Page Twenty Five

427 52 9
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad

*You might not be able to understand somethings indai baki/baka karanta Rayuwar bintu ba. This's the continuation of that book though a different story line somehow. Abunda kadai zan iya fada muku shine this book is connected to Rayuwar bintu. To get a better glimpse of what I'm writing currently I advise you read Rayuwar Bintu first. Thannk you and happy reading*. 😍

*Page Twenty Five*

Ameera tashi tayi daga kasa tadawo ta sashin dayamaida kallonsa tazauna tace "I'll explain everything right from the beginning harzuwa yau,I can even tell you all the content dake cikin chats din seka duba if yayi tallying da abunda nafada and if still you're not convinced after that sekasa ayi binciken but I assure you I'll still be the culprit ko bayanan" shidai Muzammil bece Mata komaiba kuma be kalli inda takeba har lokacin amma yna sauraronta. Ameera tashare hawayenta dayaki daina zubowa cikeda nadama sannan tacigaba da magana "Four years back sanda katafi South Africa kasan lokacin yayi tallying da su Mami sunzo hutu nan so koda muka rakaka airport a Abuja nan muka dawo duka. Toh bayan tafiyarka kullum Mami setayi kuka,in ance tazo taci abinci setace bazataci ba sede akaita gunka kuci tare. Haka Mummy zata kamata tamata dure tana ihu,inmuna wasa bata shigowa cikin mu kullum tana daki tana makonka,gabadaya bata walwala like before and that makes me so Sad seeing her that way dukda kuwa alokacin banida yanda zanyi dankona je gurinta bata saurarona. Seven days da tafiyar kane dadare Muna dinner a dinning Daddy kefadama Ummi aiyana office ka kirashi har video call ma kunyi kuma kace mai zakuna iya communicating time to time inkaje CAFE din cikin makarantar ana bari kuma kace inkasake samun lokaci zaka koma kakira kagaisa damu though babu rana. Murna muka dinga yi kamar muyi Yaya alokacin Dan we were all sad da daga baya akace ba abari kuyi amfani da waya a makarantarku meaning bazamuna samu muji daga garekaba.

Naso inkaima Mami good news din awannan daren amma nasan koda wasa Ummi bazata bari infita ba kasan dawuri muke bacci sabida zuwa makaranta don haka na hakura kan the following day inna taso a makaranta dayake Thursday ne babu islamiya zanje insameta inmata albishir. Aikuwa the following day din inadawowa a makaranta ko uniform bancireba nawuce sashin su but I was not lucky to see her,Uncle Noor yazo gida dasafe dayatashi tafiya yace zaitafi dasu gidan sa itadasu Ammi su wuni dayanma zaidawo dasu.

Sashin mu nakoma kan dayanma insun dawo naje inmata albishir din,a parlour na tarar da Ummi da Aunty Ilham dabata Jima da zuwa ba sunata hira akan wani Indian film daza'asaka a Bollywood in aka gama shuffle dinda akeyi lokacin,Naji Aunty Ilham nacewa taji ance film din nada dadi sosai dukda kuwa tsohon film ne.

Ummi tace "Gaskiya tsohon film ne sosai don tun ina Yan Mata na kallah anma ya hadu sosai gakuma abun tausayi ciki" Aunty Ilham tace "Aiko ba inzauna in kallah toh Aunty Yusyyy" Ummi tace "Nima dakika ganninan sake gani zanyi,shidasu Kabhi kush kabhi gham,kuch kuch hota he,Kedai duka tsoffin films dinnan ko sau dari zan gani bana gajiya da kallonsu" Aunty Ilham tayi dariya tace "Haka wata Mamar kawata ma. Intaga suna kallon sabbin Indian films setace aiduk shirme suke gani Indian film masu ma ana dakyau Sena da" Ummi tasaki dariya tace "Ai gaskiya ne,kwata kwata bata inda Zaki hada films din da dana yanzuma" Aunty Ilham dake dariya tace "Kema hardake kenan Aunty Yusyyy" Ummi tayi dariya tace "Bayanzu zaki kalli film dinba? Inanan dake ana gamawa kema Zaki dawo team dinmu" nidai daki nawuce not minding what they were saying ko film dinda suke magana akaidin,wanka nayi nasauya kaya sannan nasake fitowa don indibi lunch anma sena tarar still su Ummi hirar film din sukeyi,Ummi tanadan briefing Aunty Yusra kan yanda film din yake.

Dinning area natafi nazubo abincin a plate anma memakon inwuce daki ko inzauna a dining inci senaji inason kallon film din nima jin yanda Ummi keta hyping dinsa,parlourn nazo nazauna alokacin kuma anfara film din dan se ananne ma naga ansa sunan film din bayan angama listening sunayen casts din cikin movie din because sanda nashigo nasamu su Ummi suna hirar already sunfadi sunan film din

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now