Page Fifteen

461 59 10
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad

*Page Fifteen*

Suna isa Zaria akaje akayi preparing release papers na Sadiq akabashi,murna agurin Sadiq kamar yayi yaya haka ya rungume Muzammil yana yimasa godiya heartily. Muzammil yace "Kagode ma Allah Sadiq danshine abun godiya"

Wujajen la'asar suka koma hotel shida Captain Abbas,wanka Muzammil yayi sukaje masallaci sukayi Sallan la'asar sannan yadawo dakinsa yakwanta bacci, bashi yatashi ba seda Captain Abbas yadawo a masallaci maghrib prayer beganshi acan ba yasa yashigo dakinsa yatashe shi yace "Muzammil katashi kayi sallar maghrib har an idar a masallaci" Muzammil yatashi yazauna a tsakiyar gadon yana fadin "Toh" sannan yasauka yashige bathroom donyin alwala wanda hakan yasa Captain tashi yakoma dakinsa shima.

Muzammil na idar da Sallah bayan yagama evening azkar dinsa wayarsa dake ajiye kusa da pillown daya kwanta kai yajanyo,missed calls din Mami da Ummi yatarar. Dialing number Ummi yayi yakara a kunne, Ummi na dagawa from her side tace "Son wai inakashiga ne inata kiranka baka picking" Muzammil yace "I was sleeping Ummi kuma nasaka wayar a silent shiyasa banmasan kinyita kiraba" Ummi tace "Waini yaushe kakoyi baccin yanma ne Muzammil?" Muzammil yayi yar dariya yace "Bafa kullum nakeyi ba Ummi" accusingly Ummi tace "Bawani,ranar daka dawo daga South Africa ma kayi" Muzammil yace "Allah Inna gajine nakeyi,ranar I was so exhausted yauma nadawo hotel agajiye shiyasa" Ummi tace "Toh kadai daina babu kyau" Muzammil yayi murmurshi yace "Toh Ummina" Ummi tace "Ya Zarian toh?hope things are moving smoothly over there?"

Muzammil yace "Komai Alhamdulillah Ummi" Ummi tace "Toh Allah yacigaba da baku nasara" Muzammil yace "Amin ya rabbi,yasu Sa'adah? Ina Yar Amirmira? Kowa yakirani yatambayeni yana isa Zaria anma banda ita" Ummi tace "Sa'adah nacan gurin Daddynku Amira kuma gatanan tanama jinka" sekuma yajiyo muryar Amira a background din tana fadin "Ayya Hamma am banzauna bane badai, school is hectic gashi JAMB exams dina next week" Muzammil yace "Bawani! duk busy schedules dinki bekai na Mami ba these days but she always find time to communicate with me" Ameera tayi dariya tace "Toh tuba nake Hamma,kayi hakuri zangyara. I will call you right away inkungama magana da Ummi" Muzammil yace "Banaso kirike gaisuwarki,seda na roka?" Ummi dakejinsu tayi dariya tace "Son Inka biyema halin Amira akan busy schedules gaba gaba magana ma dena Mata zakayi" Muzammil yayi dariyar shima yace "I know Ummi,was just pulling her legs. Allah dai yakawo ranar dazaa gama Makarantar nan muhuta da excuses" Ummi da is still laughing tace "Amin" daganan sukayi sallama yakatse wayar.

Tashi yayi ya ninke sallayar dayake kai ya ajiye a ma ajiyinsa sannan yafice a dakin. Captain Abbas yabima suka fito tare suka sauka kasan hotel din suka shiga retuarant suka ci abinci,even after they finished their dinner basubar gurin ba,Zama sukayi suna Yar hirarrakinsu. Se after 9pm sannan suka koma masaukinsu kowa yayi retiring to his bed. The following Morning Muzammil yakira Chief of Army,tun adaren jiya dasuka dawo daga restaurant yaso kiransa anma ganin dare yayi yasa ya hakura yace bari yabari seyau dasafe.

Bayan sun gaisa bayani yashiga masa kan abubuwan dake faruwa daga zuwansu Zaria zuwa yau game da case din Alhaji Sammani din inda daga karshe yace "I'm thinking of handling this case alone Abbu,like seriously look at the way the DPO acted akan case din shopkeeper dinnan" Chief of Army yayi murmurshi irin nasu na manya yace "How will you handle the case all alone Muzammil?" Muzammil boldly yace "I am thinking of seeing Alhaji Sammanis wife privately,zanfada Mata duk halin da ake ciki sannan in nuna Mata no one is to be trusted, including us we really have to be very careful. I will ask her to call me alone in kidnappers din suka kira already inada wani plan in mind, I'm looking forward to it" Chief of Army yace "But that is not right Muzammil,don't you think by doing that you'll make the citizen question our work and not trust us anylonger tunda har atsakanin mu ma babu yarda?inmu bamu yarda da junanmu ba tayaya Suma zasuyi entrusting dinmu?"

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now