CAPTAIN MUZAMMIL

By Zeeneert

46.8K 4.3K 1.6K

The life of a Soldier More

PROLOGUE
The Story Of M&M
Page One
Page Two
Page Four
Page Three
Page Five
Page Six
Page Seven
Page Eight
Page Nine
Page Ten
Page Eleven
Page Twelve
Page Thirteen
Page Fourteen
Page Fifteen
Page Sixteen
Page Seventeen
Page Eighteen
Page Nineteen
Page Twenty
Page Twenty One
Page Twenty Two
Page Twenty Three
Page Twenty Four
Page Twenty Five
Page Twenty Six
Page Twenty Seven
Page Twenty Eight
Page Twenty Nine
Page Thirty
Page Thirty One
Page Thirty Two
Page Thirty Three
Page Thirty Four
Page Thirty Five
Not an Update
Page Thirty Six
Page Thirty Seven
Page Thirty Eight
EID MUBARAK 💫
Regarding the poll
Regarding the Poll 2
Page Thirty Nine
Page Forty
Page Forty One
Page Forty Two
Page Forty Three
Page Forty Four
Page Forty Five
Page 46 and 47 merged
Page Forty Six and Seven
Page Forty Eight
Page Forty Nine
Page Fifty
Page Fifty One
Page Fifty Two
Page Fifty Three
Page Fifty Four
Page Fifty Five
Page Fifty Six
Page Fifty Seven
TIME FOR QUESTIONS
Page Fifty Nine
Page Sixty
Page Sixty One
Page Sixty Two
Page Sixty Three
Page Sixty Four
Page Sixty Five
Page Sixty Six
Page Sixty Seven
Page Sixty Eight
Page Sixty Nine
Page Seventy

Page Fifty Eight

609 75 33
By Zeeneert

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

Zeeneert@wattpad

*Page Fifty Eight*

Sadiq besamu yayi magana da Ammi aranar ba sanin cewa sundebo gajiyar hanya suna bukatar hutu. Akuma daren sarkin musulmi ya tabbatar da ganin wata inda yakama washegari Sallah. Sallan nan na daban ne agurin su Mami kasancewar zasuyishi cikin Yan uwa dasukayi shekara da shekaru basuyi ba and the Family were so happy to receive them back too. Khalil da Khalipha ma sundawo daga makaranta tun shekaran jiya inda jirginsu yasauka a Yola,the Family is full. Amira ce kawai batanan sabida finals dazasu fara immediately after sallah yasa Daddy yace tayi hakuri tayi zamanta kawai intagama gabadaya seta taho. Se Muzammil dake can Ummara segobe zaidawo

Tun sassafe suka tashi aka gyare gidan tasss akasa Turaren wuta tako ina da daka shigo compound din gidan kamshin dazaifara welcoming dinka kenan. Wanka sukayi suka shirya kowa yayi kyau gwanin ban sha'awaa in his new Eid attire sannan suka tafi Eid ground. Daga abinci har snacks kuwa bayarwa Mummy da Ummi sukayi amusu. Ko kafinsu dawo har anyi delivering abincin acan side din Hajiya Mami dankuwa every Eid sukazo Yola acan ake haduwa aci abincin sallah. Nany Ngozi da Ajidde wata new housemaid din Ummi ne sukaje suka hadu a sashin Hajiya Mamin sukayi setting komai a katon Family dining dinsu. Abincine varieties na yan gayu babu kalan wanda babu haka ma snacks. Ga bottle and can juices kala kala jibge wasu a fridge wasu kuma awaje.

Koda suka taso daga Eid ground din can suka wuce direct inda akaci, akasha,akayi raha akakuma yiyyi hotuna. Harta Amira ba abarta abaya ba dan seda suka kirata video call taga ganimar datayi missing aka kumayi gaisuwar sallah. Muzammil ne kawai basusamu ba,sunkira wayarsa akashe. Aikuwa dukda haka seda Fa'iza tayi blessing inbox dinsa da hotuna da videos din duka abubuwan dasuka wakana. Basu suka watseba se azahar inda kowa yakoma sashinsu dan hutawa.

Ammi is trying in every possible way to be acting normal kamar batada wani damuwa and tahowarsu Yola has helped alot kasancewar koda yaushe tana cikin Jama'a. Ashir kuwa tuni tajefa komai nashi a kwandon shara. She deleted his pictures,their chatss and every single thing regarding him,tayi blocking dinshi ta ko ina kafin daga karshe ta goge digits dinsa even though it's inscribed on her heart kamar yanda haryanzu soyayyarsa ke dawainiya da'ita.

Sadiq kuwa haryau takasa kiranshi suyi reconciling kamar yanda tayima kanta da Mami alkawari,wani irin tsananin kunyar sa da nauyinsa takeji yanzu. Sautari setayi yunkurin kira seta fasa dan batamasan ta ina zata fara conversation dinba. Aikuwa dan halak din sega kiransa yashigo wayarta. Wani irin wara idanu Ammi tayi hankali tashe ayayinda ta kifa wayar kan gado haryagama ringing bata dagaba. Ba ajima ba sega wani call din yasake shigowa. Wannan karan silencing wayar kawai tayi dan dukyanda taso tayi mastering courage tadaga kasawa tayi. Seda yamata missed calls kusan biyar sannan ya hakura.

Da yanma ma yasake kira shiru bata iya dagawa ba.

Sekawai yayi deciding yace Mami tahadasu. Aikuwa dadare bayan sungama shan hirar su irinta masoya yace tahada shi da Ammi. Mami kamar gaske curiosly tace "Waini shiri akafara da Ammin ne banida labari?" Dan ko jiya dadare dasuke waya yatambayeta ko Ammi tafada mata wani abu anma tanuna mai batasan komaiba

Cikin sigar zolaya Sadiq yace "ina ruwanki? Kuma damacan ce miki mukayi bamwa shiri?" Mami tayi dariya tace "Oh hakane abun? Niza ayiwa danwaken zagaye?" Sadiq dake dariyar shima yace "Eh din bakin zabi kigoyi bayan Kaninkiba? Tonima se a barni inshigar ma Kanwata" Mami tace "Toh Allah yasa kar Kanwar taka tabaka kunya kuma intayi tsamidai zamuji" Sadiq na dariya yace "Ba abunda zaiyi tsami insha Allahu. Nidai yanzu hadani da'ita muyi magana" Mami dake kwance kan gadon Mummy tashi tayi tafice a dakin zuwa dakinsu. Ammi dake kwance tareda Naaana suna sana'ar kallon cartoon kawai seji tayi Mami  tasaka mata waya a kunne. Da mamaki Ammi tacire wayar a kunne in a whispher tana tambayarta wayene anma bata samu amsarba sema cewa da Mamin tayi inta gama wayar tabama Naana wayar tamaido mata tana dakin Mummy.

Maganar data ji Sadiq nayine yasata maida wayar kunne adole,yace "Ammi are you there....?" akunyace Ammi tace "Uhhm" Sadiq yace "Shikenan kuma haka zamuyi dake Aunty Ammi? Laifin wani seya shafi wani duk kinbi kin rikitamin Kani inata kiranki bakya picking?" Ammi tace "Anma ai tunda can dama bana daga wayarka" Sadiq yayi murmushi yace "Eh amma ai kina daga na Ashir? Yanzu dakika gano Kanina ne bakin jinina ya shafeshi kika zubashi a kwandon shara shima" Ammi dai kunya kamar ta nutse cikin kasa,kai kace agabansa take,tace "Ni wallahi bahaka nake nufiba Yaya Sadiq" Sadiq dariya kamar yayi yaya anma ya gimtse abunsa aciki. Wai yau shi Ammi ke kira da "Yaya"? Lallai dare daya Allah kanyi bature kuma hausawa suka ce inda rai da rabo, yace "Toh menene?" Ammi tace "Kunya nakeji" Sadiq yana murmushi yace "Dama akwai kunya tsakanin Yaya da kanwa ne if you really meant what you just addressed me with?Kuma kunyarma ta mecece? As far as I'm concerned baki taba min wani abunda zaisa kiji kunyata ba ni Ammi. Kodai surukantar ne akeso afara dani tun yanzu?"  Sadiq yakarashe maganar cikin sigar zolaya.

Ammi kamar zatayi kuka tace "Dan Allah kabari kanasake sani jin kunyarka Yaya Sadiq. Ainasan kagane abunda nake nufi" and this time Sadiq couldn't hold his laughter,yarinyar bazata daina amusing dinshi ba,yace "Okay fine....nayarda nagane mekike nufi. Kinajin kunyata ne sabida kiyayyar da rasar kunyar dakikayita min abaya and now i turned out to be the Brother to your Boyfriend but then abunda baki saniba shine bantaba kullatan ki ko inji haushin abunda kikaminba because everyone is entitled to his own opinion sannan ba asaka mutum yaso wani dole. It's absolutely normal for you to dislike me and to be honest with you bankiraki dan muyi reconciling akan issue dinnan ba but rather to beg you karkibari abunda ke tsakaninmu ya shafi alakarki da Ashir sekuma wata magana mai mahimmanci danakeso muyi" Ammi tace "Still I'm sorry for all my actions towards you and not because I want to reconcile with Ashir too sedan nagane kuskurena. Asali bawai na tsaneka haka kawai baneba. I was only against you base on a fact da banida masaniyar bashine mafi alheri ga Yar uwatabama seda ta nusar dani. Kayi hakuri kayafemin insha ALLAH from now on I'll see you and accept you for who you're not base on my silly reasons da basuda madafa" Sadiq yace "Babu komai and I'm glad you're finally seeing me this way. Nikuma namiki alkawari bazaki taba dana sanin yin hakan ba" seyanzu Ammi ta'iya sakin murmushi,tace "Nagode" Sadiq yace "Now back to the important topic: MY BROTHER ASHIR"  Ammi ta girgizakai kamar tana gaban Sadiq dinne tace "Dan Allah kabar maganarshinnan kawai Yaya Sadiq" Sadiq yasaki murmushi yace "Inkikace nayi haka kenan haryanzu komai bewuceba agurinki" Ammi tace "A'a Wallahi bahaka bane" Sadiq yace "then let me speak...." haka babu yanda ta'iya dole tahau sauraronshi,yace

"Ammi realizing you're my Brother's  girlfriend bansaniba farin ciki zantaya ki ne ko akasin haka?Ashir is a nice guy,yanada halin kirki, yanada addini, ya iya zama da mutane ga iya neman nakai. He's so dawn to earth but at thesame time bazan boye miki ba yanada wani hali da ba lallai ki iya putting up to it ba inkukayi aure. Ashir yanada neman Mata. Nooo....not in the sense that yana Zina,zan iya rantse miki ko kama hannun mace bana tunanin yatabayi. He's just a flirt. Tara Yan mata yake babu gaira babu dalili which is so out of his class.  I've never see him so serious about a girl se akanki. Ranar dakuka sake samun contact with each other ya sallami duka Yan matansa,he introduces you to all our family members inaga dani kadai ne baihadamu mun gaisa ba kuma shidinma nine naqi,I thought da useless girlfriends dinsa yakeso yahadani mugaisa ashe bahaka bane which is so unlike him. Do you know that because of how you reacted ranarda mukazo da kin daga wayarsa dakikayitayi nima kuma naki insa baki a al'amarin gabadaya yadauka Kinga no halinsane seeing us together muna dawowa gida yakwanta rashin lafiya harsai da aka hada dasu allurai da karamai ruwa? Yanzu haka danake miki magana bai gama warwarewa completely ba but can we still trust him base on this? Maza irin Ashir in sunason abu babu irin lane dinda bazasujeba tareda daukan alkawarurrukan da dazaran sunsamu abunda sukeso din kuma se akoma gidan jiya so we're reforming him, I'm reforming him, He's ready to reform himself for you Ammi.... I had a heart to heart conversation with him yesterday. Nayimai alkawari indai har yacanza hali nan da shekara daya zuwa biyu na tabbatar yafita harkar wasa da hankalin Mata nikuma zanshigemai gaba wurin shawokanki muzo anema masa aurenki so here I am Ammi....

Will you endeavour to wait for my Brother dukdama banida tabbacin after hearing all this about him you're still into it ?" Without a second thought Ammi tace "We all are not perfect Yaya Sadiq. Kowa yanada nashi flaws din and This's him sannan tunda ya dauki alkawarin gyara kansa sabida ni then I've no reason to back out. Innayi masa haka banyiwa soyayyar dake tsakanin mu adalciba. I love and I've waited for him for good six years so shekaru biyu agaba bakomai bane agurina so far as he'll attain all we're looking for in him" Sadiq yaji dadin kalaman Ammi,yace "I'm glad to hear this from you. Allah ubangiji yashige mana gaba" Ammi tace "Amin ya rabbi"

The following day dasafe jirginsu Muzammil yasauka a Yola around 11am na safe. Ummi dakanta tareda girls dinta ciki kuwa harda Ammi da Naanaa sukaje suka daukoshi a Airport. Mami ce kawai bata bisuba. Ganimar dayayi missing jiya kuwa dukseda Ummi tasake yimasa nasa. Haka tatasashi agaba seda yaci kowanne,Muzammil harsaida yaji kamar cikinsa zaifashe anma inaaa. Ummi tadage,tace ya rame sosai bakuma komai ne yajawo masa ramar ba irin rashin samun wadataccen abinci. Muzammil kamar zaiyi kuka yace "Toh ai Ummi ba dura abinci dayawa lokaci guda bane zaisa inyi regaining weight dina" Ummi tace "Eh nasani. Ainima bacewa nayi daga yanzu kagama ba. Anjima zaka dura wani,gobe da safe ma haka,da rana too kai harka koma Damaturu haka zamunayi kullum" Muzammil besan lokacinda yakware ba. Kanninsa dasukayi surrounding dinsu suna kallon dramarsa da Ummi mezasuyi inba dariya ba.

Yace "Nashiga uku dan Allah kiyi hakuri Ummi" Ummi tace "Aibaka shiga ukuba tukunna. Bani zakayiwa tsiyaba ina yimaka gata kana wani cemin dure nake maka" dakyar dai akasamu aka shawo kan Ummi tahakura tayada makamanta.

Ranar agida Muzammil ya wuni yana hutawa se the following day yazaga Family house din akayi gaisuwar sallah. All this while Muzammil behadu da Mami ba. He's trying all his possible ways wurin ganin yayi making things easier for them and he don't want to keep giving false hope to the Family members. Yana gani kullum zasu shirya ayi family pictures kafin afita ziyarar sallah anma sam baya yarda yashiga ayi dashi dankuwa yasan along the way za'a iyacewa sutsaya ayi masu shida Mami. Seya koma ma baya yini a gidan,dayayi wanka yashirya zaitafi gidan Captain Abbas dayake suma sunzo gida yin sallah. Acan dimma be tsiraba dan kullum Matar Captain Abbas din tana cikin tambayarsa yaushe zai kawo mata Kawarta(Mami) and he would only smile. Se aranar sallah na hudu suka hadu. Sunyi ziyara within the family house babu kofar da basu shiga ba,sunje fun fair,sunje meet and greet,sunje school reunion yau kuma gidajen Yan uwa dake cikin gari zasukaima ziyarar. Suna zaune parlourn Ummi suna jiran Fa'iza ta karasa shiri shikuma yafito daga daki zaitafi gidan Captain Abbas yaganta. She was wearing a boubou gown da akayi masa hadadden dinkin zamani awani ubansun Supern ta. Simple makeup tayi anma karkuso kuga irin kyaun da tayi dan bakadan kalar Supern da dinki da akayi suka amshi jikintaba. They were soo lost in each other's eyes,ita mamakin irin ramar dayayi takeyi dukda hadadden milk shaddan dayasaka ta amshi jikinsa sosai shima.

Intace batayi kewansaba tayi karya. She miss seeing his calls on and on on her phone screen dukda kuwa bata taba yunkurin dagawaba,she miss seeing his morning,afternoon,night and every silly text he usually send her dukda kuwa babu wanda tataba yarda ta karanta bare har tayi  tunanin yimai reply, she miss how he teases and pull her legs all the time,barinma lokacin datake kaimai abinci kullum da dare,she miss every bit of attention he was giving her! A yan kwanakinnan sautari da wayarta tayi kara alamun shigowar text ko call she always wish it was from him....tayi kewarshi fiye da tunanin me karatu da alkalamin Zeeeneeertu bazai iya rubutawa ba

But then at thesame time she's glad he's put a halt to everything from his side too. Koba komai it'll help both of them wurin moving on easily.

Gaisheshi da Ammi tayine yafidda su a reverie dinsu duka,Muzammil yayi gyaran murya his voice not audible yace "Lafiya lau Hajiya Ammi" daganan kuma yashiga zolayarta da ina zasuje haka irin wannan wanka haka? Nan ta sanar dashi ziyara zasu fita kafin Naaana tagaidashi ya amsa sannan Mamin ma tayi thesame thing.

Dede lokacin kuma Fa'iza da Ummi suka fito Fa'iza na fadin "Yauwa Ummi ga Hamma ma seyakaimu kawai" dan harararta Muzammil yayi yace "Cemiki nayi nibanida gurin zuwa?" Ummi tace "Ina zakaje?" Muzammil yace "Gidan Captain Abbas" Ummi tace "nagadai tunda kadawo kullum kana hanyar gidan Abbas dinnan. Yau kadai ka hakura mana kuje kuyi ziyara cikin Yan uwa abu daga bana sai badi?" Muzammil yace "Innaje gurin Captain Abbas dinma ziyara muke fitadai Ummi" Ummi tace "gidajen Abokanan ku ba?" Fa'iza tace "Don Allah muje Hamma. Su Aunty Ilham dama na mitar baka taba zuwa gidan suba" adole Muzammil yayarda sutafi.

Koda sukaje jikin motar Ammi ce tayi sauri tashige gidan gaba,hakan ba karamin dadi yayima Mami ba while on the other hand Fa'iza keta mamakin Abunda Ammi tayi anma se batace komaiba. Haka suka hau ziyara gidan yan uwa da abokan arziki. Koda sukaje gidan Ilham karkuso kuga irin farin cikin datayi da ganin su,barinma data gansu tareda Muzammil tace "Oh yaudai Allah yayi ga Commander a gidana dukda inada tabbatacin albarkacin Yan Matannan naci" shidai Muzammil murmushi kawai yayi. Kankacemi tacika gabansu da kayan motsa baki sannan tazauna suna hira. Yaranta biyu kuwa tuni suka dale cinyar Muzammil. Mimi na game a wayarsa ayayinda Noor keta yimasa gwaranci and looking at the two girls he could not help but think of the past. They were suppose to get married thesame day with Ilham dabadan Allah beyiba. Dan satan kallon sashin Mami dake zaune gefensa kan two seater sunata zuba dasu Ilham yayi kafin yasake maida dubansa kan Noor and the urge to speak of his feelings immediately rush over him. Yayi kasa da murya yanda itakadai zata iyajinsa yace "Our first two kids would have been this age too had it been......" sekuma ya lumshe ido yakasa karasa kalamansa...

Mami jin maganar tayi kamar daga sama hakanan batasan lokacin data juyo tana kallonshi cikin sauri ba anma sedai har yayi regaining emotions dinsa. Yanda yadage yanata wasa da Noor ko kallon sashin datake bayayi zaka iya rantsewa maganar ba daga bakinsa yafito ba,sekawai ta tsaya tana admiring yanda yake wasa da Noor da Mimi. She could swear,he'll make a great Father.

Ranar se yanma lilis suka koma gida and that's the end of their Sallah celebration se fatan Allah yanuna mana na badi.

________

Ana jibi magabatan Sadiq zasuzo Abba yaje yasamu Daddy sukaje suka samu Abba Babba da Daddy Babba kan sunaso suyi wata muhummiyar magana dasu anma so samu agida ba'a Fada ba inda take sukayi deciding suhadu a sashin su Daddy Babba dadare bayan antashi daga Fada. Aikuwa 13 minutes after 9:00pm gabadaya Maza hudun suka hadu a main parlourn gidan. Daddy yadubi dattawan Ya'yan nasa guda biyu yace "Toh gashidai Allah ya taramu guri guda kamar yanda kuke bukata. Wane maganane kuke tafe dashi?" Abba ya sunkuyarda kai kasa yace "Akan maganar Auren Mami ne dama" Abba Babba jin haka yasaki murmushi yace "Kaii maganar kenan dama?aida zamuyita acan Fadar ma babu wani matsala. Aiko kunkyauta dakuka tada maganar danko jiya seda mukayi zancen dasu Yaya Himu a Fada kan yakamata atsaida komai da lokaci kafin kukoma,Yara nata girma shekaru nata ja duksun kama madafa alkawari kuma nanan ankasa cikashi"

Daddy duk seyaji jikinsa yayi sanyi jin zancen da Abba Babban yakeyi,yace "Abba Babba ba maganar Mami da Muzammil mukazo dashiba" Abba Babba da Daddy Babba gabadaya se suka rasa inda maganar Daddyn ya dosa,Daddy Babbane yayi karfin halin cewa "Kaman yaya?" Abba ne yayi magana wannan karan,yace "Eh Daddy wani daban tasamu yanzu" Daddy Babba dai gabadaya sungama confusing dinsa yace "Shikuma Muzammil dinfa? Meya faru dashi?" Abba yace "Cewa yayi yafasaa" Abba Babba baki sake in disbelief yace "Bangane ya fasa ba. Shida bakinshi yace muku ya fasa?" gyadakai Abba yayi ahankali sannan yashiga basu labarin yanda Muzammil yayi rejecting Mami 6 years back tiryan tiryan and everything that transpired. Daddy Babba gabadaya yakasa digesting maganar,yace "And when did all this happened?" Abba kanshi nakasa yace "6 years back. Shine babban dalilin dayasa muka koma Sweden ma" in disbelief Daddy Babba yace "This much has happened 6years back and you're just informing us? And didn't you and your BROTHER convinced me that you were going there only for business purpose lokacin....?" Yanda Daddy Babba ke maganar kadai zakasan he felt betrayed,unimportant and was taken for granted....sosai ranshi yabaci

Abba Babba da is equally shocked as his Brother yace "Kama ajiye wannan batun agefe Ya Himu because this's a story for another day. What I can't seem to understand is if all this has happened miyasa haryanzu Umar keneman Auren Mami yake kuma ta shirye shirye?" Daddy Babba in agreement tace "kaima katayani ganin wannan lamari dai Ibrahim"

Daddy da tunda yayi magana saudaya besake cewa komaiba seyanzu,yace "I was a living witness duka abubuwan da Muazzam yafada gaskiya ne agabana komai yafaru but I don't know why Muzammil went ahead with maganar Auren before resolving the previous issue" Daddy Babba yace "Kiramin Muzammil din yanzu. Kai harda Mamin ma duka kace suzo munanan muna jiran su" babu bata lokaci Daddy yayi dialing number Muzammil da Mami yasanar dasu sakon Daddy Babba.

Ba'ayi mintuna goma ba dukansu suka iso parlourn. Abba Babba yadubi Abba yace ya sake maimaita abunda yafada dazu inda take yasake bayani briefly. Abba Babba ya dubi Muzammil da Mami at thesame time yace "Is this what happened 6 years back?" Gyadakai sukayi duka lokaci guda. Abba Babba yadubi Muzammil yace "knowing all this has happened miyasa kazomin da zancen aurenka da Mamin kaketa shirye shirye kuma?" Muzammil kansa na kasa yace "Nazo nagane kuskurena nane shine nake kokarin gyara komai" Abba Babba yace "Ka taba ganin inda ba'agyara baya ba se atari gaba kuma? You should have inform me about your wrong doings first" Muzammil yace "Ayimin afuwa Abba Babba. Daddy da Abba wanted to keep it a secret from you all sabida kar hankalinku yatashi shiyasa nima bance komai gameda hakan ba" Abba Babba yace "How will you mend everything bayan kaida kanka kaine silar komai?" Muzammil yace "ko alokacin danayi wannan abun bawai nadaina son Mami bane ba and i still  do Abba Babba. Kuskurene irin na Dan Adam da baya wuce kan kowa" Abba Babba yace "Why did you reject everything that was between you both then?" Shiruuu Muzammil yayi bece komai ba kanshi na kasa ayayinda Abba Babba yazuba masa idanu yana nazarinsa na wani lokaci. can yace "Do you feel keeping it within yourself will be best?Do you feel not saying it out will be better for everyone for peace to reign?" Gyadakai Muzammil yayi ahankali

Abba Babba yasan halin jikokin sa kaf kamar yanda yasan tafin hannunsa yakuma san irin bond dinda ke tsakanin Mami da Muzammil. He knows what both of them are capable of dawanda bazasu iya ba. He feels this's just a little misunderstanding da daga Parents har Yara biyun suka kasa solving keenly atsakanin su kowa yadauki zafi yadaura aka and realizing this he wouldn't let shaitan get the better of them. Karamin abu irin wannan bekai ya tarwatsa alakar da aka jima ana ginataba dan yanada tabbacin daga Mami har Muzammil babu wanda zaitaba maye masa gurbin dan Uwansa,babu wanda zaitaba son wani fiye da yanda sukeson junansu.

Yayi gyaran murya yace "Toh kunjii....Nidai aganina maganar ace anfasa Aure ko ayita putting blame akan wani duk bai tasoba. Cikin mu nan duka babu yaro karami sabida haka yara bazasu kicincina maganarda batada madafa ba mukuma mubiye su muzama kananun mutane. Hausawa suka ce abunda Babba ya hango yaro koyahau dogon dutsi bazai gani ba sannan amatsayinmu na iyayensu basu fimu sanin abunda yafi dacewa dasu ba. inamai tabbatar muku wataran su da kansu zasuyi alfarahi da abunda zamu yanke. Da ace tun awancan lokacin kuka sanardamu halin da ake ciki da ba'akawo wannan gabar ba anma dukda haka bai baci ba and alhamdulillah that shi wanda yakawo matsalar ma yagane kuskurensa yana kokarin ganin komai yagyaru. Bansaniba koya sanar daku but he's been preparing for the wedding for morethan 2 years now. Yayi gini a both nan cikin Family house da Damaturu ko ina anyi furnishing. Yasayi akwatuna and recently yace min yatura kudi anakan hada lefe. We were just waiting for this moment azo ayi magana asaka rana and Inagani in akace anfasa yanzu ba a kyauta masa ba so i hope each and everyone of us will put everything behind us yayi hakuri a tafiyar da abun yanda aka tsara. zumuncin dake tsakani yafi karfin ace shedan zai iya wassarare dashi sabida silly reasons haka" Abba Babba yadubi sashin Daddy Babba cikin son jin opinion dinsa yace "This's my own perception anma kai me kake gani Ya Himu?" Daddy Babba da sosai yaji dadin bayanan Abba Babban dankuwa decision dinda ya yanke kenan yace "nooo go ahead....shawararka tayi dannima abunda nayi niyar yankewa kenan...."

jinjina kai Abba Babba yayi sannan yamaida dubansa ga Abba yace "Batun Yaron dake neman Mami kuma inaga indai magana batayi nisa tsakaninsu ba abasu hakuri kawai inkuma magana tayi nisa harkun riga kunbasu izini suturo then zan fada muku baku kyautaba. Ko a addinance ba'a neman aure kan aure. Yes officially ba'a zauna ance anbawa Muzammil Mami ba anma ai kowa yasan da maganarsu akasa. Regardless of everything that happens daya kamata ayi clearing tsakaninsu kafin ashigo da maganar wani but then what can we do? Kuskure anriga anyishi neman hanyar gyara ake yanzu. Aceda iyayen sa su dan tsagaita zuwa aturomana Yaron muyi magana dashi tukunna. Nizan sanardashi komai inkuma bashi hakuri. Zamu kuma bashi dama in acikin yan uwanta akwai wanda yaga tayi masa se mubashi because I'm sure he must be from a reputable family tunda kuka a mince mai"

Abba kuwa shikadai yasan irin tukukin bakin cikin dake cinshi arai as Abba Babba is speaking. He cannot believe even after hearing all that Muzammil did har yayi confessing dakanshi anma yayi taking side dinda tareda daukan wannan decision din and he's seeing everything as silly and not reasonable!? Damuwarshi Family intact!? What about Mami? What about the things Muzammil has caused her? What about all that she went through? He didn't even bother asking her opinion bare yaji ko haryanzu tana son Muzammil din kobata so ya yanke hukunci! Sekace ba jikarsa ta Yar cikinsa ba!? Inshi besan darajartaba shi yasan darajar kayansa! Inshi beyi witnessing halinda ta shiga awancan lokacin ba shi agabansa komai ya faru and he wouldnt want even if it's his enemy to go through such bare yarsa ta cikinsa! If as an elder bazaiyi adalci yayi taking decision dinda yakamata ba then he has no choice than to stand for his Daughter and he don't mind what everyone will think of him!duniyar tacanza yanzu! Shiba irinsu iyayen da masu hakuri da kauda kai akan al'amarin Ya'yansu subari wani yayi deciding ma rayuwar su bane sabida kara......! Ahaka ake cutan yaje yafada wani hali and Daddy babba too....he cannot believe ya goyi bayan maganganun Abba Babban ba!

Yasauke kai kasa batareda ya iya kallon idanun kowaba yace "Naji bayanan ku Abba Babba but I'm sorry to say this is unfair to Mami sannan koda ace batada wani manemi akasa after everything that happened bana tunanin har abada zan iya bawa Muzammil aurenta" Daddy Babba tsabar takaicin abunda Abba yayi besan sanda yatashi ya wanke shi dawani wawan Mari ba,yace "Muazzam yau mu zaka nunawa ka haifi 'Ya dahar ana yanke hukunci akanta kana cewa it's unfair to her!!!? Sokake kace kafimu sonta komi!? Or are you trying to show us our lane and limit!???" Daddy Babba yayi kwafaaa cikeda bacin rai yace "Shikenan barina nuna maka nawa iyakar nima! Inkana gadara kana iko da ita toh ai nima ina Iko dakai kuma baka isa katake maganata ba inkanaso ka wanye lafiya" yanuna shi da yatsa strictly yace "Umarni nake baka.....Ko bayan raina banyarda Mami ta auri wani ba inba Muzammil ba! Allah yasa dukanta yake kullum! Allah yasa cin namanta danye yake kullum! Allah yasa kasheta yakeyi every now and then!!!! banyarda ko yaji tayi agidansa ba bare akai ga  batun tanemi saki if not the consequences will be on you......!!!"

Mami jin tsauraran kalaman Daddy Babba akanta da Abba batasan sanda taruga da gudu takarasa gabansa tarike kafafunsa tana kuka mai tsumarai tashiga rokonsa ba

"Dan Allah kayi hakuri ka rufamin asiri kayi min rai ka sassauta kalaman ka akaina da Abba Granpa....wallahi bazan iya Auren Hamma ba! Bazan iya rayuwar aure dashi ba! Bazan iya aurensaaa baaa!Ko mazan duniya sun kare da in aureshi na gwammace inkare rayuwata hakanan! Da in aureshi gwanda inshiga duniya inyi rayuwar dan....." ball dinda Daddy Babba yayi da'itane yahana ta karasa kalamanta. Besan sanda yazaro cable jikin TV yashiga nadanta duk inda hannunshi yakaiba! Muzammil ganin yana kokarin illata ta dagudu yazo yana kokarin kareta yashiga bawa Daddy Babban hakuri tareda rokon yakyaleta hakanan anma ko gezau. Sekawai ya rungumeta cable din na sauka jikinshi. Haka Daddy Babba yahadasu duka yadaki banzaye,yana haki cikeda takaici yace "Ba laifin kibane! Laifin ubankine dabai nuna miki mahimmancin zumunci ba yasa kike furta wadannan kalaman! Bakuma shiga duniya ba Allah yasa hadiyan rai zakiyi ki mutu maganata babu fa shi. Indai nina haifi ubanki zaikuma yimin biyayya baki da miji bayan Muzammil. Bakuma sai wataranba! Ba gobe ba ba anjima ba yanzunnan zan daura muku aure in akwai wanda ya isa ya hana ingani!" ya juya sashin Daddy da ba abunda yakeyi se hawayen takaicin abunda ke faruwa yace

"Mu'allim tashi kahado min kan dattawan gidan nan kace inason ganin su a Fada nan da mintuna go....." anmasedai ko rufe bakinsa beyiba Mami tasaki jiki ta sume kafin kuma suyi aune sukajiyo karar faduwan mutum acan kusada kofar daki. Hajiya Mami dake zaune a dakinta ne jin hayaniyar dasuke yi tafito inda idanunta suka gane Mata abunda ke faruwa ta yanki jiki tafadi. Tsakanin Abba da Daddy ba asan wanda yariga wani isa inda Hajiya Mamin ke kwance almost lifeless ba. Muzammil da dama yana zaune kusa da Mamin tunda Daddy Babba yagama nadarsu ne yayi saurin tarota ayayinda Abba Babba yashiga neman inda zaisamo ruwa acikin gidan sabida kawowa rai biyun dauki and at thesame time blaming himself for all that's currently going on. Daya san haka zaifaru dabai ja maganar ba anbarta ayanda su Abban sukazo dashi....

*Assalamu Alaikum lovelies. Questions will be posted on wattpad tomorrow regarding this book insha ALLAH and I'll appreciate if each and everyone of you participate please. Kobaki taba comment ba kidaure kifadi naki ra'ayin gobe as it'll determine how this book ends. Yes I've my own lines already but who knows I might change em after reading your reviews? Just curious if tunani na da nakudayane...*

Nagode kwarai da soyayyar ku gareni😍😘

Vote
Comment
Share!

Continue Reading

You'll Also Like

463K 29K 40
Let's see how different personalities mends with each other to form a beautifull bond together. Where the Eldest is calm and cold, Second is aggress...
Sarkaar By eira

General Fiction

51.2K 3K 21
The book contain painful and horrifying visual in book read at your risk This my first time story based on india in 1970s. This story deal with the...
247K 15.4K 46
The feeling of being abandoned by one's own family was not unknown to Aadhira. She hates her family for abandoning her when she was only a newborn, l...
150K 2.4K 44
Sweet Romantic (Loose Trilogy #2) Failure and disappointment are the hardest things that she's afraid to achieve. Amaryllis Raine Lozano, a girl ful...