21

3.4K 222 0
                                    

             💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 22

waye Alh Sunusi dala?._
      Alh sunusi dala rik'ak'k'en d'an siyasane, kuma d'an kasuwa Wanda yay zarra akan canjin Dala, matarsa d'aya haj Falmata da yaransu hud'u, Surayya itace babba yanzun haka tayi aure yaranta biyu, sai Haneef shikam babuma auren a tsarinsa, sai Hafeeza da Shareefa suduk 'yammatane.
   Alh Sunusi bashida kirki ko kad'an, mutumne mai matuk'ar had'ari, idan yanason Abu zaibi takowace hanya ya sameshi, yana matuk'ar Son Haneef kasancewarsa shikaid'aine d'ansa namiji, sosai Haneef yad'akko halayen mahaifinsa harma yaso zartashi, Dan Haneef tamkar d'an bunsuru yake wajen Neman mata, idan yakwafama mace tota shiga uku, kasancewarsa k'yak'yk'yawa gakuma kud'i saiya zama 'yammatan dakansu suke kawo Kansu gareshi, Ak'alla Haneef yakai shekara 36 amma yak'iyin aure sai iskanci da ta6ara.
   Kwata kwata haj Falmata bata k'aunar halin d'an nata, kullum cikin yimasa nasiha take da nuna masa kuskurensa, amma yayi burus da zancen nata acewarsa har yanzu bata wayeba.
   Halin Haneef da haj Falmata take k'yamata shine yasa Alh Sunusi yake ganin bata son Haneef d'in kwata², aganinsa tafison yaranta matane.
     Itadai kullum cikin nuna fasa ba haka bane take, amma baya ta6a saurarenta, Dan haka tazuba musu ido shida Haneef d'in.
   Yaranta mata duk halinta suka biyo, suma basa k'aunar halin babansu da d'an uwan Nasu, amma babu yanda zasuyi saidai addu'a kawai.

Toyanzu mugun halin Haneef yaja masa Shiga tarkon bobo, shikam bobo karanbani yaja masa shiga tarkon mahaifin haneef, Alh Sunusi dala, toko waye keda nasara?.
   Saimun cigaba dabin labarin zamu tabbatar.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
        K'afar Rahma ta warke, amma tasha bak'i 'yan dubiya, ammi kanta saida tazo dubata, Matansu ya Ishaq ma haka duk sunzo, harsu ya ishaq d'in kansu.
   Itakam daga Rahama saitace gara dataji ciwon, Dan kobabu komai acinkin kwana ukun kullum gidan yana cike da dangi asha hira, su khursiyya kuwa kullum suna gidan.

Kwata² tadaina gyarama Bobo d'akinsa, tun ranarma bata sake kallon ko hanyar d'akinba, su khairiyyane suke gyara masa idan sunzo.
   Dama bawani shiga harkarsa takeba, to akwana ukunnan ma talura yana matuk'ar busy, Dan kullum yana danna laptop, wani sa'inma saiyakai 10 baidawo gidanba.
    Dukda abin na damunta tanason kuma tambayarsa abinda ke faruwa?, amma tana tsoron wulak'ancinsa, Dan haka ta shareshi itama, tanadai tayasa da addu'a samun nasara akan abinda ya burkitashi haka.

+++
    A6angaren bobo kam ya ajiye komai gefe, gaba d'ayan hankalinsa yabada akan shari'arsu da Haneef, bak'aramin shiri yayma shari'arba, Dan yayi bincike na musamman akan halayyar haneef, wannan yasa yakeson ceto sauran yara daga gudun fad'awa tarkon Haneef d'in na gaba, Dan ance mai halin bata barin halinsa.
       Tun washe garin daya kai Rahma asibiti taga muheebat kuma yaji tasanta, da safe yakar6i address d'in gidansu Idris, tare sukaje shida ya Hamza da ya sulaiman har gidan suka maida muheebat.
    Dangin hebba sunyi murna da dawowarta garesu, sunkuma sakama su bobo albarka gameda taimakon dasuka bama yarinyar, saidai sunyi kuka sosai akanjin k'addarar data afka mata.
   Nansu ya Hamza sukaita lallashinsu, sukace sukwantar da hankalinsu zasu kwatoma Hibba hak'inta dukda dai budurcinta yatafi bazai dawoba.
    Sunji dad'i sosai tareda yimusu k'yak'yk'yawar addu'a.
     Bobo ya ce, " zamu tafi, amma ga no. d'ina Indai dawata Matsala sai'a kirani, sannan akan rashin maganar heeba d'in kodama tanada wannan matsalar?.
      Eh damacan bata iya magana tun bayan ciwon k'yanda datayi lalurar ta sameta, amma tanajin abinda ake fad'a cewar baba Hamisu mahaifinsu hibba da idris.
     ALLAH sarki, amma baba kunta6a d'aukar mataki akan hakan?. Dr sulaiman ya tambaya?.
    A'a yaro, gsky bamuta6a yiba kasancewarsa kada muyima ALLAH shishshigi.
    Hakane baba amma yana da k'yau anema mata magani, Dan naga zata iya samun lfy, ban yimata aikin bane dama saboda inaso saida izininku, amma insha ALLAH zamu yimata wani aiki komai zai dawo daidai, Dan matsalarta bata cika tsananiba.
   To shikenan mungode ALLAH yasaka muku da alkairi, yayma Rayuwarku albarka, ALLAH yajik'an mahaifa.
   Ameen suka fad'a suna mik'ewa, sukai musu sallama suka tafi akan sai suhad'u a kotu ranar talata.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now