Page Fifty Two

309 51 16
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

Zeeneert@wattpad

*Assalamu Alaikum CM fam. Anyi sallah lafiya? Allah yamaimaita mana. To those that are not aware i was sick before Eid shiyasa kuka jini shiru sekuma akazo aka shiga hidimar sallah but we're finally back Alhamdulillah and yes nida TUMBIDOS muna nan muna jiran kason naman mu from each and everyone of you....lols* 😅

*Page Fifty Two*

Khadija tasa bayan hannunta tagoge hawayenta tana sauke numfashi kamar gaske kafin tafara bayani,tace

"Nayarda dafari bana gabansa anma tunda akayi recruiting dinsa yafara aiki a Abuja muka fara nema,kusan kullum muna tare inbaya gidanmu ze kirani insamo shi a office har yakaiga yafara inviting dina gidansa. Haka zai daukeni muje muyi kwanaki acan yasani inyi karya a gida cewa gidan yan uwan Hajiya natafi. Alokacin idanuna sunrufe da soyayyarsa dakuma irin alkawarurrukan dayakeyi min kan zai aureni shiyasa without hesitation nabashi kaina! Nazo na fara daukan cikinsa haka zai lallabani muje asibiti azubar! Innayi masa maganar aure yace bayanzu ba akwai wani abuda yakejira in lokacin yayi zai sanar dani ahaka har akamai transfer yadawo nan garin aiki still babu abunda yacanza a tsakaninmu dan kamar yanda nake karya inje gidansa a Abuja inyi kwanaki haka nake zuwa nanma. After so many years of togetherness and some unfulfilled promises kwatsam segasu Abba sundawo shine yanzu yake kokarin juyamin baya koma ince yajuya din!

Yadaina kulani,yadaina kula duk wani al amari dayashefini,yayi watsi daduk wasu alkawarirruka dayamin abaya acting as if i never existed in his life. Akwai ranarda har threatening dina yayi kan innasake nuna akwai wani abu tsakaninmu zaiyimin abunda har inmutu bazan taba mantawa dashiba and this's all happening because of MAMI! ayanzu baya ganin kowa se ita shiyasa nikuma nadauki alkawarin lalata nata rayuwar kamar yanda ya lalatamin nawa,koba komai zan huce takaicin abubuwan dayamin,koba komai we'll be equal indan budurcin dashine sanadiyar rabani dashi ne yasa yake wulakanta ni..." Khadija ta karashe maganar ayayinda tasake fashewa dawani kukan makircin

Maman Khady da tunda Khadijar ke bayani zuciyarta ke tafarfarsa batasan sanda tadubi Daddy ba tace  "Wallahi yarinyar nan karya takeyi Muhammad" Daddy yabudi baki zaiyi magana Maman Khady ta dakatar dashi tahanyar dagamai hannu tace "A'a Muhammad kyaleni inyi magana! Haka kawai yarinyar karama bazatazo tataramu guri guda tana tsaramu da labarai tamaida mu shashashaii ba" adole Daddy yaja bakinshi yayi shiru abunka da suruka(Yayar Ummice ai inbaku mantaba)

Maman Khady tamaida dubanta ga Khadijar rai bace tace "ke dubeni dakyau! Inkowa a parlourn nan besan makirci da take taken yan bariki irinki insuka kwallafa rai akan da namijiba toni nasani,nakuma ga dubunki wallahi tallahi! Tun ranar da nafara ganin ki dama nagane idanunki abude suke baza ayi abun arziki dakeba kawai naja bakina nayi shirune sabida gudun kada ace nacika yawan magana da shishigi but not when you're trying to tarnish my Sons image and dignity! Muzammil dakike gani ko yatsan macen daba muharramarsa ba bazai iya rikewa deliberately ba bare har akai ga zancen Zina! Sede inkece kika sashi adaki kika duramai kwayoyi kikamai fyade dan ko asirce shi kikayi yunkurin yi bana tunanin zaibishi dan dagashi,iyayensa,Yan uwa da abokan arziki da irin masoyan da Allah yabashi babu wanda bayamai addua,fatan alheri dakuma Allah yatoni asirin masuson ganin sa a rana irinki and I'm sure adduartamuce takabarsu yasa asirin ki yatonu sabida haka inzakidaina kukan munafurcin nan gwanda ma kidaina ki amshi laifin ki. Mami kuma dakike gani nan gani nan bari dumamen mayya budurci setakaishi gidan Muzammil ya amshe abunsa sede kihadiyi rai ki mutu dan mere munafurcin ki be isa ya rusa soyayyar da aka ginata tun tale tale ba..."

Kowadai a parlourn kunya kamar yayi yaya sabida irin baranbaramar da Maman Khadyn keta aikinyi,barinma Muzammil dayaji kamar ya nutse cikin kasa dukdama he was stunned by how she believed and have trust in him daharsaida idanunsa suka cikoda kwalla anma Maman Khady ko akwalarta,ta inda take shiga batanan take fitaba amma dukda haka Khadija batayi giving up ba,tasake fashewa dawani sabon kukan harda shesheka tace

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now