38

4.5K 231 4
                                    

            💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 39

Bobo dabaisan Safna nabinsa abayaba yabud'e mota yashiga, harya tada motar yaji ana kwankwasa masa gilas.
    Sauke gilas d'in yayi ahankali Dan atunaninsa Rahma ce kosu khursiyya, had'e fuska yayi Dan ganin safnace, baice komaiba ya kauda kai daga kallonta.
    Rik'e k'ugu tayi tanamai jifansa da shu'umin kallo, cikin narkewar murya ta ce, "haba my jaan wai miyasa kakeson wulak'antanine?, aiko bakomai ance kaso mai sonka, yanzu Dan ALLAH abinda kamin agaban Rahma d'azun yadace?.
            Tsaki yaja tareda yatsine fuska tamkar Wanda yaga kashi, ya ce, "ke awa? dabazan miki abu agaban Rahma ba?.
   Ya nunata da d'anyatsa wlhy kifita hanyata, karki yarda kibari na nunamiki asalin colour d'ina, ina d'aga miki k'afane saboda 'Yar uwarki, amma zakisha mamaki idan kikacigaba da bibiyata.......
    Kafin ta ce, " wani Abu yaja motarsa yafice, dama tuni mai gadi yabud'e masa gate.
    Hawaye suka kwararo afuskar safna, wani d'an lungu tasamu dagacan baya ta zauna, saida tad'anyi kuka sannan tad'auki waya takira baseera, bata d'agaba takuma kira nanma haka, ajiye wayar tayi tazabga tagumi cikeda damuwa.
  
Su Rahma suna ciki basusan bikin da akeba, bayan sungama ware kayan da ammi tasakasu suka dawo falo wajen sauran 'yan uwansu suna hira, saidai hankalin Rahma yana kan tunanin ina aunty Safna?, gashi batason tashi Dan gudun karsu fahimci halin datake ciki, tasan ko kowa bai tanka tafiyartaba sai aunty Rasheeda tayi magana, Dan tun d'azu take binta da kallo, itakam idan antambayeta batasan amsar dazata bayarba.

     Da sauri Safna ta kalli wayarta ganin Baseera CE yasa tad'auka da hanzari, ko gaisuwa bata tsaya sunyiba ta ce, ''kekam baseera ina kika Shiga haka inata kiranki tun d'azun?.
     Safna muna lectures ne, kinsan ba'a d'agama sir hamza waya idan yana lecture, waimi yahanaki zuwa school yaune?.
     Wlhy babu komai hakanan naji banason zuwa.
   Lallai kinyi wauta Dan wlhy sir hamza yayi test yanzu.
   Ke babu damuwa aii ina gidansu, kinsan ankusa bikin k'annenesu nextweek, to muna gidan ana shirye².
      Hummm ALLAH yasa yad'aga miki k'afa to, Dan wlhy ya CE........
     Da sauri Safna ta katse baseera kenifa bawannan bane damuwata, nakirakine muyi magana.
    To inajinki baseera tayi maganar tana zama kusada zeenat data fita harkarsu tuntuni dantaga sunyi nisa basa jin kira, idanma zasuyi k'ulle k'ullensu basaya akusada ita.
      Safna ta ce, "baseera wlhy inacikin matsala."
    Matsala kuma kamar ya?.
    Safana tafara zayyanama baseera abinda yafaru tundaga Daren jiya da motarta ta lalace harzuwa abinda bobo yamata yanzunnan.
     Jinjina kai baseera tayi sannan tad'an kalli zeenat dake karatu amma hankalinta na Kansu kuma tanajin duk abinda safna ke fad'ama baseera awaya, baseera ta ce, "lallai safna bakida wayo wlhy, keyanzun harya sakaki dafa ruwan zafin Gaza Rahma amma ki Gaza ganewa?, kumafa k'uru k'uru yafito yace miki Rahma tagirma amma duk Baki ganeba.
    Safna tad'an ta6e baki baseera ban... bangane kema mikike nufiba aii.
    Tsaki baseera taja tana fad'in aikin banza, asheke zaman banzama kikeyi agidan, ayanzukam kid'auka bobo yamiki nisa wlhy dankuwa adaren jiya ya angwance kenan.....
    Agaban safna yafad'i cikin masifa ta ce, " baseera karki k'ara 6atamin rai kema banason fatan tsiya, taredakefa malam da'u yacemana yaturomusu aljani dazai hana ya kusanceta.
    Baki baseera ta ta6e ta ce, "wannan zancekam yazama labari tunda bobo ya aikata hakan ajiya, saidai kuma kujira result d'in ciki.
    Kuka wuy wuy safna tasaka tana kuran tashiga uku bobo yaci amanarta itakam rayuwarta tazo k'arshe garama tamutu ta huta.
    Tsaki baseera tayi tareda yanke wayar tana fad'in 'Yar wahala keni nagaji da matsalolinki, wlhy da bobon zaice yana sona nimafa sonshi nakeyi harma nafiki Dana kula yamin nisa saina hakura, amma nakula ke kinkasa ganewa *_" ANNABI"_* yafaku, haba Dan ALLAH ayi mutum da tosashshiyar basira, idanma bakisaniba kisani dagani har malam da'un cin k'ud'inki kawai Mukeyi babu wani aiki dayake miki Dan tun farko yafad'amin komai wlhy, ya ce, "kwata kwata babu aure tsakaninki da bobo Dan bazaima sokiba.
     Zeenat tayi galala tana kallon baseera wadda da alama tamanta tana wajen shiyyasa taketa sakin zance babu (,) babu (.).
     Ganinfa da gsk tamanta tana wajen yasaka zeenat zungurar ta baseera kinsan mikike fad'a kuwa?.
     Figigit baseera ta kalleta saikuma tafara Kame kame au.. au.. Ummm zeenat dama kina nan?, Dan ALLAH kinji minake fad'a?, pls kirufamin asiri maganarnan tatsaya dagani saike Dan ALLAH, kitaimakeni Zeenat wlhy su6utar bakice.
    Girgiza kai kawai zeenat tayi tamik'e tabar mata wajen Dan wlhy yau bak'aramin tsoro baseerar tabataba, lallai maganar Sajna gsky CE datace *_wata k'awar tafi guba_*, itakam yau ta shaida akan baseera, idan bata mantaba baseera CE tasaka safna ahanyar bin malami da bokaye, amma Ashe tanacan tahad'a baki da bokayen sunacin dunduniyar safnar, ALLAH ma ya k'ara, aiduk Wanda baiji bariba yaji hoho, babu irin nasihar da bataima safna ba amma tak'i saurarenta daga Bayama daina mata magana tayi wai bata k'aunarta, toga baseerar datake d'auka tana k'aunarta d'in nan tajefata arami mai zurfi kuma mai duhu, aii duk Wanda yagagara yima iyayensa biyayya to yanatareda gamon wahala, to ita baseera CE gamon wahalarta kuwa.
     Ganin baseera tanufota yasakata saurin yin gaba.
    Da gudu baseera tacimmata kuwa.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now