Page Sixty Eight

1.1K 67 52
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

*Zeeneert*@ wattpad

*Page Sixty Eight*

Cikin rada yace "Anya abunda ke zuciyar ki kenan Mami?are you sure your heart is clean and pure towards me?are you sure you're only angry because munsaba ma addini da values din society and we're at the verge of shiga hakkin Iman ko akwai wani abu daban?" Kukan da Mami keta kokarin rikewa tasaki a kirjinshi! Itakanta tasan she's just hiding her true feelings under a facade! Bakomai ne ke dawainiya da'ita ba face kishi dakuma ganin tana dab da rasashi!

Muzammil yasa hannu ya rungumeta sosai cikin jikinsa yanajin kowani sautin kukanta kamar ana watsamai ruwan dalma a jiki,ya lumshe idanu araunane yace "Stop decieving me and yourself Mami......I'm sorry I overheard your conversation with Abba the other day bankuma je da niyar invading privacy dinku ba.  Naje zanyi masa sallama akan washegari da sassafe zankoma Abuja kunnawa na suka jiyemin komai" yadagota daga jikinshi yana kallon cikin idanunta disappointedly yace "And innace miki I'm not disappointed nayi karya! Bakiyiwa zuciyata adalciba dakike tunanin taki zuciyar kadai ke dawainiya da soyayyata Mami. In a zamanin yarintarmu da farkon dawowana daga South Africa kinyi tunanin so na Yan uwan taka kawai nake miki zan iya yi miki uzuri but my later actions should have proved otherwise! Ashe Dan uwa na shiga damuwa in Yar uwar sa na fushi dashi akan laifin da baimasan dashiba? Ashe Dan uwa na iya driving for morethan 20hrs batareda ya hutaba sabida kawai yanaso yayi beating time ya riske Yar Uwarsa kafin tabar kasar suyi sallama? Ashe Dan uwa na turawa Yar uwar sa love messages day and night harna tsahon shekaru shidda?Ashe Dan Uwa na bibiyar rayuwar Yar uwar sa watching all her movements gabadaya rayuwarta? Ashe Dan Uwa na kishin Yar uwar sa dan wani namiji ya rabeta koya nuna interest akanta? Ashe Dan Uwa na iya sacrificing nasa happiness din sabida Yar uwarsa? Ashe Dan Uwa na iya batawa da kowa even if it means going against his family sabida kawai ya faranta ma Yar Uwarsa? Ashe Dan Uwa na iya ajiye ayyukan gabansa na tsahon kwanaki yatafi neman Yar Uwarsa dukda kuwa adalilin kin aurensa tagudu tabar gida?Ashe Dan Uwa na iya romancing Yar Uwarsa affectionately batareda yana sonta ba?Does that one night at Stockholm and the moment savored at the Car meant nothing to you?" Muzammil yakarashe maganar ayayinda ya tsareta da manyan idanunsa masu kama da zaiba dake cikeda abubuwan da ada take musu mummunan fahimta!

Yasauke numfashi ayayinda yakamo hannunta yasaka cikin nashi yacigaba

"Aiko makaho ya shafa yasan matsayin Mami azuciyar Muzammil!
Ameera bata taba zama barrier a soyayyar danake mikiba babu kuma wanda zai taba zama. I've loved you from day one! Nasoki tun nida ke bamusan inda kanmu yake ba! You were and will always be the woman I love" yace "Nasan zakice in hakane miyasa na yi rejecting dinki in the first place? The news came to me as a shock Mami...." sekuma yabata labarin tunanin dayakeyi ada dakuma yanda sukayi da Daddy da Ummi daya fada musu.

"Sabida haka bake kadai ke wahala ba"

Yakai hannunshi setin kirjinsa tana jin yanda zuciyar sa kekai kawo na wucin gadi yace "saurari yanda zuciyata ke bugu! Dauriya kawai na fiki Mami! I'm just trying to be strong for US! I'm just trying to make it easy for US anma wannan tada hankali da ramar da kikayi na kokarin ruguzaminsu. Wallahi da abune me sauki da tun aranar namaida Auren mu but then rainin wayau da wasa da hankalin iyayen zaiyi yawa. Ga uwa uba alkawarin danadaukarwa Chief of Army"

Mami tarasa shin farin cikin tagane Muzammil na Sonta zatayi ko bakin cikin abubuwan dataitayi abaya wanda shine silar halinda suke ciki ayanzu,cikin gunjin Kuka tace  "I'm sorry I ruined US.....I'm the reason for our destruction....!" Muzammil disagreeingly ayayinda yake girgiza mata kai yace " You did not ruin us and you were never the reason for our destruction Mami. Kaddarar mu ce tazo ahaka and we'll accept it gladly! Amma sede hakan bazai taba yuyuwa ba seda hadin kanki. You've to be strong like i'm trying too! Inaso kimaida komai ba Komai ba! Kisa aranki we were not meant for each other as husband and wife babu kuma alheri a tarayyar mu shiyasa komai yafaru! Kisa aranki Allah zai baki wanda yafini shiyasa ya hanaki ni for every disappointment is a blessing in disguise and you'll see how easier it'll be to accept this Destiny of ours...."

CAPTAIN MUZAMMILHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin