Page Sixty Four

682 57 11
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

*Zeeneert*@wattpad

*Page Sixty Four*

Babu wanda yasan da dawowar su Mami a family house din se yan gidansu,suma ba duka ba. Sunko yi mamakin ganinsu sosai a salasainar daren dan Muzammil besanar da kowa yasamu Mami ba bare zancen suna kan hanya yau zasu dawo.

A masallaci sallar asubahi Muzammil ya hadu da Kakanninsa,Uncles dasauran Yan uwansa Maza. Abun mamaki kuma Daddy Babba ranshi be baciba jin tareda Mamin suka dawo sema cewa dayayi yanason ganin su a Fada by 10am.

Aikuwa karfe goman nayi suka tafi Fadan,abun mamaki sesuka tarar da iyayensu,baffanansu da Kawunai duk sun hallara sukawai akejira,Daddy Babba yayi hakanne sabida already akwai gutsiri tsoma daketa yawo atsakani agame da batun Mami da Muzammil din and so he wants to clear everything agaban kowa shiyasa ya gayyacesu gabakidaya. Yara ne kawai bai gayyata ba as maganar bata shafesuba and if akwai abunda yakamata susani yasan zasuji daga bakin iyayen.

Bayan anbude taron da addu'a Daddy Babba yadubi sashin da Muzammil ke zaune yace "Yanzun daka debota kuka dawon harkun daidaita kanku ne ko kaima ta koya maka taurin kai,rashin da'a da biyayyar nata ne?"

Muzammil ya girgiza kai jiki sanyaye yace "Bahaka bane Granpa......" Daddy Babba yace " Banason nuku nuku amsar tambayar da namaka nakeso kabani" Muzammil ya sunkuyardakai kasa a raunane yace "Bamu daidaita ba...." Daddy Babba da harlokacin idanunshi nakan Muzammil yace "Uhummm....?" alamun yanason karin bayani.

Muzammil yadubi ahalin parlourn baki daya yace "Nasan abunda zan fada ba lallai yayiwa kowannenku dadi ba and I know nida Mami have been putting the family at the edge for the past few weeks. Nasan hukuncin da aka yanke was because you all want nothing but the best for us but then shiga hakkin wani at the expense of that babban hadari ne Granpaaa. Mami has made it clear and went to such extent that she doesn't like me anymore and her reasons are very valid. dukdama wasu daga cikin actions dinnata were totally wrong she don't deserve to be going through all this. Ninayi mata laifi bani kuma da hanyar kare kaina agareta and so I should be the one suffering and being punished not her. In ance za'acigaba da tursasata akan lamarin nan abunda zaicigaba da biyo wa baya bazaiyi mana kyauba duka ba which might lead to the destruction of the Family. Adalilina dakuma selfish interest dina bazan so inaji ina gani abunda akayi shekara da shekaru ana gina shi ya rushe lokaci gudaba shiyasa na yanke hukuncin bawa Mami takardarta kafin mu iso gida" and every one is shocked at revelance na Muzammil except Daddy Babba,da alama Yaran sundaina bashi mamaki.

Muzammil yatashi ya karasa inda Mami take zaune yakarbi takardar sakin daya bata adaren jiya ya karasa gaban Daddy Babba idanunshi jawur in subdue yace "Forgive me for the disobedience and going against you Granpa. Kayi hakuri ka yafe mana nida Mami musa arai cewa Allah yasa hakan shine mafi alheri and we were never meant to be"

Daddy Babba tunda muzammil yafara magana yake kallonshi sekeke,kallon mamaki and disbelief ba fushi da tunzura daya saba yi koda yaushe in ana issues irin haka ba. He looked so calm and a good listener kamar ba Daddy Babba ba wanda hakan yasake bawa Muzammil tsoro haryakai karshe. The old man is just soo unpredictable at times!

Besake shan mamaki ba seda yaji Daddy Babban na fadin
"Kagama.....?"
Aikuwa ya rude hankalinsa yasake tashi ayayinda ya sunkuyar da kai kasa batareda ya iya cewa komaiba. wai meyake faruwa ne?

Yanaji Daddy babba yadaga waya yayi kira. Besan dawa yayi magana ba anmadai yaji yace da wanda yake wayar tazo parlour yanzunnan yanason ganinta.

Se iyayen suka shiga kus kus agame da revelation din Muzammil din. Wasu na korafi da bakin ciki ayayinda  wasu me farin ciki (e.g. Ummi da Abba). Bayan kamar mintuna goma haka sega Ameera tashigo parlourn bakinta daukeda sallama. Gabadaya se attention dinsu yakoma kanta cikeda mamaki anma sede duk mamakinsu bekai na Muzammil ba. Yaushe tadawo? And why is she here? Miyasa Daddy Babba yayi summoning dinta? Badai tana kokarin fallasa sirrin su baneba?! Take yashiga girgizakai zuciyar shi na ayyana mishi

CAPTAIN MUZAMMILजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें