Page Sixty One

470 50 23
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

Zeeneert@wattpad

*Page Sixty One*

Tako yi sa'an samunsa inda tasanar dashi sakon Daddy. Babu bata lokaci Al'amin yatafi can gate din Family house din yana kuma isa bada jimawa ba suka iso inda yayi musu jagora zuwa Fada bayan sun gaisa yayi musu sannu da hanya. parlourn da ake saukan baki anan Fadan yasaukesu daganan yaje yasanar da iyayen nasa isowarsu. Daddy da Abba Babba ne suka nufi masaukin bakin inda Daddy Babba yacigaba da zamansa a Fada,koda Daddy yasanar dasu zuwan su Sadiq din kamar yanda shima Mummy takira tasanar dashi awaya cewa yayi they should count him out. Aisanda akaje akayi kulalliyar bada masaniyarsa akayiba so babu ruwanshi kuma suma dazasu burgeshi subar Abban ya warware matsalar da kansa amma Abba Babba yace baza'ai hakaba!

Tarba ta musamman su Daddy sukayi musu dukda kuwa zuwan nasu was something more like an impromtu visit. Kankace me ancika gabansu da ruwa,lemunan gwangwani,fruits dakuma damammen fresh fura da Nono daba'a rabuwa dashi a Family house din hakanan komai akakaima iyayen za'akaima Sadiq dake falon Mama Fadiiiii dankin shiga tareda iyayen nasa yayi yazauna a mota wai kunya inda Al'amin yasanar da Daddy shikuma yace yashigar dashi parlourn Mama Fadiii.

Aka kuma tura ayo musu ordern abinci da snacks da kajin dazasu tafi dashi kafin lokacin lunch yayi. Seda suka sha ruwa aka gaggaisa tareda introducing juna kafin Aminin mahaifin Sadiq yashigo da zancen dalilin zuwan nasu harya gama.

Abba Babba jiki sanyaye yace "I would have been glad to give out my Granddaughter to your Son dankuwa na tabbata Aliyu(Muazzam) bazai taba baku damar zuwa gida neman Auren Yarsaba inbai yaba da halin Yaron dakuma irin tsatson daya fito ba and by just sitting and talking with you all for few minutes nayarda da hakan nima anma sede wani hanzari ba guduba and I'm really sorry to announce to you Maryam ayanzu ta haramta ga Sadiq.......jiya Kakanta Yayana kenan ya daura mata aure da Wanta kuma Dan uwanta" and everyone was shocked at the news,sukaji abun kamar wasan yara ayayinda suka dinga juye juye suna kallon juna da mamaki in disbelief

Daya daga cikin Baffanun Sadiq ne yakasa shiru yace "Bangane an daura mata aure jiyaba? Dama akwai zancen ta da Dan uwanta shine akasa muka ajiye ayyukan dake gabanmu muka taho takanas ta kano dan ayi abunnan?" Abba Babba yace "Kuyi hakuri zanyi muku bayanin komai yanzu" and they all gave him listening ears trying to keep their calm

Abba Babba yafara da basu labarin irin shakuwar dake tsakanin Mami da Muzammil tun suna yara zuwa girmansu,tafiyar Muzammil makaranta,fara soyayyarsu, dawowansa,tafiyarsu Mami Sweden not long after dawowar Muzammil,shirye shiryen aurensu da Muzammil yaitayi for the past 6years while anticipating their return,what they came to know shida Yayanshi and all that transpired from day before yesterday harzuwa yanzu. Be boye musu komaiba harta guduwan da Mamin tayi tareda sharrudan da Daddy Babba ya gindaya. Akarshe yace "Ban baku labarinnan dan in bude sirri ko intona halin da ahalina ke ciki ba sedan in wanke mu agurinku. Dukwanda yasanmu yasan asalinmu yasan mu mutane ne masu nagarta dakuma sanin mutunci da darajar dan Adam. Bamu kiraku takanas ta Kano dan muci zarafin ku ko mu nuna muku iyakarkuba. Dan mune yayi laifi by giving permission ayi neman aure kan aure and believe me shima beyi dan ya tozarta kuba,anashi tunanin hakan shine best solution bayan abunda yafaru tsakanin Yara biyun whilst it's not. As an elder and future second successor of the family kamata yayi yaduba lineage dinda iyaye da Kakanni suka bari dakuma yanda familyn zaicigaba da tafiya kai ahade ba well being din Yarshi kadai ba dahar hakan yasa baiyi consulting dinmu ba yaje yayi yin kanshi which results to everything that's currently going on. Ayanzu haka maganar danakeyi muku he's not in his right state of mind,bemasan kunzoba nakuma tabbata kidimar hukuncin da muka yanke dakuma barin Maryam gida ne yasa ya manta baisanardaku sakona ba tun ashekaranjiyan and so on behalf of him and my entire family members muna baku hakurin kadwaita ma Danku Auren Maryam da akayi,taso daku da akayi daga wani gari zuwa nan a irin halin tsadar rayuwar damuke ciki yanzu. Find a place in your hearts to forgive us as it wasn't deliberate! Yanda bazamuso wani yamana haka ba muma bazamuyima waniba and inamai muku albishir dacewa tunda kuka zo bazamu bari kukoma haka ba! Mudauka cewa wata kaddarar ce ke kokarin gittawa tsakaninmu daku shiyasa komai yafaru ahakan. Kamar yanda nafada acikin labarin dana bayar dazu danmun hana Danku Maryam bazamu hanashi sauran yan uwantaba. Tanada kanne Mata biyu gakuma cousins dinta nan wanda inada tabbacin inbesansu duka bama yasan wasu acikin su...yaduba yagani in akwai wacce tamasa aciki nabasa duniya wa lahira,zanbiya masa sadaki inkuma yimasa alwalanci inkun amince bakuda matsala da hakan"

CAPTAIN MUZAMMILDove le storie prendono vita. Scoprilo ora