BIYAYYAH

By maryamad856

41.8K 1.9K 467

Labari ne akan wasu masoya guda biyu da suka had'u wajen yiwa iyayensu BIYAYYA. 'Kir'kirarran labari ne b... More

BIYAYYAH
BIYAYYAH
BIYAYYAH....
BIYAYYAH...
BIYAYYAH...
BIYAYYAH....
BIYAYYAH.....
BIYAYYAH....
BIYAYYAH....
BIYAYYAH......
Biyayyah......
biyayyah.......!
biyayyah.....!
biyayyah.....!
biyayyah....!
biyayyah....!
Biyayyah....!
Biyayyah.....!
Biyayyah.....!
Biyayyah....!
biyayyah.....!
biyayyah....! 59-60
Biyayya....61-62
biyayya....62-63
biyayya.... 65-66
part.....67
biyayy.....68
biyayy....69
biyayy....70
biyayya......
biyayya.....
biyayya....73
biyayya......73
biyayya.....74
biyayy......75
biyayya......76
biyayya....77
biyayya.....78
biyayya.....79
biyayya.....80
biyayya....81
biyayya.....82
Last page....83
Appology/Biyayya....12-14

BIYAYYAH......

1.1K 46 0
By maryamad856

           *BIYAYYAH*


   Story ....Writing by

  *Maryam abdul'aziz*
       (Maryam Abdoul)

Wattpad @Maryamad856




*page....25-26*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*


---------Cikin zafin rai kawu yace " kinji ai irin abinda nake gudu ko Iya, sabida tsabar shashanci da iskanci irin na yarinyar nan mutake gayawa haka, na tabbata da babanta yana da rai ko shi kika shinfid'awa kara bai isa ya tsallakeba, amma gashi  tana Neman ta bamu kunya. Kisani wannan kunyar dazaki bamu, bamu kad'ai bane aciki harda *mahaifinki* da baya da rai, ko kinaso ace ahlinku basu da cika alqawari, kisani mahaifinki da yana Raye sai yafi kowa murna da farin ciki domin harda da hannunsa acikin lamrin nan"

Iya ta kalleta tace " haba 'Yar albarka kada ki bamu kunya mana kinji"

Dije ta kalleta cike da sanyin jiki, duk abinda za asa da babanta to tabbas tana ganin girmansa kuma zatai hakanne Dan *MAHAIFINTA* amma ba Dan komi ba, kuma zata kare Martabar gidansu  da ahlinta. Kallonsu tai tace " kawu, Iya kuyi ha'kuri da abinda na muku a yanzu, nayarda na amince zan aure za'bin da kukayimin. nayarda zanyi *BIYAYYAH* agareku."
Cikin farin ciki Kawu yace " mun gode d'iyar albarka, Allah yayi miki albarka, yanzu ga kud'inki nan na Nagani inaso"

Ta kalle kud'in ta dube kawun Nata tace " kawu ni ba abinda zanyi dash, duk wani Abu da za'aban to mallakin June, kiyi duk abinda yake dai-dai agareni"

"Allah ya miki albarka, tashi kike" Kawu ya fad'a. Nan suka cigaba da tattaunawa kan lamuran. daga bisani yaiwa Iya sallama tare da ajjiyemata kud'in.

Dije kam koda tashiga d'akinta zama tai akan katifarta tare da shimfid'a kyakkyawan tagumi akan kumatunta.tunani kawai take yadda zata tafi tabar 'kauyensu, tabar Iyanta ita kad'ai, wannan shine gatan da ake mata a rabata da kowa Nata, akaita ahlin da bata san suba.

Iyace tashigo d'akin amma Sam Dije bata ki shigowarta ba domin ta fad'a duniyar tunani.  dafata tai tace "ya akayi d'iyar arzi'ki"

Firgigit ta farka tare da kallon Iyan tace " Iya banason na tafi na barki, banason na tafi nabar 'kauyenmu"

   Iya ta tallafota kan kafad'arta tace " kiyi ha'kuri kinji haka rayuwar aure take, kuma nasan duk indai zaki zakiji fad'in zama dash sosai, suna matu'kar sanki jikalleta".

Gyad'a mata kai kawai tai, tare da zamewa ta kwanta kan cinyarta.




---------- Imran ne zaune yana game a wayarsa, sallamar da Ashraf yaine yasa shi kallonsa tare da amsa masa sallamar.waje yasamu yazauna batare da ya cemasa kanzil ba, shima ganin hakan yasa yai banza dashi, Dan yasan ko maganar duniya zai mai indai bai ga Damar mai da martaniba to bazai kulashiba.tsawon minti goma suna zaune a haka cike da mazewa Ashraf yace " kai baka San mutane sun shigo bane, Dan iskanci kana wata shegiyar game"

Kallonshi Imran yai yace " naga ikon Allah yau, nakeji bakai kazo ka tadda niba a zaune, kuma har gidanmu?"

Ashraf yai 'kwafa yace " lallai yaron nan ka raina ni da yawa, to yimin gori Nidai bamu da gidan, sannan ko banza ai na girmeka, taya wa zai fara yiwa 'kani magana salon ya rainashi" ya 'karashe yana wani kun'bure-kun'bure.

Imran yai dariya yace " ah lallai naga Alama, aikam saidai ai tazama a haka, gidan kan waya sani ko babu, ni shiyasa ma wllh na matsu dad ya aurar dakai ko kadaina biye-biyen gidajen mutane" ya 'karashe cike da dariyar tsokana.

Ashraf ya kalleshi tare da cillamai wata uwar harara yace " mai zai hana kai ka wassheshi.Mits" ya 'karashe da tsaki.

Har Imran ya bud'e baki zai magana ya katse shi da fad'in " kaga malam d'an le'ka ka kar'bo mana abinci yinwa na keji, kuma ban San komawa gida yanzu"

Imran ya 'kyal'kyale da dariya yace " ah kace yinwa ce ta koro ka, to wllh ba inda zani kaje da 'kafarka" yana 'karasawa yacigaba da game d'insa a wata.

Ganin da gasken bazai kar'bo mishiba yasa shi mi'kewa tare da fizge wayar dake hannun Imran ya fice daga d'akin nasa.

Imran yai murmushi yace " kai kasanta, duk tsiya dole wayata ta dawo hannuna dai".

Koda Ashraf ya sauka main falo d'in bai tadda mom ba, hakan yasa shi haurawa samanta, tare da 'kwan'kwasa'kofar, sannan tace "ya shigo". cike da sallama ya shiga.

Kallonshi tai tace " ah my son saukar yaushe?"

"yanzu nazo mom, amma na d'an haura saman Imran"

" OK, yasu mom d'in da sauran mutanen gidan?"

"Duk suna lafiya, suna a gaisheku"

" masha Allah, muna amsawa" ta 'karasa cike da murmushi.

Kallon ta yai yace " mom Allah yasa da akwai abinci, ina son ci"

Mom tace " da akwai, kuma best food naka wato tuwon shinkafa miyar agushi"

Dariya yai yace " kai amma mom naji dad'i, na gode"

" bakomi, muje na zubama ko?"

Nan suka sauka 'kasa, Imran yana zaune yana jiran yasakko ya bashi wayarsa, dan yana da abinda zaiyi da ita. Shikam Ashraf ko kallon indai yake baiyiba direct kan dinning ya nufa.cikin sauri Imran ya 'karasa ya janye kujerar tare da fad'in " wllh bazaka ci abin cin nan ba sai ka bani wayata"

Kallonshi yai tare da murmushi yace " in banason wata kajira magana"

Imran yace " to muzuba mugani dani dakai wazai ci riba"

Mom ta kallesu tace " yawwa halin ne zai motsa ko?"

Imran yai caraf yace " kawai mom Dan nace bazan kar'bo mai abinci ba, sai ya 'kwacen waya, Allah bazai Ciba sai ya bani"

Mom tai murmushi tace " to ai Ku ba a iya muku, mutum yashiga fad'in kuma yaji kunya, amma dai yanzu kai Imran kai ha'kuri ya gama cin abin cin man"

Zun'boro baki yai yace " haba mom, ai daman nasani, indai dashi shi zaki goyawa baya, haba Dan Allah"

Mom ta kalle Ashraf tace " my son kaga Kaine babba , ka ci girma ka bashi kaji."

Jin an anbaci girma yasa kan Ashraf ya dad'a fasowa, kallon Imran yai yace " d'auke a kwalar wayar ka, yaro" ya 'karasa tare da dire mai ita a kan dinning d'in.

Imran yai 'kwafa yace " wllh ido ba muduba yasan 'kima, itama mom d'in ai tasan ba haka bane, ko a fuska ansan nini babba kai kuma yaro, aljanin kawai"

Cikin zafin nama Ashraf ya mi'ke yace " ni kake cewa aljani, wllh yai sai nayi maganinka, tsohon banza kawai"

Shima Imran cikin zafin nama ya haura sama tare da fad'in " bisimillah man aljani" ya tura 'kofar tare da d'aga murya yace " ka gaida Dije nasan can zaka, shi yasa kace bazaka gidan ba yanzu"

Ashraf yai 'kwafa yace " zan kama Kane, ai zaka sakko, ba kwana zakai a nan ba dai"

Itakam mom abinmaa kallon ya zamemata kamar wacce ta sami cartoons. dafa kafad'ar Ashraf tai tace " calm down my son, rabu dashi, zai sakko yasaman ai, maza ci abincin ka"

Bashi yabar gidansu Imran ba sai wajen magrib.


----------Turo baki tai tace "wllh Sam Jummai banajin dad'in tafiyar da zanyi nabar Iya ita kad'ai, nasan zata rasa kulawa sosai, inajin haushin auren nan da za'ayimin, na kar'be shine badan komiba sai Dan *MAHAIFINA* zan cika mishi burinshi kamar yadda kawu ya fad'a, zansa yai farin cike dani kamar yana raye"

Jummai tai murmushi tace " yo in banda abinki ai abinda zasu miki shine gata, kin manta kullum mama tana cewa aure a wajen 'ya mace shine gatanta da rufin asiri, kuma daman can Iyan ta yata wasu ayyukan kike, kullum kina zaune kamar jaririya, ni gwara kiyi auren ko ta samu hutun jarabarki"

" Kut mey lesy...wato ni cema jaraba ko, wllh Jummai ki fita hancina tun kan na fatoki, ni daman tsiyata dake bakya abin arzi'ki, aikin banza"

Jummai tai murmushi tace " haba 'kawalliya roman dad'i, maida wu'kar bani nakai zomanba rataya aka bani, amma kiyi ha'kuri kinji"

" ke kika sanshi, daman ai haka kike, da an fara magana sai ki fara bada wannan shegen ha'kurin naki, kina wani karyar da kai, to naji" Dije ta fad'a.

" yawwa ko kefa, ta d'an birni" Jummai ta fad'a cike da tsokana.

Habawa, daman su Dije a kusa tuni tayo kan Jummai da duka. habawa 'kafa mai nace ban baki ba, tuni Jummai tai wajen, itama Dije tamara mata baya tare da fad'in kitsaya man kiga abinda zai faru"

Dai-dai wajen wani mai saida gurasa suka tsaya, Jummai ta kalle Dije tace "wash amma fa wllh kin wahalar dani"

" ninace kiyi tsokanar" Dije ta fad'a kamar ba da ita dakai gudunba.

zama sukai daga gefan mai gurasar suka ci gaba da hirarsu, Jummai ce ta sunkuyar da kai tare da rad'awa Dije magana a kunne " Dije kinga Ramai an ji sau'ki har ta fara yyawo"

Dije ta girgiza kai tace " rabu da ita tai tayi ni sabgar gabana ta ishen" *nikam nace "oho su Dije ansan sabgar gaba"*

Jummai tace " ai shikkenan, kinga tashi mu wuce, ni nagaji da zama anan, kamar almajurai"

"wllh sai dai in kece almajurar, amma dai bani ba" ta 'karasa a hasale. Itadai Jummai bata ce uffanba. Dai-dai zasu wuce Dije tace " ah Ramai sannu har kin fara yawo, daga warkewa"

'Daga kai taibta kalle ta tace " kedai bari Dije, Sabgogi sunmin yawa, ga jama'a wasu sunce saina biyasu kud'ad'ensu, kinga duk na rame sabida aiki da nake na surfe"

" ayya Allah sarki Ramai sannu, amma wad'annan mutane ba tausayi, Allah ya shiryesu"

Ramai tace " hmm kedai bari...ameen 'Yar nan"

Nan ma Jummai ta tofa albarkacin bakinta kana suka wuce.koda sukai gaba Jummai ta kalle Dije tace " wllh taban tausayi kinga yadda ta'kare, sai naji dama bamu ta'ba mata kud'iba"

Dije tace "wllh nima taban tausayi, bakomi zamu maida mata da kud'inta amma ba yanzu ba, itama taji abinda akeji da dad'i ko ba dad'i"

Jummai tace " to sai yaushe, kedai zaki bar 'kauyen nan da wata guda"

" Mits! kefa wllh shashasha ce sam, ana maganar arzi'ki kina ta hauka" tana gama fad'a tai gaba, ganin hakan yasa itama Jumman binta.





..............Koda ya 'karasa gida, direct d'akinsa yanufa, yana Shiga ya fad'a toilet dan watsa ruwa. Wannan al'adar shice, indai ya fita ya jima a waje ya kwaso gajiya to yana dawowa zaiyi wanka, hakan har ya zame masa jiki, Dan wani zu'binma mom ca ta kemai "kwad'o"

Nan ya haye kan gado Dan hutawa, auta ce ta turo 'kofar tashigo tare da fad'in " yaya kazo inji dad"

Idon sa a lumshe yace " ba na hanaki shigomin d'aki ba sallama da Neman iziniba?"

" nayi yaya, baka jibane" ta fad'a .

" Da yake ni d'in kurmane ko?". Ya bata amsa a gajarce.

" a'a yaya sorry". Itama ta fad'a cikin sanyin murya.

" OK kije gani nan kaya zan canza" tana 'karasa jin zancen tai wajen tare da jamai 'kofar.

Saida ya sauya kayan sannan ya sakko 'Kazan. Zaune ya taddasu gaba d'ayansu wato mom da dad, sai kuma auta, waje ya samu yazauna a 'kasa yace " dad gani"

Dad ya kalleshi yace " yawwa Ashraf, d'azu naje 'kauyen matarka, kuma ban baro canba saida na bada kud'in Nagani inaso, sannan kuma an tsaida rana nan da wata guda, Dan haka inaso kaje ka fara shirye-shiryen bikin, in kuma baka da bu'kata to mu zamu yima, zamuyi duk abinda ya dace"

Tunda ya fara magana idonsa ke kan mom d'in shi, " kenan bata gayamai maganar da sukai ba, ina mom zata fad'a , to dad 'kin amincewa yai kenan, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wannan wace irin masiface haka, wace irin jarabtace haka?"

Dad ya kalleshi yace " yadai son kayi shiru?"

Kallon dad d'in yai yace " dad Dan Allah abar....."

Cikin zafin nama ya daga mai hannu tare da fad'in " wato Ashraf kanason ka nunan ban isa da kai ba ko, kayi duk abinda kake ganin shine dai-dai a rayuwar ka, to kaje kayi, tunda mu bamu isa dakai ba"

" ba haka bane dad, kayi ha'kuri, nayarda na kuma amince zanyi *BIYAYYAH* agareku, kune iyayena kuma kune za'bina, banda kowa saiku, Dan Allah ka gafar tamin, 'bata ma ran danai"

" bakomi, ya wuce, Allah yayi albarka" dad ya fad'a. Tare da fad'in " kaje ka RUBUTA duk abinda kakeso asaiwa matar taka, da kuma abinda kai kake bu'kata, sannan gobe kaje kaga gidan nan na gangare"

" dad na barwa mom komi, na bar mata wu'ka da nama, tasan duk abinda ya dace a zuba, kuma komi ta zuba dai-dai Ne, zanje Allah ya kaimu"

" to masha Allah, tashi kaje dama maganar kenan, Allah yayi albarka" dad ya fad'a, cikin farin ciki.

Shikam Ashraf zuciyar sace kawai take mai suka, yanaji kamar an da'ba mai wu'ka a 'kirji, yana jin wani Abu maras dad'i na yimai yawo, ya zaiyi da wannan 'kajagar da ake shirin 'kallabamai ita, tabbas sai tayi da nasanin amincewa datai dashi, lallai sai ya shayar da ita guba mai d'acin gaske.

Itakam mom tausayin d'an nata take ji. tabbas tasan bai San auren amma ita kanta ba yadda zatayi sabida komi zata ce dad bazai ta'ba sauya ra'ayinsaba, sannan shi Kansa Ashraf d'in yakamata ace yana da iyali, lallai ba zasu tsaya dakatata tasa ba, tsawon shekara biyu kenan dad na bashi dama, amma shisam yace har yanzu  baiga matar da zai aura ba, hakan yasa dad d'in yanke wannan hukuncin. to itawa, da zatace ya fasa, ina Sam bazai yiwuba, ita kanta tasan ko ayanzu tace yafito da wacce yakeso ca zaiyi babu.

*Miss Gentle Taku ce...*✍✍

Continue Reading

You'll Also Like

1.2M 80.4K 114
Cover- edited from google Start Date -22.4.22 End Date- 22.3.23 အနံ့သင်းတဲ့ သဇင်မင်းကမှ ပန်းထင်သလား မထင်ပါနဲ့ အဲလိုမထင်ပါနဲ့ အနံ့မဖက်တဲ့ သပြေခက်ကလဲ...
333K 43.7K 200
Book-6 I just translate this story. I don't own this story. All credits go to the original writer and English translator team. Profile picture goes c...
103K 13.6K 55
Back To The Countryside [ Myanmar Translation ] Author - 北冥魑 Original publisher - jjwxc Associated names - 归隐乡野 Status in COO - 96 Chapters + 2 Extr...