa'iza tahau kukan yaza ayi a rabasu,shima Fa'iz yace bazai tafi yabartaba sede itama anema mata a can din sutafi tare. Daddy ko yace basu isaba,atsarin shi Ya'yan sa Mata babu maitafiya waje karatu so inma zasu kwantar da hankalinsu kowa ya yi a Inda aka nema masa yafi amma sam suka ki,Fa'iz yace ya hakura zaizauna anan din suyi tare Daddy yataima yaje yanema masa alfarma ko a supplementary list ne asashi.

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now