49

3.5K 189 3
                                    

             💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 50

BAYAN WATA →1
         
       Bikin su safna ya kankama, anata hidima dakai kawo, yau takasance ranar kunshi suna tsakar gida itada Ameera da k'awayensu irinsu zeenat baseera da sauransu, masu k'unshine har uku sukema k'awayen amaren, saikuma Basma datakema Ameera da Safna harma angama ma Ameera yanzu safna akeyimawa, hira da barkwanci aketayi irinna taron k'awayen amarya.
   Duba nakai ga fuskar safna, kadaran kadahan take, bata d'aureba sannan kuma bata saka baki cikin hira da dariyar k'awayen nasu.
    Rahma ta fito daga cikin falon hannunta d'aukeda filet na d'anwake dayasha yaji, sanye take dajar atanfa zani da Riga, rigar fitet ce wannan yabama matashin cikinta damar fitowa d'as, bak'aramin k'yau cikin Yamataba, gashi yakaramata fari da 'yar k'iba masha ALLAH, ga atamfar takuma haska k'yawun halittar jikinta.
    Da yawan 'yammatan wajen bak'aramin birgesu Rahma tayiba, taja kujera 'Yar tsigunno tazauna tana fad'in kai aunty Ameera k'unshinfa yabada ma'ana tafad'a tana k'ara lek'a k'afar.
    Murmushi Ameera tayi ta ce, "da gsk auta?.
    Wlhy kuwa yau duk kunfito amarenku keda aunty safna.
    To mungode, ke sai yaushe za'a miki naki?.
     Saita gama muku 'Yar wulak'ancin idan ta gadama, nikoma zan iya jure zaman?, Rahma tayi maganar tana hararar Basma.
    Dariya Basma tayi ta ce, " karki damu uwar uku dolene namiki kodan ya Abdulmaleek yagani.
     Rahma ta d'akama Basma duka a baya 'Yar fatan tsiya ukun lfy?, nama haifi d'ayan mana, saidai ke ALLAH yasa Ranar damuka kaiki ki samo mana biyar nasan Yaya Salman bazaiyi wasaba.
      Basma dake shafa wajen da Rahma ta doketa ta ce, ''Mara kunya wlhy Rahma kin fetsare.
     Dariya Rahma tayi tanacin d'anwakenta dayaji uban yaji sai faman sheeeee! Take da baki saboda zafin yajin, ta ce, "kibari zan fad'amiki yanda akayi na fetsare.
    Anty Ameera ta ce, " ALLAH ya shiryeku yarannan, yanzufa Rahma saitace ta girmemu ko?.
    Dariya duk 'yan wajen keyi, wata acikin 'yammatan amaren ta ce, "eh mana tunda tarigaku shiga daga cikin itace babba yanzu.
   Dariya suka kuma shek'ewa da ita wasu harda tafawa.
   Safna dai fuskarta tamau babu alamun annuri, dan ita hirar tasu ba burgeta takeyiba.
   Wayar Rahma yafara Wringing, d'auka tayi tana murmushi, cikin wata sassanyar murya da kowa bayajinta awajen harsu Basma ta ce, ''Assalamu alaika ya Nurulk'albi.
    Bobo dake zaune a office d'insa sanyin AC da k'amshin turarensa na ratsashi yalumshe idanunsa yana wani murmushi na musamman tamkar yana gabanta ya ce, " wa'alaikissalam my Nusfulhayat, ina fatan kina cikin nagarta da aminci da  k'oshin lafiya keda babyna?.
         Murmushi mai sauti Rahma tayi cikin salonta ta ce, "Normal Muke, kaima muna fatan kasancewarka cikin kuzari da jarumta irin na ma'aikacin kwarai mai k'ok'arin kare hak'in al'ummarsa?.
     Alhmdllh my Nusfulhayat duk abinda kike hasashe agareni ALLAH yasaukar da ni'imarsa agareni musamman dakika kasance mai yawan tunatar dani waye ni akowane dak'ik'a na rayuwata.
   Masha ALLAH Rahma tafad'a murya anarke.
     K'ara lumshe idanunsa yayi dak'ara lafewa cikin kujerar yanad'an lilakansa akujerarsa alamun yanajin dad'in yanayi da hirar dasukeyi, ya ce, " mikikecine haka kiketa faman shan yaji?.
      Dariya mai Narkar da zuciya Rahma tayi ta ce, ''canki mana."
     Shiru bobo yayi yanad'an nazari, zuwa can ya ce, "tom saidaifa muyi da sharad'i?.
      Hummm sharad'in mi?.
    Idan na canka dai-dai to yaufa babu k'orafi awajen barci, dannaga wani guduna akeyi yanzu.
    Dariya mugunta Rahma tayi ta ce, " nayarda Dan nasan bama canka zakayiba.
    Shima dariyar yakeyi ya ce, "kardai ki cika baki.
    Batace komaiba saidai tayi murmushi.
   Shima shiru yayi yana tunanim mizaice?.
     Rahma tayi gyaran murya.
   Ai kamar ta zurgud'a masa allura ya ce, " d'anwake kikeci.
   Shiru Rahma tayi, shikuma shirun datayi yabashi damar tuntsurewa da dariya yana fad'in naci gari, yarinya yau ki shirya babu d'aga k'afa.
    Kukan shagwa6a Rahma tasaka masa tana fad'in itadai bata yardaba.
    Dariya su Basma suka saka mata har bobo na jiyosu.
     Safna kam tsaki taja ta na kauda kai.
   Rahma tajuya baya danjin suna mata dariya, jin dariyar dayake mata shima yasa tadage akan bata yardabafa.
   Shima dagacan cikin dariyar ya ce, "ahaf 'yammatana ai babu hanyar ku6ta, kima shirya tarbata Dana tashi daga office zanbiyo mutafi gida nasha Amarcina yanda yakamata.
   Da sauri ta ce, " banida lfy fa.
   Karki damu inada magani, yana gama fad'a ya Yanke wayar yana cigaba da mata dariyar mugunta.
   Ameera tarik'e ha6a oni auta d'an koyamin shagwa6ar nan mana nima na iyata, Rahma tarufe fuskar tana dariya, Ameera ta ce, "yo ALLAH kanama mijinka wannan shagwa6ar ai babu inda zai fita, shiyyasa ya Abdulmaleek baya ganin kowa saike kad'ai.
     Tashi Rahma tayi tabar wajen suna mata dariya.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon