Page Two

1K 63 11
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Asmeeey_h(Zeeneert)*💕

Zeeneert@wattpad

*Page Two*

Acan dakin su Mami Ammi da Naana kwance suke suna kallon Cartoon a tashar Neckeledeon hankali kwance,cikinsu babu wanda tacire uniform din islamiyarta as Mummy expected,suna shigowa suka kunna TV suka hau kallo kasancewar lokacin yayi daidai da lokacin da akeyin series na cartoon dasuke kallo kullum.

Mami tana shigowa kashe socket din TVn tayi gabadaya dayake yana kusa da kofar dakin. Baki sake Ammi da Naana suka bi Yayartasu da kallo

Naaana kamar zatayi kuka tace "Ayyah Addaaa Mamiiiii....." Mami tace "Mummy ne tace kutashi kuyi wanka" wannan karan Ammi ce tayi magana ashagwabe "inmun gama kallon zamuyi ai" strickly Mami tace "No yanzu tace kutashi kuyi inbahaka ba kuma no body should step out from the room for dinner with his tsatsaman jiki" Ammi da gabadaya ranta yagama dagulewa tashi tayi tana tura baki gaba "but there's still time before dinner ai. Harzamu gama kallo muyi wanka before time yayi"

Naanaa ta marairace murya "Yes Adda. Don Allah kibari mukarasa gani it's our favourite series kuma baswa repitation se next week wednesday za akumayi and it'll be the next episode" Mami batareda ta kallesu ba tawuce changing room dinsu dake cikin dakin donta sauya kaya tashiige wanka tana fadin "sekuma kuyi ai"

Ammi tana ganin Mami tashige changing room duban Naana tayi tace "Naanaa jeki kunna mana" make kafada Naanaa tayi "Aa nikam tsoro nakeji Adda Ammi" hararanta Ammi tayi tace "Bakiji metace bane? She said saimuyi ai. Meaning mu kunna"

Make kafada Nanaa takumayi,gabadaya atsorace take tace "Nidai tsoro nakeji kisake tambayarta intayarda se in kunna" tsaki Ammi tasaki sannan tatashi daga kwancen da take takarasa kusada changing room dinda Mami tashige ta tsaya daga bakin kofah kamar wata munafuka ta marairace murya kamar mutumiyar kirki "Adda Mami don Allah mukunna? I promise anagamawa zansaka Naanaa agaba muje inmata wanka nima inyi" Mami datariga tagama jin duk conversation din Ammi da Naaana murmushi tasaki tana girgiza kai
Tace "bazafah ku kunnah ba. Ai lokacin sallan inyayi ba jiranku zaiyiba so inzakuwuce kuyi abunda zaifisheku gwanda kuwuce kuje kuyi" sumui sumui haka Ammi taja kafarta tafice adakin dom zuwa laundry ayayinda tace Nanaaa tabiyo bayanta.




Mami tana daga cikin closet taji sanda suka rufe kofar dakin alamun sunfita daga dakin. Sake girgizakai tayi tareda furta "Unbelievable! A 14 year old still obsessed with cartoons" akullum son kallon cartoon din Ammi baya daina bata mamaki. When she's young she's a big fan too,tare suke kallo anma data fara mallakar hankalin kanta tuni abun yafita aranta anma gashidai ita Ammi takasa dainawa kuma bata tunanin she's ready to stop anytime soon. Ko yaushe rai zata daina? Oho.

Mami kayanta tacire tasaka bathrobe dinta sannan tashige hadadden bathroom dinsu dake daukeda kayan zamani aciki and it looks very clean and tidy,warm water tahada cikin bathtube sannan tashige tafara wanka. Koda tagama wankan kasa fitowa tayi daga cikin bathtube din,tajima tana lailaya jikinta dankuwa yanayin dumin ruwa bakaramin dadi yayi mata ba kasancewar lokacin sanyine. Seda taji ana anfara kiraye kirayen sallar maghrib sannan tayi sauri ta dauraye jikinta tadauro alwala sannan tafice a bathroom din. A changing room dinsu ta tsaya tashirya kasancewar kayan sawansu daduk kayan shafansu anan suke.

Wani soft and cotten mixed pink and sky blue riga da wandon sleeping wears dinta tasaka,tasaka hula akanta sannan tadauki hijabin datake sallah dashi sannan tafito dakin donta yi sallah. Dede lokacin Ammi da Naana suka shigo kowannensu daureda towel hakanan jikinsu a jike. Da alamadai daga wanka suka fito suma

Da mamaki Mami tadubesu tace "A ina kukayi wanka?" Ammi tace "A dakin Mummy. Muntajira kifito baki fito ba shine Mummy tace muje muyi adakinta kar lokacin sallah tayi bamuyiba" jinjinakai Mami tayi sannan tace "sorry. i got carried away nama manta bakuyi wankaba wallahi. Go wear your clothes kuzo kuyi sallah" cewa sukayi "toh" ayayinda suka wuce changing room din inda itakuma tashimfida sallaya tatada sallah. Koda Mami ta idar da sallar evening azkar tashigayi calmly harta gama.

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now