7

3K 186 1
                                    

              💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 8

_Gidansu Safna_*
           Safna na kwance akan gado tana chart, sai faman murmushi takeyi, da alama tana jin dad'in charting d'in.
   Rahma dake zaune akan sallaya tana karatun alkur'ani ta waigo ta kalli safna dataketa 6a66aga dariya harda rik'e ciki, kai Rahma ta girgiza tareda fad'in ALLAH ya shirya azuciyarta.
  Kanta tamaida tacigaba da karatunta.
   Safna kam bamatasan tanayiba, dariyarta taketayi cikin farinciki, hira takeyi da Baseera akan nemomata Bobo, Baseera tana gayamata akwai wani guy a unguwarsu sunansa *boy shiyakama subama aikin, Dan tasan cikin sauk'i zai samomusu bobo da labarinsa.
    Tak'ara wani d'an ihun farinciki, tareda fad'in saini mata agidan Bobo.
    Rahma takuma kallonta cike da mamaki, ganin bazata barta tayi karatunta cikin Nutsuwaba yasa tarufe alkur'anin tayi addu'oin ta tamik'e ta ajiye alkur'ani ama'ajiyarsa.
    Hijjabinta tacire tana fad'in aunty Safna kofa sallar magriba bakiyiba har anyi isha'i amma kina kwance kina charting akan abinda k'ilama bazai amfaneki da komaiba.
    ALLAHU Akbar  maikaratu nagaba, Safna tafa idonta akan waya, tacigaba da fad'in malama Rahma jawo wata ayar na haddace wannan.
   Ajiyar zuciya Rahma ta sauke, ta ce, "Niba malamarki bace, kuma ba wa'azi nake mikiba, ina tunatar dakene dannaga kin shagala.
     Wani wawan dundu safna tasaukema Rahma abaya, Dan ubanki idan aljanna takice ki hanani, shegiya 'Yar iska uwar tsari, kenikam daba agabana ummi ta haifekiba wlhy danace anmata canji a asibiti, anya kuwa acikin 'yan barka wata bata sace ainahin d'iyar da ummi ta haifaba ta ajiye mata ke?.
    Rahma tashare hawayenta ta ce, " kije kitanbayeta k'iladai kece aka canja mata, Dan halinki daban dana mutanen gidanna.
    Afusace Safna taduro daga gado tana d'urama Rahma zagi.
   Tuni Rahma tafice tabar mata d'akin.
   Afalo taci karo da abbansu yadawo masallaci, sannu da dawowa Abba. Yauwa d'iyar albarka ina zuwa haka?.
   Ba inda zani Abba, nadai fito falone nasha iska.
   Masha ALLAHU, ina 'Yar uwar taki to?.
   Tana d'aki Abba.
Yauwa jeki kiramin ita zamuyi magana, ina umminku?.
     Ganinan Abba Shaheed ummi dake fitowa daga d'aki tafad'a.
Tamai sannu dazuwa sannan tafara shirya musu abinci.

Rahma tatsaya abakin k'ofa ta ce, "aunty Safna kizo Abba yana kiranki.
   Shegiya munafuka gulmata kina kaimasane?.
   Niba munafuka bace, yace dai kizo..., tana gama fad'a tafice.
   Safna tasakko daga gadon tana mita, zan koya miki hankaline 'Yar banza maikan dankali.
    (Araina nace kekuma maikan doya ko?.)

Kusada Abba taje tazauna, Abba gani.
   Kanta yashafa yana murmushi haba safnan Abba miya faru kika k'unshe kanki a d'aki?.
   Zamanta ta gyara tana ballama Rahma harara, babu komai Abba nayi sallane INA zaune ina Azkar.
   Da k'yau 'Yar albarka.
  Rahma kam ido tazaro waje danjin k'aryar da safna ta gilla, saikuma ta k'unshe baki tana dariya.
  Safna na kallonta, Dan haka haushi yak'ara kamata.

_(Hattara iyaye kuringa kula da addinin 'ya'yanku, akwai yara dayawa masu wasa da salla irinsu Safna, wata zakiga tana zaune tana chart za'a kira salla, amma ko'a kwalar rigarta, har Matan aurema akwai masu halinnan, musamman yanzu da karatun Novels sukayi tasiri arayuwarmu, yakamata duk lokacin da aka Shiga sallah kiringa lek'a d'akin yaranki kitabbatar suma suyi, ALLAH yasa Mugane)._

Ummi ta ce, "kutaso ga abinci, atare suka tashi har zuwa dani, anacin abinci Safna na chart saida ummi Tamata magana sannan ta ajiyewayar tana zum6ura baki.
      Bayan sun kammala Rahma takwashe kayan, takaima masu aiki su wanke.
   Falon tadawo Inda iyayenta suke zaune harda safna.
  K'asa ta zauna kusada Abbansu.
   Zamansu babu dad'ewa ya Shaheed da ya Muneer sukayi sallam.
  Cikin girmamawa suka gaida iyayensu, suma suka tambayesu ya iyalinsu?.
  Kowa ya amsa da lfy k'alau.
    Suma su Safna suka gaishesu.
   Bayan gama gaishe2 Abba ya ce, "dama bawani abune yasa na tarakuba zancen auren safna ne yatashi.
   Wata irin d'agowa Safna tayi arazane, aurena kuma Abba tafad'a da k'arfi!!!.
   Suduka kallonta sukeyi, Abba ya ce, " eh aurenki safna ta, kiyi hak'uri abin yazo miki wani iri kuma 1time, wlhy nima haka lamarin yazomin babu shiri.
   Kuka safna tafasa tana fad'in itafa wlhy akwai Wanda takeso Dan haka bazata yardaba.
   Ya Shaheed ya daka mata tsawa, wlhy idan bakimana shiruba jikinki zaiyi tsami, iskancim banza kawai, Abban kike fad'ama haka?.
   Toni Dan ALLAH baza'a bari aji uzurinaba haka kawai amin auren dole, narantse bana sonsa karma afara wlhy.
        Idan bahakaba kuma wlhy zanbar gidannan.
   Duka ya Muneer yakai mata tatashi dagudu tashige d'aku tana kuka da fad'in wlhy itafa bata sonshi.
    Ajiyar zuciya Abba ya sauke ya ce, "akwai matsala kenan?......
   Babu wata matsala Abba Shaheed ashema ita ta haifemu bamu muka haifetaba, wlhy acigaba da hidima kawai, idan ankaita ta mutu aranar, ni wlhy dama halin Safna ya isheni agidannan.
   Shikenan ummin Muneer yanzu dai munyi dasu ranar juma'a zasu kawo komai, nasanar da Alhaji Rabi'u, (yayan ummi), sannan kuma suma su yaya na sanar dasu shida Abubakar.
  Tom ubangiji ALLAH ya tabbatar da alkairi yasa ayi damu.
   Amin Abba yafad'a, ya kalli su Muneer ya ce, " to manyan yayye yakukace?.
  Dariya sukayi, yayi daidai Abba ALLAH ya Sanya alkairi, insha ALLAHU zamu fara shirya biki.
    Tattauna maganar bikin suka cigaba dayi har zuwa wani lokaci, daganan su ya Shaheed suka tafi gidajensu.

+.+.+.+.+.+.+.+.+.+.+.
    A 6angaren bobo kam abubuwa biyune suka cinkushe masa tunani, ga tunanin yarinyar da akaima fad'e, gakuma tunanin zancen Appa na yau, yasan appa sarai mutumne mai sauk'i da sanyi, komai zaiyi zaiyishine cikin hikima da lallashi, to amma mutumne kaifi d'aya idan ya ve e babu maisakashi fad'in A'a, Dan duk abinda zaiyi baya yinsa da ka saiyayi bincike.
   Yasan ko giyar wake yasha bai isa ya gujema Auren nan ba, to amma shikam harga ALLAH baiji zaiso wata mace bayan Ni'ima ba, duk macen datayi kuskuren shigowa rayuwarsa bazata samu wani farincikin saba, ya rintse idonsa, ahankali yak'asa gaban wani k'aton hotonsa shida Ni'ima, sunyi k'yau sosai ahoto, suna tsayene gaban wasu filawoyi sun fukanci juna, yad'an rissina yadafa cikinta sannan tanada cikin Nawal, itakuma tana kallonsa shida cikin tana murmushi.
   Hoton sunyi bala'in k'yau, wasu hawaye suka zuraro akumatunsa, baidamu daya gogeba sai shafa hoton daya cigaba dayi, yad'au tsawon lokaci yana kallon hoton daga baya yafad'a kan gado yana hawaye kamar wani mace.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
      Babu 6ata lokaci aka su Appa suka kai k'ud'i da komai ranar juma'a, antarbesu tarba ta mutunci da girmamawa, cikin girmama juna komai ya gudana aka tsaida biki sati uku kacal, saidai daga amarya har ango suna cikin tashin hankali, garama angon yadaure sosai yamaida komai ba komaiba, harma yanad'an saka baki idan 'yan uwansa suna maganar shagalin bikin.
   Haka yasa ammi taji dad'i sosai itada Appa, sai albarka suke saka masa.
   Nawal ma sai murana take ankusa kawo mata momynta.
  Shirye shiryen biki ya kankama sosai Dan hidima akeyi babu kama hannun yaro, abubuwa sosai su ya Hamza suke shiryawa.

+.+
    Yarinyar da akaima fad'e tana samum sauk'i saidai har yanzu bata iya magana, kullum sai Bobo yaje asibitin safe da yamma, har yanzudai ba'a samu iyayentaba ana kan nema, gashi bata magana bare asamu wasu bayanai daga gareta.
  'Yan sandama suna aikinsu na binciko Wanda ya aikata laifin ta hanyar Number motarsa da matashin nan ya d'auka.
  To ALLAH yasa adace amin.

A6angaren Safna kam abubuwa sun cakud'e danta tsaya kaida fata batason auren, anbuga anbuga tak'i, anyi lallashin abanza, hardai takai yau ya Shaheed ya zaneta amma abanza, Dan tace wlhy aka matsa mata zatabar gidan.
  Hankalin Abba yatashi sosai, yarasa mafita, gashi har anfara shirye shiryen biki, Dan gobe za'a kawo lefe............

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now