Page Twenty One

425 49 8
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad

*Page Twenty One*

Abba daukan Mami yayi yafice a parlourn cikin sauri ayayinda Daddy,Ummi,Muzammil da Mummy datunda abun yafaru batace komaiba suka mara mishi baya. Sashinsu yawuce da'ita yakaita dakinsu yakwantar,yadubi Mummy dagabadaya hankalinta tashe yake  yace "Kawomin ruwa Fatima" cikin sauri tafice a dakin taje Kitchen tadebo ruwa a cup takawo masa.
Karba Abba yayi yazauna gefen Mami abakin gadon yadibi ruwan kadan yashafa Mata a fuska,seda yayi sau uku sannan ta farfado. Tashi tayi tazauna tana kallon Abban da Mummy dan Ummi,Daddy da Muzammil daga parlour suka tsaya. Abunda yafarune yashiga dawo Mata daya bayan daya kawai seta fashe da kuka tana kallon Abba tace "Abba wallahi Hamma karya yakeyi,shida bakinshi yace yana sona sede incanza ra’ayi yayi yanzu" Abba cikeda tausayin Mami yamatsa kusa da'ita yakwantar jikinshi yana shafa bayanta soothingly araunane yace "I know Mamana,I believe you" Mami in subdue tace "Ya cuceni,yagama da rayuwata Abba. I can't live without him......" sekuma tasake fashewa dawani sabon kukan
Abba yace "Kul Mamanaaa! Stop saying that,gatanki yawuce ace bazaki iya rayuwa sabida babu wani Da namiji ba. You've me, you've your Mother, you've your siblings and most importantly Allah sabida haka kar insake Jin wannan maganar a bakinki"
Muzammil safa da marwa yake tayi agaban dakinsu Mami,jiyakeyi kamar yabude yashiga yaji halin da Mamin take ciki ganin tunda Mummy tafito tadibi ruwa a cup takoma babu wanda yakuma fitowa daga dakin,Gashi Family Doctorn dayakira harlokacin be karasoba,wayarsa yaciro a aljihu zaisake kiransa yaga wayar tamutu,daman tayi battery low. Tsaki yasaki tareda dafe kai sannan yadubi Daddy da Ummi dake zaune parlour looking so worried too,so yake yaje yace susake kiran likitan anma besan dawani fuska zaiyi hakanba bayan suna ganin shine sanadin state dinda Mami ke ciki. Jiki sanyaye ya maida dubansa kofar dakinsu Mami.
Few mins after that sukaji anyi sallama daga waje,dasauri Muzammil yanufi kofar jin muryar Family Doctor dinnasu ne.
Shigo dashi yayi suka gaisa dasu Daddy sannan yamasa jagora zuwa dakinsu Mami. Knocking jikin kofar Muzammil yayi Abba yazo yabude,yana ganin shine rai bace yashiga kokarin maida kofar ya rufe. Cikin sauri Muzammil yace “I am here with the Family Doctor Abba. Zaiduba yanayin jikin Mami” Abba dahar zece likitan yatafi sekuma yayi tunanin yakamata likitan yaduba Mamin incase akwai wani matsala don haka seya matsa gefe yabama likitan hanya yashiga dakin bayan sungaisa,Muzammil yunkurin bin bayan likitan yayi Abba batareda yadubeshiba yayi sauri yashige ya turo kofar daga ciki.
Wuri Abba da Mummy suka bashi guri yaduba Mami bayan sunmasa bayanin suma tayi,after few minutes yagama gwaje gwajensa yace “ She's fine now. She just passed out due to shock so zanyi mata alluran bacci sabida tasamu hutu to relieve herself from stress da allluran yasaketa she will go back to normal Insha Allah”
Abba yace "Okay but do you have the injection with you?" Likitan yace "No babu anma yanzu zanje insiyo indawo" Abba yace "toshikenan seka dawo din" daganan likitan yafice Muzammil yabi bayansa cikin sauri yana tambayarsa yanayin jikin Mami suka tafi tare ayayinda acan dakin kuma Abba yakoma gefen Mami dake zaune tajingina da head din gadonsu looking so pale,janyota yayi zuwa jikinsa ya kwantar yana shafa bayanta soothingly,Mami wasu sabbin hawayene taji sunshiga bin kuncinta,she still cant believe Muzammil yakaryatata akan gaskiyarta gabansu Abba da Ummi. Does he even love her anymore ?cox she doubt if he does danmai sonka bazaiyi maka abunda yamata ba. To anma kuma ina soyayyar tatafi?
Muzammil ko 30mins basuyi da fitaba suka dawo likitan yashiga yama Mami alluran,in few mins bacci yadauketa jikin Abba.
Ahankali Abba yakwantar da'ita kan gado ya lulluba Mata blanket sannan yatashi  sukafice da likitan donya masa rakiya yabar Mummy zaune gefenta. Suna fita likitan yace "She'll sleep all day,se 11 nadare first dose zai saketa daganan kuma second one zaifara aiki se after another 8hours yasaketa gabadaya, by then she'll be fine insha Allah inkuma akwai wani matsala bayannan seka sake kirana" Abba yace "Okay Doctor nagode sosai" inda daganan sukayi sallama yazauna parlourn gurin Daddy  don Ummi tun fitowar Abba da likitan tawuce ciki taduba yanayin jikin Mami ayayinda shikuma Muzammil yayi walking likitan out.  Daddy yace "How is she feeling now?" asanyaye Abba yace "Alhamdulillah. She's asleep now,yamata alluran bacci" sauke nannauyar ajiyar zuciya Daddy yayi sannan yadubi Abba pleadingly yace "I'm sorry about everything that happened  Mu'azzam....." Cikin sauri Abba yashiga girgizama Daddy kai yace "Don Allah kadaina bani hakuri Yaya. It isn't your fault,Yarane ka haifesu baka haifi halinsu ba. We're all victims here, dani dakai duka bahaka mukaso ba anma sedai daman kana naka shima Allah yana nashi. Mudai muyi fadan Allah yasa hakan shiyafi alkhairi" Daddy yace "Hakane Mu'azzam anma sedai ni aganina hukuncin daka yanke baiyiba,its too early to say that. Fasa maganar aurennan dakake cewa ayi kamar anbar Muzammil yayi nasara ne indai dagaske yaudaran Mamin yayi,how can we let him go like this bayan yayi playing with her emotions? Ko da wani ne yace yaje yace Yana sonta? Bamu muka hadasu ba su suka hada kansu so banga dalilin dazaisa rana daya yajuya bayaba. Cikin familyn nan babu wanda baisan da zancennan ba,yau akace babu zancen auren Mami da Muzammil what do you think they'll say kokuma wani irin kallo zasu mana?sannan in akabarshi kamar anbama sauran yara masu tasowa avenue din yin the same thing ne thinking they will get away with it" Abba yace "Bazance maganar ka bata kan hanya ba Yaya anma ni aganina disadvantage din ayi auren yafi yawa akan kar ayi din. Yes Muzammil bekyauta ba kuma ya yi playing da emotions dinmu duka anma gwanda a hakura din kawai tunda Allah yasa mungane dawuri. Hakura da maganar auren is far better than ayi din azo ana samun matsala daga baya. Maganar mutane kuma you can't stop it Yaya sannan bazamuyi abunda zai cuci Ya'yan mu sabida maganar mutane ba dankuwa bamu da tabbacin they will stay happy after that sannan in abu yazo ya kwabe akarshe dole mutanen suji kuma ananne bazaka iya hanasu maganar dabakason ayi dinba. Sautari kuskuren da iyaye keyi kenan,anfi tsoron abunda mutane zasuce than happiness din Ya'yansu,anfi tsoron maganar mutane than consequences dinda in akayi abun zebiyo baya"

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now