Page Seven

570 43 5
                                    


👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad

*You might not be able to understand somethings indai baki/baka karanta Rayuwar bintu ba. This's the continuation of that book though a different story line somehow. Abunda kadai zan iya fada muku shine this book is connected to Rayuwar bintu. To get a better glimpse of what I'm writing currently I advise you read Rayuwar Bintu first. Thank you and happy reading*. 😍

*Page Seven*

Cikin lokaci kankani mutuwar Hajja yagama zagaya Family house din hakanan rasuwar bakaramin jijjigasu yayi ba kasancewar garas take,tadan kwana biyu batayi rashin lafiyarta baitashi ba. Gashi kuma daman ita kadaice Babba data rage a ahalin bakidaya sauran duk Allah yakarbi abunsa. Tumbido Shekaru biyar dasuka wuce yakoma ga Allah wanda hakan yasa Abba Babba yakarbi ragamar rike Family House din tunda daman shida Daddy ne manya and Daddy kuma acan Yobe yake zaune,there's no way za a bashi wannan resposibilty din.

Su Ameera da Mami kuka kamar suyi yaya suna al ajabin abun ayayinda suke reminiscing moments dinsu daita.

Mami tatuna sanda shekaranjiya Hajja kecewa su Ameera "Dukranda Mami tazo koyar damun fura da Nono aguna inason kuzama shaida kukuma tuno da maganar damukayi yau dinnan" ashedai itakam tafiya zatayi tabarsu Allah baisa zataga wannan ranarba. Tatuno Muzammil da irin shakuwar dasukayi da Hajja. She's just imagining how he'll react if labarin rasuwar Hajja ta riskeshi,sekawai takuma fashewa da kuka. Kankacemai gidan yafara cika da jama'a kama dagakan yan uwansu nawaje,yan unguwa dakuma abokanan arziki. Haka akayima Hajja sutura akakaita gidanta na gaskiya.

Su Hajiya Mami da Daddy kam basu samu damar halarta jana'izar ba kasancewar sunyi nesa bazaiyuyu a jirasuba anmadai aranar suka taho,isowan yanma sukayi. Khadija da iyalinta da iyayen Ummi suma duk aranar suka iso inda daganan kuma aka hau zaman makoki. Ummi mahaifiyar Alhaji Muallim,Uncle Faiz da Naina,Uncle Hanif,Uncle Mudassir da Aunty Hafsat duk basu semu zuwa ba dayake ba akasar suke da zama ba sedai suka kira a waya sukayi ma su Daddyn ta aziyar rashin Hajja da akayi. Aunty Surayya dasu Mami ke kira da Ummi lagos ne kawai tasamu zuwa acikin cousins din Daddyn. Tareda first Born dinta Abubakar da matarsa with their little Daughter sukazo. Sekuma Deenah who's her 2nd to the last child da Sagir who's her last born. Deenah is 20years while Sagir sa'an su Mami ne and lokacin rasuwar yayi daidai da lokacin dasuke hutun makaranta shiyasa Ummin lagos din tataho dasu.

Attorney Kamaludden da Matarshi tareda Hamma Sagir sunzo anma sede su kwanansu uku sukayi suka koma. Sagir kawai suka bari dasuka tashi tafiya kasancewar daman shi yazo da shirinshi,daga Yola zaibisu Abba suwuce Damaturu inda acan zaiyi service dinsa. Ummin Lagos kuwa se anyi sadakan bakwai zasu koma su,acewarta sun kwana biyu basu zo Yola ba gwanda Sudan zauna suyi ziyara kafin sukoma. Acan gidan su tasauka ayayinda take zuwa kullum tawuni indare yayi takoma.

Deener da Sagir kuma suka dage anan Tumbido family house zasu zauna cikin Yan uwansu

Maganar tafiya South Africa kuwa tuni aka ajiyeshi gefe guda.

☆☆☆

OR TAMBO INTERNATIONAL AIRPORT,JOHANNESBURG,SOUTH AFRICA

Kyakyawan Saurayine dabazai wuce shekaru ashirin da uku zuwa huduba kezaune kan daya daga cikin Fancy chairs dinda ke cikin OR TAMBO International Airport dake cikin birnin Johannesburg a South Afica. Bakine though more of a choculate coloured skin yakedashi. Bayida wani tsayi sosai dan baza acemasa dogo can sosai ba hakanan baza asakashi cikin jerin gajeruba. Madaidaicin hanci gareshi dankuwa his nose is not that pointed to an extent. Yanada manyan idanu dasuke farare kal gwanin ban sha'awa. Fatar jikinshi kuwa it's so smooth barinma fuskar dankuwa ko kwarzane bazaka gani ba bare halamar wata spot din kuraje. Yanada kwantattacen sajen dake matukar karama fuskar sa haiba akullum. Muzammil is not an epitome of beauty but for sure he has this charisma dabazaka iya kallonshi kasaka shi cikin jerin marasa kyau ba.

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now