19

3.1K 212 0
                                    

             💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 20

washe gari

  Rahma tatashi tayi duk abinda tasabayi dukda tasan yau weekend Bobo bazai fitaba, tana cikin saka turare a falo bobo yafito sanye da jallabiya ruwan toka mai gajeren hannu, rissinawa tayi ta gaidashi, kamar yanda yasaba ya amsa da lfy.
    Amsa gaisuwar nan nabama Rahma haushi, amma babu yanda zatayi.
   Yad'anbi falon da kallo komai tsaf, gawani k'amshi na musamman, yana jin dad'in kasancewarta mace mai tsafta.
   Itadai cigaba tayi da abundan takeyi.               Ya ce, "bari nad'anje wani waje nadawo.
    Aranta tace kofa wanka bakayiba, amma afili ta ce, " to ga Break.
   No barinaje nadawo, aiba dad'ewa zanyiba, yafad'a yana ficewa.
   Itama ta ce, "ALLAH ya tsare.
   Dukda yafita amma yajiyo addu'arta.

Bayan takammala saka turaren zuciyarta tabata shawara dataje ta gyara masa d'akinsa, kamar bazatajeba saikuma tatuna nasihar mahaifiyarta da ummansu Basma.
   d'akin tanufa da tunanin ALLAH yasa bai rufeba, tana tura k'ofar tabud'e, k'amshinnan yana nan kamar kullum, yau tanutsu takalli ko ina na d'akin, komai farine tas, aranta tace farin Abu name tsaftane.
     Sai manya manyan hotunanan Ni'ima Maman Nawal, bani gurin ita kad'a, wani gurin kuma shida ita.
     Ko kad'an bataji haushiba bare kishinta, Bata 6ata lokaciba tafara gyara ko ina, Dan danan tagama d'akin yak'ara d'aukar haske komai yana d'aukar ido.
    Bathroom tashiga zata wanke saitaga kaya ajik'e abokiti.
    Shiru tayi tana tunanin ta wanke kota barmasa abinsa, wata zuciya ta ce, " ki wanke, kobabu komai zaki samu lada aii.
   Haka tazauna tahau wankin gajerun wandunansa da vest, akunyace take wankin tamkar tana gabansa, gudu gudu sauri sauri tagama bataso yazo yataddata tanayi.
   Dandanan tagama tawanke bayin, tad'auki kayan tafito waje, acan baya taje tashanyasu sannan tadawo d'akinta tashiga wanka, Dan Nawal bata tashiba.
  
Shigarta wanka babu dad'ewa yashigo gidan, d'akinsa yanufa kai tsaye, baki da hanci da ido yasaki yana kallon d'akin NASA, yalek'a bayi nanma fes, bokitin daya jik'a kaya wayam, wani lallausan murmushi yasaki, labulen window d'insa yad'aga, can yahango kayan ashanye.
   Jiyay wani Abu nata6a zuciyarsa, afili ya ce, ''ALLAH yaymiki albarka.
   Fitowa yayi yanufi d'akin Rahma, hakan yayi daidai da fitowarta daga wanka, daga ita sai guntun tawul iya cinya.
   Wata tsayuwar sojan badakkare bobo yayi, sai Raba idanu yake akan Rahma, da wannan munafikin kallon nasa k'asa k'asa.
    Itakam dukta rikice, waige waigen abinda zata rufe jikinta kawai takeyi, can ta hango hijjabin sallarta, amma dole saitabi tagabansa zata d'auka, ganin haka saikawai takoma cikin bayin da sauri.
   Murmushi yayi tareda sauke ajiyar zuciya, yak'arasa inda hijjabin sallarta yake yad'auka, ahankali yak'arasa har k'ofar bayin ya kwankwasa, Rahma dake jingine da k'ofa tagwalo ido waje, k'irjinta sai dukan Tara Tara yakeyi.
   Yak'ara kwankwasawa.
   Muryarta narawa tamkar zatayi kuka tace yes, yanda tayi maganar tabashi dariya amma saiya gimtse ya ce, "bud'emin k'ofar.
     Innnalillahi tace azuciyarta, wai mi mutumin nan yake nufi.........maganarsa ta katse mata tunani, " wai kobaki jinane?.
   Bayan k'ofar takoma tala6e sannan tabud'e, gaba yay tamkar zai Shiga, saikuma yamik'a mata hijjabin, dasauri takar6a tamaida k'ofar burum tadatse.
   Girgiza kai yayi yanad'an ta6e bakinsa, yazauna bakin gadon yana shafa kan Nawal daketa barcinta hankali kwance, shi mamakin kansama yakeyi, wai miyake jirane?, zuciyarsa ta ce, "kanason sake kallon Rahma ne.
   d'an tsaki yaja yamik'e yafice, shi adole zuciyarsa tayi k'arya.

Saida taga yafita sannan tafito, taje tasakama k'ofar key, sannan tazauna tagyara jikinta, tasaka Riga da wando na Pakistan, nakula tana son irin kayannan sosai.
   Nawal ta tashi itama tayimata wanka tashiryata cikin wandon Jin's da pink d'in T shert mai k'yau.
   Falo suka fito, fitowarsu babu dad'ewa shima ogan yafito, haryayi wanka yashirya cikin jins blue da farar Riga sai zabga k'amshi yakeyi.
   dinning suka nufa, Rahma sai sinne kai takeyi Dan kunya, shikam ko'a kwalar rigarsa, yanacin abinci Nawal namasa surutu, iyakarsa Yamata murmushi koya d'aga kai.
   Rahma ta ce, " azuciyarta, muskili kafi mahaukaci ban haushi.
    Suna kammalawa Nawal taja hannun Rahma wai suje tamata lilo, fitowa sukai sukabarsa kwance saman doguwar kujera yana kallon film.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now