Page Thirty One

447 51 15
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad

*You might not be able to understand somethings indai baki/baka karanta Rayuwar bintu ba. This's the continuation of that book though a different story line somehow. Abunda kadai zan iya fada muku shine this book is connected to Rayuwar bintu. To get a better glimpse of what I'm writing currently I advise you read Rayuwar Bintu first. Thannk you and happy reading*. 😍

*Page Thirty One*

Mami har suka dauki hanyar gida bata ceda kowa uffan ba cikin motar amma fa sede dazaka tono karkashin zuciyarta zakaga irin zugi da kunar da zuciyartata keyi mata. Tarasa takaimaimai me Muzammil yake nufida ita,tarasa meyake so,tarasa ribar meyake samu daya kasa sakar mata mara tayi fitsari yake bibiyar rayuwarta haryanzu. Ta so shi tun a jaririyarta,taso shi tun bata da wayau,taso shi tunma kafin tasan menene so hartazo tasan menene so. She loved him with every myth she had ayayinda shi ya karyata soyayyar ta agareshi.

Ya ce baya sonta,ya karyata soyayyarsu agaban iyayensu,yasa aka alakanta soyayyar da takeyi mishi da hauka,ya kunyatata,ya muzanta ta agabansu,yanuna musu itadin bakowa bace agareshi anma dukda haka ta kyaleshi bata cemai komai ba toh me kuma yake so?is this how he repay her for being silent for this whole time?koya Mamin dayasani abayane haryanzu? Ko ya dauka bata gama sanin wanene shi bane? koya dauka haryanzu batasan shidin mutum ne dababu abunda bazai iyayi ba don yasamu abunda yakeso batareda yadamu da halin dazai jefa wasunsa ba?Koya dauka duka abubuwan dayakeyi din suna tasiri akanta kamar yanda sukaitayi abaya ne? Koya dauka haryanzu sonshi takeyi shiyasa takasa yin komai akan dukwani abu dayakeyi din?Tajinjina kai,lallai kuwa inhakane yayi babban kuskure dankuwa batun yau tagaji da cin kwan makauniyar da yakeyi mata ba!ba tunyau tagaji da pretense dinsa ba,batun yau tagaji da using innocence din yan uwansu dayakeyi to satisfy his own selfish reasons ba hakanan batun yau takeson ayimata iyaka dashiba. albarkacin iyayensu da baswason kowa yasan halin da akeciki,harsu Ammi kawai yakeci shiyasa haryau take overlooking duk wani abu dayakeyi,acting as if batama San yanayiba batareda ta dauki wani kwakwran mata ki ba. Farin cikinta daya,they'll be going back to Nigeria soon,koba komai in one way or the other dole kowa yasan abunda yafaru 6years back dankuwa they can't hide it forever,dole questions will arise sooner or later and that will be the end of everything. Zata huta da overlooking pretence din Muzammil kowa yasan matsayinsa,zata sa ayimata iyaka dashi because at the stage she's in her life;bata bukatarsa!she has nothing to do with him! He was important in her past life but not in her present life,shidin wani kaddararren al'amarine dayafaru da ita a baya dabata fatan yafaru da koda makiyinta ne bare kuma yakuma wanzuwa cikin Rayuwar datake ciki ayanzu. Kai! ita dada hali ma ko crossing path batason takuma yi da Muzammil amma yazatayi tunda dangantakar iyaye yahada?and if that's the case,she wants nothing beyond that relation.

Tatuna yanda kowa yakeyin su yake kuma farin ciki da auren zumuncin da sukasoyi kokuma tace taso yi,tunda shi yace abun bahaka bane agurinshi,tasan everyone is now anticipating for their return atada maganar and she wonder how they'd react in sukaji anfasa suka kuma ji dalilin daya sa akafasa din. Bawanda yake bata tausayi ma irin siblings dinsu dasu keta dabbaka abun,barinma Ammi da Faiza dasuka fi kowa zakalkalewa. Tun farkon dawowansu Sweden da Muzammil yamaida Ammi CID dinsa tasha nuna mata tadaina amma sam taki,akullum takwabi Ammi Ammin cewa take "Nibansan wani irin laifi Hamma yamiki ba kike irin wannan fushin dashi,gashi shima yaki fadamin but believe me he regret his actions and he still loves and care for you Adda Mami,give him another chance please na tabbata bazakiyi dana sanin yin hakan ba......" Inko taki kulata setahau mita "Haba Adda Mami,dan ina baki shawara shine zaki manna min? nidai kinsan gaskiya nake fada miki kuma fasaba! Aiko Allah mukanyi masa laifi ya yafe mana bare kuma mu bayinsa" akwai ranar da har kararta takai gurin Mummy da Abba wai tana gaba da Muzammil, laifi yamata yakumace yagane kuskurensa amma taki hakura. Alokacin murmushi tasaki dankuwa ta tabbata da ace Ammi tasan abunda Muzammil din yayi mata da tuni tabar goyon bayansa.

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now