CAPTAIN MUZAMMIL

By Zeeneert

64.5K 4.7K 1.7K

The life of a Soldier More

PROLOGUE
The Story Of M&M
Page One
Page Two
Page Four
Page Three
Page Five
Page Six
Page Seven
Page Eight
Page Nine
Page Ten
Page Eleven
Page Twelve
Page Thirteen
Page Fourteen
Page Fifteen
Page Sixteen
Page Seventeen
Page Eighteen
Page Nineteen
Page Twenty
Page Twenty One
Page Twenty Two
Page Twenty Three
Page Twenty Four
Page Twenty Five
Page Twenty Six
Page Twenty Seven
Page Twenty Eight
Page Twenty Nine
Page Thirty
Page Thirty One
Page Thirty Two
Page Thirty Three
Page Thirty Four
Page Thirty Five
Not an Update
Page Thirty Six
Page Thirty Seven
Page Thirty Eight
EID MUBARAK πŸ’«
Regarding the poll
Regarding the Poll 2
Page Thirty Nine
Page Forty
Page Forty One
Page Forty Two
Page Forty Three
Page Forty Four
Page Forty Five
Page 46 and 47 merged
Page Forty Six and Seven
Page Forty Eight
Page Forty Nine
Page Fifty
Page Fifty One
Page Fifty Two
Page Fifty Three
Page Fifty Four
Page Fifty Five
Page Fifty Six
Page Fifty Seven
TIME FOR QUESTIONS
Page Fifty Eight
Page Fifty Nine
Page Sixty
Page Sixty One
Page Sixty Two
Page Sixty Three
Page Sixty Four
Page Sixty Five
Page Sixty Six
Page Sixty Seven
Page Sixty Nine
Page Seventy
Page Seventy One
Page Seventy Two

Page Sixty Eight

1.3K 69 52
By Zeeneert

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

*Zeeneert*@ wattpad

*Page Sixty Eight*

Cikin rada yace "Anya abunda ke zuciyar ki kenan Mami?are you sure your heart is clean and pure towards me?are you sure you're only angry because munsaba ma addini da values din society and we're at the verge of shiga hakkin Iman ko akwai wani abu daban?" Kukan da Mami keta kokarin rikewa tasaki a kirjinshi! Itakanta tasan she's just hiding her true feelings under a facade! Bakomai ne ke dawainiya da'ita ba face kishi dakuma ganin tana dab da rasashi!

Muzammil yasa hannu ya rungumeta sosai cikin jikinsa yanajin kowani sautin kukanta kamar ana watsamai ruwan dalma a jiki,ya lumshe idanu araunane yace "Stop decieving me and yourself Mami......I'm sorry I overheard your conversation with Abba the other day bankuma je da niyar invading privacy dinku ba.  Naje zanyi masa sallama akan washegari da sassafe zankoma Abuja kunnawa na suka jiyemin komai" yadagota daga jikinshi yana kallon cikin idanunta disappointedly yace "And innace miki I'm not disappointed nayi karya! Bakiyiwa zuciyata adalciba dakike tunanin taki zuciyar kadai ke dawainiya da soyayyata Mami. In a zamanin yarintarmu da farkon dawowana daga South Africa kinyi tunanin so na Yan uwan taka kawai nake miki zan iya yi miki uzuri but my later actions should have proved otherwise! Ashe Dan uwa na shiga damuwa in Yar uwar sa na fushi dashi akan laifin da baimasan dashiba? Ashe Dan uwa na iya driving for morethan 20hrs batareda ya hutaba sabida kawai yanaso yayi beating time ya riske Yar Uwarsa kafin tabar kasar suyi sallama? Ashe Dan uwa na turawa Yar uwar sa love messages day and night harna tsahon shekaru shidda?Ashe Dan Uwa na bibiyar rayuwar Yar uwar sa watching all her movements gabadaya rayuwarta? Ashe Dan Uwa na kishin Yar uwar sa dan wani namiji ya rabeta koya nuna interest akanta? Ashe Dan Uwa na iya sacrificing nasa happiness din sabida Yar uwarsa? Ashe Dan Uwa na iya batawa da kowa even if it means going against his family sabida kawai ya faranta ma Yar Uwarsa? Ashe Dan Uwa na iya ajiye ayyukan gabansa na tsahon kwanaki yatafi neman Yar Uwarsa dukda kuwa adalilin kin aurensa tagudu tabar gida?Ashe Dan Uwa na iya romancing Yar Uwarsa affectionately batareda yana sonta ba?Does that one night at Stockholm and the moment savored at the Car meant nothing to you?" Muzammil yakarashe maganar ayayinda ya tsareta da manyan idanunsa masu kama da zaiba dake cikeda abubuwan da ada take musu mummunan fahimta!

Yasauke numfashi ayayinda yakamo hannunta yasaka cikin nashi yacigaba

"Aiko makaho ya shafa yasan matsayin Mami azuciyar Muzammil!
Ameera bata taba zama barrier a soyayyar danake mikiba babu kuma wanda zai taba zama. I've loved you from day one! Nasoki tun nida ke bamusan inda kanmu yake ba! You were and will always be the woman I love" yace "Nasan zakice in hakane miyasa na yi rejecting dinki in the first place? The news came to me as a shock Mami...." sekuma yabata labarin tunanin dayakeyi ada dakuma yanda sukayi da Daddy da Ummi daya fada musu.

"Sabida haka bake kadai ke wahala ba"

Yakai hannunshi setin kirjinsa tana jin yanda zuciyar sa kekai kawo na wucin gadi yace "saurari yanda zuciyata ke bugu! Dauriya kawai na fiki Mami! I'm just trying to be strong for US! I'm just trying to make it easy for US anma wannan tada hankali da ramar da kikayi na kokarin ruguzaminsu. Wallahi da abune me sauki da tun aranar namaida Auren mu but then rainin wayau da wasa da hankalin iyayen zaiyi yawa. Ga uwa uba alkawarin danadaukarwa Chief of Army"

Mami tarasa shin farin cikin tagane Muzammil na Sonta zatayi ko bakin cikin abubuwan dataitayi abaya wanda shine silar halinda suke ciki ayanzu,cikin gunjin Kuka tace  "I'm sorry I ruined US.....I'm the reason for our destruction....!" Muzammil disagreeingly ayayinda yake girgiza mata kai yace " You did not ruin us and you were never the reason for our destruction Mami. Kaddarar mu ce tazo ahaka and we'll accept it gladly! Amma sede hakan bazai taba yuyuwa ba seda hadin kanki. You've to be strong like i'm trying too! Inaso kimaida komai ba Komai ba! Kisa aranki we were not meant for each other as husband and wife babu kuma alheri a tarayyar mu shiyasa komai yafaru! Kisa aranki Allah zai baki wanda yafini shiyasa ya hanaki ni for every disappointment is a blessing in disguise and you'll see how easier it'll be to accept this Destiny of ours...."

yadagota suna kallon idanun juna cikeda tausayin junansu danshi kanshi Muzammil din dauriya kawai yakeyi.  He know it's not going to be easy And like he said

"He's just trying to be strong for them..."

Yace

"Sannan inaso ki sani ko Muzammil be mallaki Mami amatsayin matar aurensa ba she'll always be his Soulmate and favourite cousin. As for my relationship with Iman abunda yafaru yau was nothing but ajizanci irin na dan Adam and Insha Allah hakan bazai sake faruwa ba! Our relationship will henceforth be clean and pure and so it'll never be the cause of anyone's pain.."
Ayanzu Mami bazata iya cigaba da sauraronsaba! Zuciyarta bazata iya cigaba da juran wannan al'amarin ba! She's not as strong as he claims to be danhaka tafice a motar dasauri sautin kukan ta na karuwa............

Zaiyi yunkurin tsaida ta idanunshi suka sauka kan wani dan karamin box akan seat dinda tatashi,daukowa yayi ya bude and seeing a Male designer expensive wrist watch yagane gift taso ta bashi. Ciro wrist watch din yayi daga box din yana kare masa kallo with mixed of emotions ayayinda yakoma ya jingina da headrest din motar yanajin sautin kukan Mami na taba kowani illahiri na jikinshi as she's drifting away,breaking every pieces of him! And it hurts even more inya tuna bashida wata hanyar yaye damuwarta after the little effort he just made. Wayarshine yashiga ruri and seeing Hanan ce ke kira sebe yi picking ba,yasan Iman ce tasa takirashi jin shiru bedawo ba. Koda ya tsinke ganin tanata sake kira sekawai yamata text cewa yana zuwa. Yayi scrolling contact dinshi yanemo number Ameera yay dialing. Ringing biyu tayi picking,atakaice yace

"Kifito compound kisameni ina jiranki" ko 5mins ba'ayi ba kuwa segata tafito tanata wurwurga idanu a harabar gidan waiko zata ganshi. Fitowa yayi a motar takaraso inda yake tace "Gani Hammah...." Muzammil yanuna mata bayan Mota yace "Small chops dinnan zaki shiga muku dashi keda sauran Yan Matan" yazagaya boot din motar yasauke kayan dasuka yo sayayya da Mami yace "Wannan kuma na Mami ne" Ameera curiosly tace "Dama kuna tare? We've been looking for her. Wayarta kuma tunda sukayi magana da Waleeda lokacin muna hanyar event center yadaina shiga" taleka front seat din motar wai kozata ga Mami aciki anma wayam danhaka tamaida dubanta ga Muzammil din tace "Where's she......?" ahankali Muzammil yace "Inside the House or may be around the compound" jin yanda yyi maganar yasa ta kura masa idanu tana nazarinsa,seyanzu talura gabadaya yayi wani iri and he's not acting like her lovely Brother when conversing....

Curiosly tace " Wani abun ya hada kune?" Ahankali Muzammil yace "Not really and it's a long story yanzu kuma ana jirana kibari daga baya zamuyi maganar" Ameera zatayi insisting ya katse ta ta hanyar cewa "Sa Hannu intayaki mukai kayannan varender ke kadai bazaki iyaba" adole tahakura tayi yanda yace harsuka gama tartare kayan. Zata fara diba takaisu ciki yatsaidata,pleadingly yace

"I know you're not her favourite person at the moment but please, take care of her, for me, Ameera." daganan bejira cewartaba yajuya yatafi.
Ameera batasan ya akayiba seji tayi hawaye suncika mata idanu,everyone might think Mami and Muzammil have moved on from each other anma ita tasani they still love and care for each other! Babu kuma wanda zai iya maye gurbin junansu a zukatansu.

Seda ta leka parlourn Waleedah ta tabbatar babu kowa sannan tadawo ta tattari kayan takai wani extra room dasu Waleedahn keda shi babu mai zama aciki ta kulle,tadebi small chops din takai can dakin da Yan Matan suke tace injisu Hammah and all this while tunaninta yanakan a ina Mami take?how's she? Bata kumayi gigin tambayar Yan Matan kosun ganta ba sabida bataso sukawo komai aransu.

Compound din gidan takoma tacan baya sanin halin Mami dason isolating kanta intana cikin damuwa,aikuwa a parking space ta same zaune ta bayan motocin dake parke ta cusakai cikin cinyarta tanata shesheka,Ameera wannan karan kasa rike nata hawayen tayi itama. Takarasa gefenta tazauna tajawota zuwa jikinta ta rungume tafashe da kukan itama.....And then gultiness dinda tayi shekara da shekaru tanaji yasake engulfing dinta lokaci guda. Tsakanin Ameera da Mami aka rasa me rarrashin wani! Seda sukayi kukan me isarsu sannan suka hakura dan karan kansu. Akarshe Ameera ganin dare yafara ratsawa taja hannun Mami suka shiga ciki,dakin datakai kayayyakin tajata suka shiga inda tashiga bandaki tawanke nata fuskar sannan tatafi dauko musu kayan bacci.

****

Muzammil nakomawa gidan Chief of Army yakira Hanan yasanar da ita yana waje. Ba'ajimaba sega Iman tafito sanye da zumbulelen hijabi da alamadai tacire wedding outfit din already. Koda ta karaso kamar gaske harda sake gaisheshi gakuma "Uncle Umar" dataketa kakaba mai dukwaidai yayarda batayinshi a aspect dinda iyayensu ke kokarin daurasu. Atakaice Muzammil ya amsa ayayinda tamai gesturing sukarasa garden din gidan kamar dazu.  Babu musu Muzammil yabita abaya harsuka isa garden din suka samu guri suka zauna. Iman ta tsareshi da idanu tana murmushi curiosly tace

"Is she the one?" Muzammil yagane watake nufi anma yayi kamar be gane ba yace "Who?" Iman tace "The one you return Home" Muzammil yadaga gira daya sama yace "Abunda kika kira kitambayeni kenan?" Girgizamai kai Iman tayi still smiling tace "zaka iya alakantashi da hakan. I just want us help each other dan naga kamar matsalar mu iri daya ce" strictly Muzammil yace "Count my problems out and tell me why you call me here" sauke numfashi Iman tayi tace "Shikenan....." kafin tafara bayani,tace  "Zanfara da baka hakuri akan threatening dinka danayi tayi a baya. Wallahi ba intention dinaba kenan rashin mafita ne yasani yin hakan anma segashi dukda hakanma ban samu yanda nakeso ba. I'm sure Abbu be sanar dakai dalilin hana aurena da Abba ba because from all indication you think Abba is a bad guy but believe me he's not. He's the nicest Guy you'd ever want to interact with. Shekaru hudu kenan muna tare. A makaranta muka hadu abroad. I went for my first degree while he was pursuing his Masters. We started with friendship daga baya alakarta rikide takoma soyayya. Acikin shekaru hudunnan akullum burin mu bewuce mu mallaki juna ba,kullum cikin planning yanda zamu tafiyar da rayuwar aurenmu muke. Dukwanda yasan Abbah yasanni hakanan dukwanda nake hulda dashi yasan wanene Abbah agareni,including our family members. Harta Abbu na yasanshi sautari yakanzo gida yamishi gaisuwa ta musamman koda kuwa bana gida ko kasar gabadaya. Everything was moving smoothly untill akazo batun neman aure Abbu yasa ayi bincike akansa da Familynsa ananne komai ya tabarbare. Abbu found out that mahaifiyar Abba first Cousin suke da Alhaji Auwal dasukayi plotting against him sukayi poisoning dinshi kwanaki" Iman tana kallon Muzammil araunane tace "For sure this's something to be worried about dankoni da Abba lokacin da abun ya faru we were deeply worried. Babu wanda zaiso familyn dayake kokarin hada alaka dasu abu irin haka yafaru but i don't think yakamata ace laifin Uncle din Abba ya shafemu! We're just pure souls in love! We have nothing to do with harkar siyasarsu!
I explained this to Abbu several times,sukansu familyn Abba sunzo sunmai bayani but he's being adamant,gani kawai yake Abba da Family dinshi have been using me to get to him tunda sunjima suna samun sabani da Alhaji Auwal matsalar batayau bace kawai shiyasa ya yanke alakar dake tsakaninmu ya raba ni dashi. Har raina inaso inyi mishi biyayya bawai dan na yarda da assumptions dinsa ba sedan shidin mahaifine a gareni ya isa yafada inji but I'm helpless Uncle Umar. Abba ba isasshen lafiya ne dashi ba! He have been suffering from heart tumor tun yana dan kankaninshi! Akullum likitoci gargadi suke kan aguji dukwani abu dazai bata mai rai sekuma gashi wannan abun yazo yafaru!yanzu haka yana kwance a gadon asibiti battling with his life...." Iman tafashe da kuka mai tsuma zuciya "I don't want to loose him bana kuma so inzama silar dazai sa iyayensa su rasa sa! He's their only child! Sunayi masa son da nikaina bazan iya misalta maka ba shiyasa nayi dukwani abu danayi abaya! Yanzu ma kuma bazan gajiya ba!" Tayi folding hannayenta guri guda still crying helplessly "Dan Allah Uncle Umar kataimakemu! You're my last hope and the only person I can rely on now! Nasan inkayiwa Abbu magana may be ya saurareka yayi reasoning akan lamarinnan afasa aurennan! Wallahi muddin Abba yasamu labarin an daura min aure da wani rasa rayuwar sa zaiyi! Kataimaka kayi mana rai ni dashi kayi convincing Abba afasa Auren nan! Imma kana kokwanto akan dukwani abu dana fada maka kamar Abbu na nimai iya baka details din komai akanshi da Family dinshi  kaje kayi bincike" tasake marairaice murya cikin rishin kuka "Nidai kawai kataimaka min kada ayi aurennan gobe" Muzammil sosai labarin Iman da Saurayinta Abba yataba zuciyar sa! yaji tausayin su Matuka because he know exactly how it feels to lose someone you love!Yaji inama yanada hanyar taimaka musu wurin cika burinsu! Yaji inama tun farkon hada aurensu tafada mai duka wannan ba threatening dinshi taitayi ba! He would have certainly helped her anma yanzu lokaci ya kure! Wama ya isa yafara tunkara da wannan maganar!?yace da Iman

"Innace labarin soyayyar ki da saurayinki be tabani ba nayi karya and how I wished I can give a helping hand but I'm helpless too! Nidin mai tarin laifine agurin family na! They have went through alot recently a dalilina bana kuma so wani abu kwatankwancin hakan yasake faruwa! Dama dakinsanar dani tun wuri danayi convincing mahaifin ki yajanye magana ta dake ya aura miki wanda kikeso tun zancen beje ko ina ba unfortunately you're late! Gobe daurin Auren mu Iman! Daga family na har naki babu wanda ba'asan da zaman su a kasarnan ba babu kuma inda labarin Auren mu bejeba! Manya manyan mutane masu martaba ne zasu halarci daurin Auren gobe wanda inada tabbaci dayawa daga cikinsu already suna gari wnda dayawa daga cikin su inada tabbacin ayyukan gabansu suka ajiye suka zo! Yau akace anfasa Auren nan sabida selfish interest dinmu aganinki munyi ma wadanda zasu halarci taron nan da iyayen mu adalci? One has to think out of the box Iman. Nasan koke kanki bazakiso ahalina da naki su tozarta a idon duniya ba! Akan batun saurayinki kuma inaso kisani Allah baya barin wani dan wani yaji dadi! Inkuma shidin mai tsahon raine lokacin shi beyiba sekiga Allah ya tashi kafadunshi. At times we want  something  so bad and it's not good for us baza kuma mutaba gane hakan ba sedaga baya. Kiyi hakuri kisama zuciyarki tawakkali and see how Allah will reward you for yiwa iyayenki biyayya" ya numfasa "i can't promise to be a perfect Husband for all humans are imperfect anma zanyi kokari inzama mai adali dasauke dukwani nauyinki daya rataya akaina. Nima kuma inamai baki hakuri akan abunda idanunki sukayi witnessing dazu tsakanina da kanwata. Wallahi bahaka nake ba! Ajizanci ne irin na dan Adam nakumayi miki alkawari insha Allah hakan bazata sake faruwa ba" yatashi tsaye daga zaunen  dayake yace "Da wannan nake miki saida safe! Senazo kaiki wurin event dinda zakuyi gobe....." yana kai aya baijira cewartaba yakama hanya yatafi yanajin yanda kukan ta keyi masa kuwwa aka! Aranshi yana ayyana

"Shikuma tashi rayuwar haka take? Making all Women cry because of him?daya na bakin cikin rasashi ayayinda daya ke takaicin samunsa?

****
Washegari akayi Mother's eve. Taro kuma yayi kyau babu laifi an kece raini! Mami batayi gigin yin abunda tayi jiya ba! Duk inda su Waleedah suka saka kafarsu tana biye dasu gakuma Ameera data makale mata keeping her company,janta da hira take sosai gabadaya tama hana ta yin wani tunanin. Tun tana shareta dan haryanzu bawani jituwa sukeyuba harta hakura ta kyaleta ganin Ameerar ko akwalarta batamasan tanayiba! Abangaren Muzammil dinma koda wasa benemeta ba yau harkokin gabanshi kawai yakeyi! He's trying as much possible as he can wurin ganin yacika alkawarin daya daukarma Iman da Mamin na tsayawa a lane dinsa dukda kuwa every piece of him,with every passing seconds Mamin yake bidaaa. He's trying to be strong from the outside anma aciki tunanin ta da komai nata ne ke yawo a kwanyarsa dahar yafara tunanin Soyayyar Mami bazata haukatasaba kuwa? Anya soyayyarta bazata zama sanadinsaba? He remembered preaching Iman akan kalaman data furta game da soyayyarta da saurayinta Abbah ashe shima he's not out of the equation! Lallai Bature yayi gaskiya dayace

"Easier said than done" shikuma bahaushe yayi sharhi akan zuciya

"Zuciya batada kashi.."

Friday yakama rana mai dumbin tarihi ga Familyn Tumbido da Chief of Army as they're marrying their first children off. Tunda gari ya waye kuma masu halartar daurin Auren da basu samu damar isowa jiyaba suka fara sauka,babu abunda kakeji agarin Abuja ranar face tashi dasaukan jirage! Inkaje airport kuwa jirage, private jets da helicopters kamar abun banza! Ga tight security tako ina! Harta sararin samaniya helicopters din sojoji yawo suke suna watching kowani movement acikin garin! Nigeria ba inda bedauka ba zancen Auren aketayi! Harkace ake ta manyan sojoji da Familyn Yan Kasuwan dasukayi fice a kasar baki daya! Abundai seson barka!

Su Ummi da Yan Matan tun sassafe suka koma Yola leaving only few of Muzammils Aunts dazasu jira bayan daurin aure sutaho da Amarya tareda angwaye. Karfe shabiyu da Yan mintuna Muzammil da abokanansa suka isa central mosque inda za'ayi daurin Auren bayan sallar Juma'a. Su Daddy babba,Abba babba,Daddy da Abba tuni suka samu isowa suma kowada tasa tawagar inda aka shiga gaishe gaishe kafin kuma lokacin huduba yayi aka fara.

***
Familyn Tumbido ya kacame biki ake ta ko ina. Kowa kagani yana farin ciki dawannan rana anma banda Mami. She's been trying to be strong anma abun yaci tura! with every passing second getting closer to time din daurin auren Muzammil damuwarta daduwa yakeyi! Ga Ameera dake dan debe mata kewar ma yau bata samu kanta ba sam! Gabadaya Yan Matan sunyi wanka sun cakare cikin ankon su sunata kwalliya amma ita batayi ko daya ba! She look so sad and lost! Dukwanda yamata kyakyawan kallo dole ma yasan akwai abunda ke damunta! Wannan dalilin yasa ta sulale tafice a gidan ma gabadaya batareda wani ya lura ba. Bata kuma zarce ko ina ba se sashin me sunanta (Hajiya Mami). A parlour tasameta tareda tsoffi kawayenta sunata yan hirarrakinsu duk sun shirya suma,dakyar Mami ta kakalo murmushi tagaidasu duka. Hajiya Mami tatambayeta dalilin dayasa bata shirya ba haryanzu inda tayi mata karyar kanta na ciwo ne,kodayake kan nata nadan sarawa kadan kadan. Tace tana so tadan kwanta tayi baccin kona awa dayane kilan tasamu kan yadena kuma sashinsu akwai hayaniya shiyasa tatahonan.

Hajiya Mami batareda takawo komai aranta ba worriedly tace "Kinsha magani ne?" Gyada matakai kawai Mami tayi ahankali. Hajiya Mami tace "Tokishiga daki na kikwanta babu kowa. Allah ubangiji yakara sauki" ciki ciki ta amsa da Amin din ayayinda ta wuce ciki and dukyanda taso baccin yadauketa kasawa tayi ga tunanin Muzammil da batun aurensa dake neman ya haukatata! Tabude wayarta ta kunna data waiko hakan zai taimaka wurin debe mata hankali ashe bata saniba wani rigimar ta rikitowa kanta. Daga whatsapp, Facebook,Twitter har Instagram dukdai maganar dayace!

"Auren LT. Umar Tumbido da yar gidan Chief of Army Iman"

Daga masu posting manya manyan yan siyasa da kasuwa dazasu halarci taron,yanda suka iso da tarbarsu da akayi,familyn Ango da amarya sekuma amarya da angon dakansu! Awani post Mami taga videon convoy din Muzammil da abokanan sa asanda suka tafi central mosque Abuja. 2nd slide kuma yanda suka isa central mosque din aka tarbeshi yashiga gaisawa da mutane! Ciki kuwa harda mataimakin shugaban kasa dasukayi musabaha ya rungume shi yana radamai magana a kunne. She couldn't get a better glimpse of him se awani post din data ga hoton shi shikadai! He looked extremely regal in his white bubaaa,shadda ce nagani nafada dayasha aiki da brown din zare. Kannan yasha rawani,daga kuma gefen fuskarsa kana iya hango sajen kanshi daya kwanta luf luf gwanin ban sha'awa! Kana ganinshi kaga jikakken Angon da hutu da jin dadin rayuwa ya zauna mai dukdama there's this sadness lying in his eyes da take da tabbacin ita kadai ke ganinsu takumasan ma'anarsu dankuwa aduka hotunan data gansa he's trying all he can to fake a laugh and smile!

Idanunta suka sauka kan wrist watch din dake hannunshi! Ko shakka babu this was the wrist watch she wanted to give him as a gift jiya ta manta a motarsa! Sekuma kalamansa na jiya suka shiga yimata yawo a kwanya and for the 2nd time taji tatsinci kanta a hali irinna jiya but this time even worser.....

Hawaye masu zafi suka shiga bin kuncinta sharshar! Kanta yacigaba da mugun sarawa zuciyarta nakara yi mata nauyi with every passing seconds! Kankace me kuma zazzabi me mugun zafi ya lullubeta! Babu inda baya karkarwa ajikinta batakuma san ya akayi tasaki wayar hannunta tafadiba. Dakyar ta iya putting strength taja katuwar bargon Hajiya Mami ta lullube jikinta bakidaya. Da halinda zuciyarta take ciki ayanzu dawanda take tunanin zata shiga anan gaba seeing Muzammil with another woman zatayi farin ciki ace Allah yakarbi ranta ayanzu! May be tahuta dawannan kaddara da jarabawar data ki ci taki cinyewa!

Karfe biyu da yan mintuna bayan an idar da sallar Juma'a aka daura Auren
IMAN AHMAD IBRAHIM da UMAR MUHAMMAD TUM.......

Abeg don't come for me😔out of love yasa naki karasa sunan wai kar in kunsa muku bakin cikin dayawa😂😂🏃‍♀️

Vote
Comment
Share

Continue Reading

You'll Also Like

Claiming Emilia By Daisy

General Fiction

417K 10.3K 55
Emilia Morelli's world shatters when she's told her mother has died. Left with no family, well at least none that she knows of, she's pulled into a s...
37.1K 5.9K 88
College cum work space story...enemies to lovers kind of story...
1.7M 44.3K 84
πŸ“Œα€€α€‡α€¬α€α€Ία€œα€™α€Ία€Έα€žα€Šα€Ία€…α€­α€α€Ία€€α€°α€Έα€šα€₯α€Ία€‡α€¬α€α€Ία€œα€™α€Ία€Έα€–α€Όα€…α€Ία€α€²α€·α€‘α€α€½α€€α€Ία€œα€€α€Ία€α€½α€±α€·α€˜α€α€”α€²α€·α€€α€½α€¬α€α€Όα€¬α€Έα€•α€«α€œα€­α€™α€Ία€·α€™α€šα€Ία‹ "α€™α€Ÿα€¬α€‘α€­α€―α€€α€Ία€α€”α€Ί+α€…α€±α€¬α€‘α€šα€Ία€’α€±α€Έ"
111K 15.1K 47
Book 2 in the Chauhan Family Saga - sequel to From Strangers to Siblings. Truth....... Everyone says the truth can't stay hidden forever. But no one...
Wattpad App - Unlock exclusive features