22

3.3K 222 2
                                    

           💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 23

   Safna ga sir Hamza canfa yazo, baseera tafad'a tana kallon Safna data rafga tagumi kamar wadda akace ummi zata mutu yau.
    Zumbur tamik'e tana fad'in habadai?.
     ALLAH kuwa yanzu yashiga office d'insa.
    Kinga tashi muje kirakani.
    Mubari Zeenat ta iso mana tunda ta ce, "tana hanya.
    Mtsooow dallah shareta tashi muje, kinsanfa bakomaine take Goya mana bayaba.
    Mik'ewa Baseera tayi tana kakka6e doguwar rigarta, hakane kuma wlhy, kinsan zeenat ya ustaz CE.
    Aii saitaji da ustazancin ta ita kad'ai.
    Saida suka kwankwasa yabasu izinin shigowa, sannan suka shiga, bayan sun gaidashi baseera ta ce, " Sir mun biyo sawune.
    Kallonsu yake cike da mamaki, amma baice komaiba yarubuta musu number Bobo, ya d'ago yana kallonsu, ban tanbayesaba Dan ina mantawane, amma baridai yau nabaku Dan kun fara bani tausayi, dukda bansan mizakuyi da no. d'in *Abdulmaleek!* ba.
    Wlhy bawani mugun Abu zamuyi da itaba, kawai zamu sada zumincine.
    Girgiza kai kawai ya Hamza yayi, yamik'a musu number, gashi to, nadai baku number sa gama gari tunda bannemi izinin saba bare nabaku number sa mai muhimmanci, amma insha ALLAHU zaku samesa da wannanma.
     Mungode sir, ALLAH yak'ara girma.
    Amin yafad'a yana binsu da kallo atak'aice, shifa mamaki suke bashi wlhy, koda yake basuda laifi k'anin nasa ya had'u, ga k'yau ga iya wanka, uwa uba kamun kai.
   Cigaba yayi da aikin gabansa kawai.

A can kuwa suna fita Safna ta daka tsallen murna tareda rungume Baseera, wayyo k'awata yau na mallaki number Bobona.
   Dariya baseera tayi, kinga Laila karki karyani nikam.
    Miye kuma laila?, safna tafad'a tana yatsine fuska.
    Dariya baseera tayi, laila majnun mana, aigara mufara kiranki Laila kafin bobo yazama majnun.
    Dariya Safna tayi tareda Jan hannun Baseera suka nufi class.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
    Baya Rahma tashiga matsawa tana fad'in inna'lillahi wa'inna ilaihirraji'un.
   Ina Bobo baisan tanayibama, kanta kawai yayo tamkar wani zaki maijin yunwa.
    Gadon ya hawo yafincikota jikinsa, jikinta sai Rawa yake, ga kukanta ya k'aru, bakinsa da nata ya had'e yashiga wasa da harshenta tamkar yasamu alawar lollipop, agefe kuma hannunsane ke murza ko ina najikinta, Rahma dai sai dukansa da tsungune takeyi, amma baimasan tanayiba, shidai sak'o kawai yake burin isarwa.
   Yakai tsawon minti 13 yana Abu d'aya, tuni Rahma tabar kukan tsoro saidai na ceton kai.
   Shikam Bobo idonsa yarufe baimasan mi yake aikatawaba, shidai kawai burinsa  yake son cikawa, jin hannunsa a k..... Yasata k'ara rikicewa.
    Shima da sauri yasaketa danjin pad alamar tana period kenan.
   Zubewa yayi agefe sai wani wahalallen numfashi yake saukewa, Rahma tayi saurin sauka daga gadon takoma jikin bango ta mak'ale tana kuka, sai kallon yanda Bobo yake fidda numfashi tamkar zai mutu takeyi, nan take kuma tausayinsa yakamata, jitai hawayenta sun k'aru.
   Tanaso taje ta taimakeshi amma tana gudun karya k'ara damk'arta.
   Sunkai minti15  ahaka, shi yana cikin wahalar ciwon mara ko magana yakasa mata, itakuma tana cikin tsoro da abinda yamata gakuma halin dayake ciki abin tsoro.
     Bobo ya daure dak'ar ya ce, "ki matsemin lemon tsami please zan mut  u..........yak'arasa maganar da k'yar danji mararsa da kansa tamkar zasu fashe."
   Da gudu tafita zuwa kichin, cikin sauri tamatse lemon tsami wajen takwas, dama tasaka ruwan zafi kad'an awuta, tajefa lifton uku dantaga wani sa'in haka yakecewa ta dafa masa, juyewa tayi akan ruwan lemon tsamin tad'auka tanufi d'akinta yanata turiri.
   Da k'ar ya iya tashi yakar6a, dukda zafin da shayin yake dashi bai sauraraba yakafa kai ya shanye kamar yasamu ruwan sanyi.
   Mik'amata kofin yayi yakoma yakwanta, jikinsa har Rawa yake, ya ce, " lullu6eni sanyi nakeji, kuma ki kashemin AC.
    Duk abinda yace tayi masa da saurinta, sannan takoma gefe tazuba masa ido.
    Lumshe idonsa yayi, danda nan zazza6i ya rufeshi, jikinsa yad'auki azababben zafi kuwa.
    Rahma sai kallon sa takeyi tana hawaye, yanzu ba kukan abinda yaymata takeyiba, kukan halin dayake cikin takeyi, tarasa yanda zata fassara al'amarin nasa.
    Idonsa alumshe yake amma yana kallonta ta k'asan idonsa, saiyaji tama k'ara bashi haushi.
   Tunda yake baita6ajin abinda yaji yau ga mace ba sai akan Rahma, shekararsa wajen 5 babu mace, dukda yasan yana cikin buk'atar macen, amma hankalinsa bai ta6a tashiba irin yau, yarasa wace irin mace ce Rahma da jikinta yazame masa tamkar wani magana d'isu, jiyake tamkar zai mutu Dan azaba, amma lemon tsamin data kawo masa yad'an rage masa azabar dayakeji, yamanta tsawon lokacin daya d'auka rabonsa da zazza6i  mai zafi kamar haka, yarintse idonsa  yana ambatar sunayen ALLAH.
   Zuwa wani lokaci kuma sai barci ya saceshi.
   Rahma ta sauke ajiyar zuciya, yanzu kuma matsalarta d'aya shine a ina zatayi wanka?, Dan bazata sake shiga bayin taba sai an kashe tsakar can.
   Zuciyarta ta ce, "kije d'akin mijinki tunda barci yakeyi.
   Aiko tayi na'am da wanga batu, d'akinsa tanufa ta shiga bayinsa tayi wankanta sannan tafito.
    Harta shirya yana barci, kichin taje tafara girki, zuwa 2:00pm tagama takuma gyara ko ina, tana falo zaune tana kallon Hausa film Nawal tadawo, direbanta ya d'akkota.
    Dagudu tashigo gidan tana kiran momyna! Momyna!!, Rahma tamik'e da sauri Nawal tafad'a jikinta, d'agata tayi tana juyi da ita afalon suna dariya.
    Hayaniyarsu ce ta tada Bobo, yamik'e dak'yar Dan Marar tasaki saidai zazza6in shima kad'an, falon yafito, sukam bama su gansaba sunata murnar ganin juna itada Nawal d'inta.
     d'an murmushi yayi yashige d'akinsa, ko babu komai yanajin dad'in yanda Rahma take kula masa da yarinyarsa, idan ba fad'a maka akayiba bazaka ta6a cewa ba ita ta haifetaba, saidai kawai idan ka kalli Rahma d'in zakaga yarinyace batakai ta haifi kamar Nawal ba, ammafa duk wata kulawa irin ta uwa akan d'anta Rahma tana k'ok'arin bama Nawal, kuma har zuciyarta takeson yarinyar.
    Kama hannunta tayi suka shiga d'akin, tabi gadon da kallon mamaki to ina yaje?, tafad'a azuciyarta, tad'an lek'a bayi daga nesa taga wayam, inaga to yana d'akinsa.
    Da wannan tunanin tacirema Nawal kayan makarantar.
    ‘Nawal!.’
Na'am momy.
    Kije d'akin papa kigani barci yakeyi, idan barci yakeyi muje can namiki wanka.
    Lah momy bayinmu fa?.
    Akwai ojuju aciki ina tsoron shigane.
    Kai, momy kema kinajin tsoron Ojuju.
    Dariya Rahma tayi ta ce, "kinga kedai jeki duba kidawo.
    Tamata hakane Dan tambayar ta tsaya haka.
   
Da gudu Nawal tafita sai d'akin Papanta.
   Fitowarsa kenan daga wanka, yana zaune abakin gado yana shafa mai, Nawal ta shigo aguje tafad'a jikinsa.
     Uccch yafad'a yana rungume Nawal d'in, saboda yaji zafi data fad'a jikinsa.
    baby bana hanaki guje²n nan bane?.
     Sorry papa nadaina.
    Yalumshe idanunsa yana kad'a kai, toya School?, harkun dawo?.
     Eh papa, tad'ago tana kallonsa, papa kaima bakada lfy kamar momy?.
    Kallonta kawai yakeyi yakasa magana, ta girgizashi kaji papa, ajiyar zuciya ya sauke, a'a baby lafiya ta k'alau, itama momy aita warke ko?.
    Eh mana ta warke, yanzuma catayi Nazo naduba idan kana barci saitazo tamin wanka a bayinka, wai bayinmu akwai ojuju tanajin tsoronsa.
    Papa dama idan mutum yay babba yanajin tsoron ojuju?.
      Bobo dake shafa mai yanajin zancen Nawal yayi murmushi, baby Momynki tacika tsaorene, amma zan koya mata yanda zata daina, jekice mata tazo tamiki.
       Papa nima zaka koyamin Dan nadaina tsoron ojuju d'in?.
    Eh zan koya miki, jeki kirata.
    Fita Nawal tayi kiran Rahma.
     
Momy tahoto kimin.
    To Babyna, amma papa fa?, yananan ad'akin.
     Atunanin Rahma yana barci Nawal take nufi Dan haka takama hannunta suka fito zuwa d'akin bobo.
    Kanta tsaye tashiga d'akin, saikuma tatsaya cak Dan ganin bobo tsaye yana saka ma6alin rigarsa, baya tayi zata koma, batareda ya kalletaba ya ce, " kizo kimata wankan mana.
    Rahma tayi k'asa da kai kamar wata munafuka tanufi bayin rik'eda hannun Nawal.
     Shikam baki yata6e yad'auki brush yana k'ara kwantar da sajensa bak'i sid'ik, yak'ara fesa turare sannan yafice daga d'akin.
       Masallaci yanufa, saida yayo sallah yadawo sannan ya d'auki Jakar aikinsa daga fallo, yamanta a can yabarta, yacire laptop d'insa da wayoyi ya ajiye a tebird'in tsakkiyar falon sannan yakawo jakkar d'aki Yakuma fita.
     d'akin Rahma yashiga, yanufi bayimta danya kashe matsa tsakar, dube² yahauyi, can yahangota kwance a bango, tsintsiya yasa yabugota tafad'o, Yakuma bugunta ta mutu, yawanke hannunsa yafito.
    Daidai nan Rahma tashigo d'akin itada Nasal.
      Batareda ya kalletaba  ya ce, "gatacan na kashe saiki fidda.
    Tuni hawaye sun cika idon Rahma, kanta ak'asa tace, " Dan ALLAH ka fidda wlhy bazan iyaba.
    Eh tunda nazama yaronki ko?.
    A'a Dan ALLAH ka taimakeni nidai.
    Tausayi tabashi, yalura harga ALLAH tsoron tsaka takeyi, komawa yayi yasharota a faka, yay nufin tsokanar Rahma, danhaka gadan gadan ita yanufa.
    Ganin tsaka afaka kuma wajenta yayo tadaka tsalle tareda kwallah k'ara.
    Tabashi dariya amma saiya gimtse saida yafita sannan ya shek'e da dariya harda rik'e ciki, mai gadi yana hangensa abin yabashi mamaki Dan yadad'e baiga Bobo yana dariya hakaba, dama dariya mai yawa ba sabon bobo bace, sai Abu yakai matuk'ar tik'ewa yake bashi dariya, murmushinma saiya gadama yakeyi balle dariya.
    Komawa yayi ya k'ara wanke hannunsa, sannan Rahma tana shirya Nawal.
     Fallo yadawo ya kwanta saman doguwar kujera.
           Ya d'auki remote ya canja tasha, babu dad'ewa suka fito suma, Nawal taje ta zauna kusadashi tana fad'in baby kamomin MBC 3 naga cartoon.
    Rahma ta ce, "Nawal mikikace?.
    Baki tarik'e kamar wata babba, momy yi hak'uri bazan sakeba, Dan ALLAH karkice kin fasa zuwa danifa.
       Zanje dake ammafa idan kin daina.
   To na daina, papa aidai yanzu bana cemaka baby ko?.
    Bobo yakalli Nawal yana kad'a kai, yamaida kallonsa kan Rahma data nufi dinning, murmushi yad'anyi.
   Baby ina momy ta ce, " bazataje dakeba indai kina cemin baby.
    Nawal takawo bakinta saitin kunnen Bobo ta ce, "catayi bazataje dani makkah da madina ba muga kabarin Manzon ALLAH.
  (S,A,W) BOBO yak'arasa mata, to baby yanzu kindaina cemin baby kenan?.
   Eh bazan sake fad'aba, momyna ta ce, " nace maka papa.
    Jawota yayi jikinsa ya rungume, yabata kiss akumatu, I luv u my baby.
   Itama ta ce, "luv u too my papa.
   Rahma tak'araso da kuloli ta ajiye a tsakkiyar falon bayan ta janye tebir d'in, saida tagama kawo komai sannan ta ce, "ga abinci.’
   Mik'ewa yayi zaune yana satar kallon Rahma, itakam sai duk'ar dakai takeyi, yakula batason had'a ido dashi tun d'azu, ko kallan ma inda yake batayi.
   Haka suka zauna cin abincin Wanda Bobo kejin dad'insa.      

      Yasani lokaci d'aya Rahma taja zuciyarsa rusuna akan burin daya d'auka nayi mata rashin mutunci agidansa harsai tagudu da k'afarta, yafara gudanar da shirinsa ta hanyar fita harkarta, hartayi tsawon kwana 8 a gidan bata ganshiba, amma daga randa yakawo Nawal gidan yaci girkinta sai zuciyarsa tayi sanyi da d'ora alamar ? Akanta.
    Abi na biyu shine son datake nunama gudan jininsa Zuh'ra (Nawal), wad'an nan abubuwan suntaka rawar gani wajen ganinta da mutumci da daraja, dukda har yanzu bazaice yana sontaba, ‘Dan Ni'ima ce kawai macen dazaiso aganinsa‚’’ to amma yabama Rahma wani 6angare azuciyarsa kad'an kodan k'aunar Nawal datakeyi.............wringing d'in wayarsane yadawo dashi hayyacinsa, yakalli Screen d'in wayar batareda ya d'aukaba, bak'uwar number yagani.
   Sharewa yayi yacigaba da cin abincinsa, aka k'ara kira akaro na biyu, nanma yay burus.
    Rahma ce tad'ago ta kallesa danjin ank'ara kiran wayar, cikin sa'a kuwa suka had'a ido, tai saurin janye nata, shikuma yad'an lumshe idanunsa.
    Ba'a sake kiran wayarba harsuka kammala cin abincin Rahma tagyara wajen.
    Saman kujera yakoma ya zauna, yad'ora kafafunsa saman tebir, yad'auki laptop ya d'ora saman cinyarsa yana Dane dannensa na fama.
   Rahma kam homework take koyama Nawal.
   Falon yayi shiru kowa yana harkar gabansa sai k'arar TV kawai Dana AC, Wayar d'azuce dai aka k'ara kira.
    Wani wawan tsaki Bobo yasaki, afusace yad'auki wayar yana mita, wai miyasa mutane suke San takuramin ne?, ina gidan nawama baza'a barni nahuta da iyalina ba mtsooooow.
   Rahma dai tana jinsa bata d'agoba, aranta tace su iyali manya.
   Wayar yad'auka yasaka akunnensa batareda yayi maganaba.............

ABDUL-MALEEK (BOBO)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora