Page Thirty Six

362 49 18
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

Zeeneert@wattpad

*Alhamdulillah! We're finally back after a long break zamukuma daura daga inda mukatsaya. To each and everyone of you,thank you so much for the patience,love and support. I pray you enjoy every bit of the continuation😍😘❤ nagode kwarai*

*Page Thirty Six*

Aiko inhakane daba karamin wauta tayi ba wurin rashin iya controlling kanta agabansa. Toh amma yazatayi? Its not as if this is what she plans too. abune da yafi karfin ikonta da iyawarta.

Itakanta tarasa meke faruwa da'ita yau. yanzu haka sotake tajuya ta fada mai kalaman dazasu sa yadaina tunanin dayakeyi akanta but she couldn't find the right words. Tarasa dalilin dayasa presence dinsa has so much effect on her,tarasa dalilin dayasa presence dinsa ke warware mata dukwani lissafinta. Intana kusa da shi gabadaya neman hankali,tunani da nutsuwarta takeyi tarasa se zuciya,ruhi da gangar jikinta ne kawai ke karbar ragamar aikin.

Sannan intayi maganar ma ai kaman ta tsargu ne tunda bawai fitowa yayi fili yaceda ita yagane presence dinsa always has effect on her ba,daga yanayin tune din maganar sa dake dauke da mischievousness tagane hakan and by trying to say something in her defence she'll only do nothing but prove his instincts right which will clearly prove herself guilty. Kuma itafa bawai taji kunyarsa bane sabida taki shigarmai da abinci apartment dinsa yayi putting question mark akan kotayi watsi da tarbiyar da akayi masu. A'a taji kunyarsa ne sabida yagane haryanzu tanada weakness akansa bayan wannan ita sam bataga wani laifin datayiba. Hasalima tsayawa datayi daga bakin kofa bata shiga cikiba ko'ina akaje shine daidai al'adance and above all kuma a musulunce. Akowani hali ta tsinci kanta arayuwa bata manta wadannan abubuwa biyun ba sabida haka koda ace bataga Muzammil a wannan yanayin ba harta firgita his door step will always be her stopping point so far as he's the only human living inside that apartment(addinin mu yakoyar damu cewa duk inda Mace da Namiji suka kebe guri guda toh tabbas inba third party na ukun nasu shaidan ne). Aiko Mummyn da ta aikota ta tabbata this's what she's expecting her to do sannan tanada tabbacin Mummyn nada yakinin koda ace tayi niyar yin abunda baidace ba cikin shagala or unknowingly Muzammil being the elder and more sensible one will put her back on the right track shiyasa taturota without any hesitation but then here he's doing the opposite tahanyar questioning tarbiyarta bayan kuma shikansa tanada tabbacin yasan abunda tayin shine tarbiya!

Zata iya kinyi wa Muzammil shaida akan komai amma banda rashin tarbiya,zata iya zarginsa akan komai amma banda kaucewa addini because she trusts their parents upbringing takuma tabbata shima yayarda danata upbringing din the same way. Kusan zata iyacewa ma Muzammil dasu Ameera sunfisu sani sosai because they were islamically moulded by two parents(Ummi and Daddy)unlike su da Abba yafi Mummy sani sosai. Mummy wasn't lucky to have attended good islamiya right from her childhood due to irin gwagwarmayar rayuwar data taso acikinta.

But then if this is the case miyasa Muzammil yafadi wadannan kalaman?tasan ko kadan he didn't meant each and every word he says

Toh kodai abunda take hasashe ne yazama gaskiya? Kodai rashin iya controlling kanta da tayi dazu a dining yasa yahada wannan ti'ilimin sabida yashiga zargin ko haryanzu tanasonshi ne daya tabbatar kuma seya samu damar cigaba da toying da zuciyarta kamar yanda yasabayi a shekarun baya,Ya samu damar mocking dinta yanda ranshi yakeso tahanyar nuna mata cewa even after all he did to her in the past wahalalliyar zuciyarta haryau takasa daina sonsa dan ta lura ba abunda yake burgeshi yake kuma sakashi cikin nishadi irin yaga ya tozartata. Yes tozarci! dankuwa bata tunanin akwai wani kalma dayayi suiting abubuwan da yayi mata six years back fiyeda TOZARCIN! He denied their love affair in front of their parents whilst she did the opposite when inza abi al'ada irin tamu ta fulani da bahaushe shine yakamata yafi kowa raising wannan maganar yakumayi protecting everything they had for each other without any shame agaban kowa unlike ita Mace da aka fi so tazamanto mai kara da alkunya but then he ended up doing the worst wanda har adalilin hakan yasa an alakantata damai tabin kwakwalwa! Yasa antono wani shafi daga cikin kundin kaddarorin mahaifinta da akayi shekara da shekaru da binneshi sannan aka alakanta ta dashi! Inbata kira wannan TOZARCI ba dame zata siffanta wrong doings dinsa agareta?

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now