BIYAYYAH

By maryamad856

41.8K 1.9K 467

Labari ne akan wasu masoya guda biyu da suka had'u wajen yiwa iyayensu BIYAYYA. 'Kir'kirarran labari ne b... More

BIYAYYAH
BIYAYYAH
BIYAYYAH....
BIYAYYAH...
BIYAYYAH...
BIYAYYAH......
BIYAYYAH....
BIYAYYAH.....
BIYAYYAH....
BIYAYYAH....
BIYAYYAH......
Biyayyah......
biyayyah.......!
biyayyah.....!
biyayyah.....!
biyayyah....!
biyayyah....!
Biyayyah....!
Biyayyah.....!
Biyayyah.....!
Biyayyah....!
biyayyah.....!
biyayyah....! 59-60
Biyayya....61-62
biyayya....62-63
biyayya.... 65-66
part.....67
biyayy.....68
biyayy....69
biyayy....70
biyayya.....
biyayya....73
biyayya......73
biyayya.....74
biyayy......75
biyayya......76
biyayya....77
biyayya.....78
biyayya.....79
biyayya.....80
biyayya....81
biyayya.....82
Last page....83
Appology/Biyayya....12-14

biyayya......

833 37 5
By maryamad856

*BIYAYYA*

       Writing by
       *Maryam Abduul*

  Wattpad@
  Maryamad856


*Page...71*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

-----------Auta kam ba ita tabar gidanba sai wajen magrib dan saida tatsaya ta dad'a tayata suka gyara gidan, tare da kunna mai turaren wuta masu qamshi.

Auta na fita dije ta fad'a tiolet nan tai wanka, tana fitowa ta shiga feshe jikinta da wasu dad'ad'an turaruka tare dayin wanka da humra da kwalakca.

Wata dogowar riga tasa ta atamfa tai hayewarta kan gado tare da jawo wani littafi tashiga karantawa.

Ashraf kam bashi yashigo gidanba sai wajen goma na dare lokacin kam dije ta dad'e dayin bacci.

Saida ya shiga d'akin nata, kwance ya taddata qarasawa yai tare da bugun gefen filonta.

Cikin bacci dije taji kamar ana dukan wani abu dake kusa da ita hakan yasa ta bud'e idanuwanta take kwa ta saukeau kansa yana tsaye ya sa hannayensa cikin aljihun wandansa, tare da kafeta da ido.

Mitsttsike idanuwan nata tai kan ta yinqura ta miqe zaune, cikin ranta fad'i take" ko meyazo yi kuma oho"

Kallonta yai tare da gyara tsayuwarsa kan yace" waya baki izinin kwanciya?"

Jin tambayartai wata iri, take tashiga maimaitata acikin zuciyarta kan tace" baccinma bada izininsa akeyi?, to Allah ne yaban iko da izini har nasami yi"

Ashraf ya juyar dakai gefe cike da cize lebe kan yace" wow yayi, amma duk da hakan saina bada izini  to kunna, dan haka kisameni a falo bakuma nason jira" yana gama fad'a yai waje.

Dije dyage kafad'a tai kan ta miqe tare da jan hijab dinta tai waje.

Yana falon azaune, kusa dashi tasamu tazauna, tana zama yakalleta tare da fad'in " bawai nakiraki ne ko dan inason ganinkiba a'a sabida inaso kisan sharad'an zaman gidanne dan haka ki bud'e kunnuwanki dakyau kiji mezance"

Batare da yajira amsawartaba ya d'ora da fad'in " abu nafarko shine bance miki ina buqatar wani cima daga wajenkiba, dan haka in zaki jagwalgwalon ki to kiyi ke d'aya. Abu na biyu shine kullum ki tabbatar kin rigani tashi, da zarar kin tashi kuma duk fad'in gidan yazamana lallai kin sharesa tare dayin mofin d'in sa. Sannam ina so ki tabbatar kin wanke min motata sabida bana fita da mota ba'awankeba.

Abu na biyun qarshe kuma shine, ke zaki dinga budan gate idan zan fita da kuma bayan nadawo and lastly kuma kada ki kuskura ko dawasa muna ido biyu dake dan bansan ganinki ko kad'an, dan haka ki kiyaye, ban kumace ki riqe karki fadawa kowaba wannan yarage yanaki, amma ki sani matakin dazan dauka bazai miki dad'i ba"

Yana gama fad'a ya miqe tare da barin wajen.

Dije kam jinjina wannan baqin hali nasa kawai take meyasa baya da zuciyar kirkine, bakomi insha Allahu zanyi biyayya agareka ya Ashraf, kamar yadda nayiwa iyayena biyayya na aureka, zan maka duk abinda kakeso da yardar Allah"

Da wannan tunanin ta miqe takoma d'akin ta sai dai sam takasa baccin tunanin halayen kawai Ashraf takeyi meyasa hakane, shi zuciyarsa bata da sanyine?, batason sanda bacci yai awon gaba da itaba.



.....Washe gari kamar jiya haka ta tashi da wuri qasa ta sauka nan tahau aikin da yasanyata, saidai tamatuqar wahala sosai sabida suk sharar da take bata taba irintaba dan gidan da girma yake sosai, amma dan tasamu tacimma manufarta saita kasa gajiyawa haka ta daure ta gama aikin.

Nan tadawo falo shima haka tayi, tana kammala tsaftace gidan ta fad'a kitchen duk da yace baison abincinta amma battajin zata iya qinyi dashi, dan Hanne sosai tamata fada akan hakan, koda yace" kartayi" to tayi amma kad'an kuda baiciba ta bayarga mai gadi ko almajiri.

Tuno da wannan yasata soya doya da qwai daman tarigada ta dafata, itama kadan tai sai cheeps da tasoya shima kad'an.

Nan ta jera komi a dinning, tana gamawa ta d'ebe nata ta haura sama abunta, saida tashiga tiolet tai wanka sannan ta zauna cin abunta.

Ashraf kuwa koda ya sakko saida idanuwansa suka sauka kan dinning d'in murmushi kawai yai tare da nufar qofar fita.horn biyu yai bai kuma sakya yiba.

Dije kam tana zaune tana katyawa taji qarar harm hakan yasata ajjiye doyar ta miqe tare da sakkowa qasa.kaitsaye gate din ta nufa nan tashiga qoqarin bud'e mai, saidai fa tasha wuya dan gate d'in babbane ga nauyi.

Ashraf kam yana kallonta ta mudubi yadda take uban zufa da nishi, saidai ko d'ar baijiba saima wata dariyar mugunta dayai, saida yazo dab da ita sannan yabawa motar wuta, itakam yana fita ta maida qofar ta rufe tare da riqe kwankwasonta game da fad'in " wash! Allah kaban ikom juriya da wannan ibadar tawa kabani ikon samun nasara acikinta taqarasa da ameen"

Komawa tai saman sai tajima gaba d'aya abincin yafita daga ranta, hakan yasa ta tattara ta sakko qasa, dinning ta nufa nan ta bud'e flask d'in ganin ba'a ta'ba komiba yasata tattara kayan a fridge tasa doyar da cheaps d'in nan tasakya gyara kitchen din sannan ta dawo falon, kan dugowar kujera tahau tare da miqewa kanta nanfa bacci yai gaba da ita.








Imran ne zaune gaban mom nasu Ashraf bayan sun gaisane yake miqamata duk wasu takaddu na dije akan makarantar koyan girkin dazata fara zuwa.

Mom ta kalleshi tace" ni da nafara tunanin ko abarahima tunda yanzi hutun baifi sati biyu ba, kaga mai zata koya"

Imran yace" a'a mom kibarta kawai tafara zuwa, inyaso mai lesson din ba sai ace yadinga zuwa weekend ba, koya kika gani?"

Mom tace" ehh hakanma yayi, kokuma yadinga zuwa kwana hud'u ba zamuyi magana da ita da kuma mommyn ku"

Imran yace" shikkenan, yanzu ko gobe ma zata iya fara zuwa, ni zan kaita sai nabada amanarta duk da narigada na gama magana da ita mai koya matan"

Mom tace" bakomi Allah yakaimu, ai nace da son din yazo zamuyi magana dashi"

Nan dai suka tsaida magana akan goben zata fara zuwa sannan yamata sallama.

Koda tagayawa dad yayi farin ciki tunda abin ai naqaruwane koba komi hakan zai temaka mata wajen jan ra'ayin mijin nata, nan yamata fatan nasara"



Da dare Ashraf yazo wajen mom kamar yadda tace" dashi" bayan sungaisane take tambayarsa lafiyar diyar tata"

Duk da cewa baison yatakeba, amma sai yakada baki yace" tana lafiya, tacema nagaidake"

Mom ta fad'ad'a mirmushinta kan tace" ina amsawa, yawwa son dama maganace akan makarantar da nakeso tafara zuwa kuma tana da matuqar mahimmanci, dan haka gobe zata fara zuwa idan ka koma inaso ka bata waya zamuyi magana"

"Ok mom, amma nifa banda lokaci kuma kinsan driver......"

Bata bari taqarasaba takatseshi da fad'in " kaga daman bance kai zaka kaitaba Imran zaiyi komi, ka huta mai aikatau"

D'an sosa qeyarsa yai aransa cayake" ashe ita da magulmacin ne " afili kuwa cayai" sorry mom"

Batace mishi qalaba saima dad'a jaddadamai datai akan"daya koma yabata wayar zasuyi magana" nan sukai sallama.

Koda yabar wajen Mom ba gida yanufa ba, gidansu Imran yawuce, nanma saida yajima danma Imran d'in ya fatattakeshi, amma asan ransa baiso komawa yanzuba.

Sai wajen goma saura sannan ya d'au hanyar gidan.Dije na kwance bacci yayi gaba da ita sosai, dan yau kusan a falon tayini, jin qarar motarsa yasata miqewa da sauri, nanfa tafita, haka tashiga jan qaton gate d'in harta bud'e mai.

Tana gamawa ta juya zuwa cikin gidan, samanta tai hayewarta tare da sa key aqofar d'akin nata.

Ashraf kwa yana gama dai-daita parking d'in sa ya wuce ciki kaitsaye d'akinsa ya wuce.saida ya kammala duk wani shirinsa sannan ya nufi qofar d'akin nata.sam baison abinda zai had'a shi da ita amma yazaiyi mom tasa dole sai yaganta.

Tura qofar yai sai dai gam yajita, hakan yasa yadanyi turus, gaskiya baijim zai iya buga mata qofa ai yawa nema.aikam juyawa yai yakomawarsa dakinsa yai kwanciyarsa batare da yasakya bi takantaba balle yacika umarnin mom d'in nashi.





....Da safe kamar kullum haka Dije ta kammala duk wani ayyukanta, wanda bata wani sha wuya kamar jiyanba, dayake jiya shine farkon farawarta.

Tana kitchen tana had'a abinda zatasa abaki taji kamar motsi a falon, hakan yasata fitowa duk da tasan bazai wuce Ashraf bane, amma bata saniba ko yana buqatar wani abunne.

Tana fitowa taga giftawar mutum alamar yagama abinda yakawoshi yayi komawarsa, murmuahi kawai tai aranta fad'i take" ka godewa Allah ya Ashraf dana tashi daga Dijeta ta asali wllh da duk abinnan dakakemin saina rama bazan qyalekaba"

Sai da ta had'a komi sannan ta fito falon, nan ta zauna ta karya kamar ance kalli table din dake tsakiyar falon, nan tahango wata farar takarda tare da waya, jitai kawai tanason sanin komiya aciki hakan yasata d'auka tare da bud'e wa.

" ki d'au waya zakuyi magana da mom" haka kawai taga ansa ajiki, shirutai tana nazarin takardar tana haka taji wayar naqara

A hankali ta danna wajen amsawa, tana karawa taji mom nacewa" wato son bazaka kaimata wayarba ko, ranka zai 'baci fa wllh"

Murmushi tai kan tace" mom nice fa"

Mom itama tai murmushi kan tace" d'iyata, kina lfiya?"

Dije ta sunkuya kamar tana gabanta tare da fad'in " lafiya lau mom antashi lafiya"

Mom tace" lafiya lau, ya kad'aici?"

Dije tace" Allah mom gidan ba dad'i ni kad'ai ba kowa sai na zauna naita tagumi kawai, dan Allah kice da auta ta dawo nan dazama"

Mom tace" ayya sorry d'iyata, ai daman haka auren yake, zaki sabani, yanzu dai inaso kishirya nan da qarfe goma Imran zaizo ya d'aukeki zaki fara zuwa school na koyan girki, sannan kada kisa wasa aranki duk abinda za'a miki ki koya da kyau, daughter banda hulda da maza kisani ke matar aure ce, kinji ko ki kuma iya ruqe sirrinku keda mijinki kada kije ki bud'e baki ki tazuba, duk danasan ke bazakiyiba amma ki kiyaye kinji ko"

Cikin farin ciki da jin dad'i ta amsa da" insha Allahu mom bazan taba baki kunyaba, tabbas ke iwa tagarice kinmin abinda ba kowacce uwace zataiwa 'ya'yantaba kinmin gata, bansan dad'in uwaba amma ayau nasan irin gatan da masu uwa araye keji, nagode mom Allah yasa aljannace makomarki" ta qarasa tare da share hawayen da suka sakkomata kan kumatunta.

Mom kwa cikin farin ciki da tsabar jin dad'in kalaman dije tace" ameen 'yata ki kula sosaifa"

Dije ta amsa da " tam mom" daganan mom tayanke kiran.koda tagama ajjiye wayar tai tare da haurawa saman biri ta samu sannan ta sakko kamar yadda yamata rubutu a peper itama haka tamai, sannan ta koma dan shiryawa kada ya Imran d'in yazo bata shiryaba.

Asraf saida yagama shirinsa nafita sannan yasakko, inda ya ajjiyemata wayar nan ya kalla, nan yatarar da wayar awajen da kuma takardar, aransa yace" bata ganiba komi?"

Wayar ya d'auka tare da takardar, saidai ga mamakinsa sai ganin rubutu yai ajikin pepar "nagama" haka kawai yaga an rubuta. Murmushi yai kawai dining ya qarasa kamar kullum dai hakan yaga ta ajjiyemai abin karin, yau sai yaji abincin qamshinsa yamai dadi, amma baijin zai iya ci hakan yasa ya fita daga falon.

Tana zaune bakin gado tana tufka da warwararta ita d'aya taji qarar motarsa hakan yasa ta miqe, riga da siket ne na wani material ajinkinta dinki ya amsheta sosai dayake dijen tamu badai banzaba.

Kaitsaye gate din ta wuce nan ta bud'e mai qofar, shikam tunda ya fito yake binta da kallo kayan sunmata kyau sosai zai cema baitaba ganinta cikin shigar data haskata irin wannanba, amma abinka da mai baqin eh yane sai kawai ya kauda idanunsa gareta tare dajan tsaki, hakan yasashi bawa mitar tasa wuta ya fice daga gidan.

Itakam yana fita ta sauke ajjiyar zuciya tare da furta" Allah dai yarabani dakai lafiya muhu kawai" nan takoma ciki abinta.

Imran kuwa goma dai-dai ya iso gidan, koda yazo yayi mamakin ganin ba mai gadi dan dije ce ta bud'e mai gate d'in. Dayake tunda suka tare baizoba shiyasa baisan ba mai gadi ba.

Koda suka gaisa fad'a yashiga yi mata" akan ai bude gate banata bane sai haqarqarinta suyi sanyi koba komi jikinta zai gayamata ai, nan yake tambayarta ina maigadin?"

Dije ta sauke ajjiyar zuciya tare da sakin murmushi kan tace" ai ba asamu mai gadin bane, kuma yaya banajin komi wllh na kwana nawa ne dan d'azu munyi magana dashi yace yabada cigiya"

Itman yace" dadai yafi hakan, amma bawata matsala ko?"

Dije tace" babu komi yayana muna lafiya"

Imran yace" masha Allah hk akeso, muje ko"

Nan suka fice daga gidan. Yayinda kai tsaye suka wuce inda zasu.

Koda suka qarasa sosai yabawa yarinyar amanar Dijen nanfa tamai alqawarin bata kulawa ta musamman insha Allahu.kallonshi tai tace" Imran ina kasami the most beautiful haka"

Dariya yai kan yace" kai hasfy kina da abin dariya, qanwatace da gaske tana da kyau"

Murmushi tai kana tace" masha Allah, sosai ma aikai bazaka ganiba amma mu da mukasan abu mai kyau muzamu gayama"

Imran yai murmushi akaro na biyu kan yace" lallai kam gaskiya ne, yanzu ai koyamata duk abinda yadace"

Hafsy tace" baka da matsala" nan yaiwa dije sallama tare da yimata nasiha sosai, dakuma bata shawarar tsayawa tayi abinda yakawota.

Koda suka ke'be da Hafsy roqarta yai akan ta tsaya sosai akanta ta koyamata duk abinda ya dace, dan ita din matar aurece kuma yanaso takoyi abubuwa da yawa sabida yanaso ta burge mijin nata, nan yagayamata yadda auren yake, shi kuma yanaso yaga yadda Ashraf zai juyi zuwa gareta"

Hafsy kam alqawari tamai akan insha Allahu zatayi mata duk abinda yadace, nan suka rabu.

Koda ta koma wajenta saida suka sakya gaisawa nan tashiga janta da hira duk da cewa Dijen ta kasa sakin jikinta, amma tasan bada dad'ewa zata saka, kuma insha Allahu sai ta gogar da ita fiye da yadda Imran d'in zaiyi tsammani, dan tayi alqawari zata koyamata abubuwa da dama bama girki kad'ai ba.

Nan ta umarceta akan ta dora wata riga akan kayan nata dan zasu shiga kitchen, zasuyi girki akan abimcin safe inda zata koyamata qosan dankalin turawa*

Kayan had'i:
*Dankalin turawa
*Fulawa
*Yeast
*Attaruhu
*Albasa
*gishiri da kuma

Yadda zakiyi.

   Zaki dafa dankalinki yadahu saiki ajjiyeshi gefe, ammafa bayan kin ferayeshi. Saiki sami fulawa ki kwabata da yeast kiyi kwabin kamar zakiyi fanke kisa arana tatashi.

Saiki zuba kwai(dafaffe) da dankalin turawa daman already kin rigada kin jajjaga attaruhu da albasa saiki zuba aciki, saiki zuba gishiri da maggi kad'an ba aso gishirin yai yawa.

Sai kizuba mai akwaskwon suya kisa albasa ki soya idan yai zafi saiki dinga diba da cokali kinasawa aman kamar kina soya qosai.idan yai ja saiki kwashe.

Ta nunfasa bayan da suka gama kana tace yanzu zamuyi *kunun kwakwa*

Kayan had'i:
*Gyad'a niqaqqiya ko markad'addiya.
*Kwakwa
*Sugar
*Gasara ta koko ko kunu

Yadda zakiyi.

   Zaki sami kwakwarki ki cire 'bawon da baqin dake jikinta saiki gogata agreater.
Saiki d'akko gyad'arki kisa mata ruwa yadda zai isheki sanwa ki dora awuta ki barshi yai ta dahuwa.

Saiki sami bokitinki wanda zaki dama kunun aciki kisa gasararki ki damata da ruwa kad'an.idan ruwan gyad'ar yadan qone saiki sheqa akan gasarar taki.kada ki bari yai guda guda.

Saiki sa kwakwar aciki da sugar kisha abinki, zaki iya had'a wa da qosan dankalin da mukai, 'yar uwa ki gwada da dad'i sosai.

Dije ta sauke ajjiyar zuciya kan tace" cab wannan girki haka, gaskiya Allah yabaki baiwa aunty hafsa"

Hafsy tai dariya kan tace" a'a kada kisakya kirana da aunty dan ni ba auntyn ki bace, sannan indai kala-kalar girkine har saikin gaji dasu, yanzu dai kinga yadda mukai komi ko, to haka zakiyi in kintashi yi, sannan in kin koma inaso kiyimin ki taho dashi gobe in Allah yakaimu"

Dije tace" insha Allah nagode sosai da qaruwar da zanyi dake"

Hafsy tace" bakomi ai yiwa kaine, muatane nawa nake koyawa balle ki qanwar Imran, Imran yana da kirki sanda na taba wata rashin lafiya aka rasa jinin da za'asan shiyaban, ke har jini yana badawa kyauta ga asibiti, shiyasa zan iya komi indai dan yaji dad'i ya kuma sashi fatin ciki"

Dije tace" hakane Allah ya biyaku da alkhairi"

Hafsy tace "ameen, fatana kitsaya ki koyi abubuwa da yawa "

Dije tace" insha Allahu , bazan baku kunyaba"


Editing is not allow....

Vote,
Comment,
Share and Like.....

*Mrs.Abduul ce*

Continue Reading

You'll Also Like

115K 11.7K 121
"မှားယွင်းသော လက်ထပ်ခြင်းမှသည်.....ကောင်းမွန်သော အိမ်ထောင်သည်ဘဝဆီသို့...(၁)" ***MM Translation (Just for fun) "မွားယြင္းေသာ လက္ထပ္ျခင္းမွသည္.....ေကာင...
109K 9.4K 70
ဘာသာပြန်သူ - စွဲညို့အသင်း ရွှီမိသားစုရဲ့ တိသမီးက လက်ထပ်ပြီးတော့ ယန်ကျင်းကို ရောက်လာပါတယ်။ သုံးနှစ်ကြာပြီးနောက်မှာ သူ့ယောက်ျားက အောင်မြင်တဲ့ စာသင်သား...
1.2M 80.5K 114
Cover- edited from google Start Date -22.4.22 End Date- 22.3.23 အနံ့သင်းတဲ့ သဇင်မင်းကမှ ပန်းထင်သလား မထင်ပါနဲ့ အဲလိုမထင်ပါနဲ့ အနံ့မဖက်တဲ့ သပြေခက်ကလဲ...