30

4.1K 225 1
                                    

            💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 31

Tana cikin kichin zaune danta kasa fitowa, jitake kamar su khairiyya sunsan miya faru, ihun Nawal ne yasakata fitowa dole, tasaki su khursiyya tanufo Rahma da gudu tarungumeta tana murnar ganinta, tana cikin cire mata uniform bobo yafito sanye cikin farar jallabiya, Shima Nawal taje ta rungumesa, yad'agata sama yana fad'in babyna yaushe kika dawo?.
    Papa yanzun nan.
Toya school?.
  Lafiya lau my papa.
    To masha ALLAH sauka naje masallaci yafad'a yana direta k'asa, ya kalli Rahma datun fitowarsa tayi k'asa da kai, ya ce, "bara naje sallah.
   Saika dawo tayi maganar kanta ak'asa.
    Baice komaiba yafice.

  Yaudai haka Rahma tawuni atakure Dan duk inda tayi idon bobo yana kanta, ko kunyarsu khursiyya bayaji.
    Bayan sallar isha'i yashirya zai maidasu khairiyya Nawal tamak'ale wai saitaje, harsun fita yaturo Nawal takira Rahma itama tazo su tafi.
   Murna tayi sosai Dan dama tsoro takeji wlhy.
    Abaya ta tararda su khursiyya, dole tabud'e gaba tashiga, har Nawal zata shigo gaban ya ce, " takoma baya, Rahma tadaure ta ce, "pls kabarta muzauna aii zai ishemu.
    Baice komaiba yatada motar, saida yafita daga gidan sannan ya ce, " kina 'Yar lukutarnan ne kujera d'aya zata isheku?.
    Da sauri tajuyo tana kallonsa, amma shiba ita yake kalloba, idonsa nakan titi, d'an harara tamasa tareda murgud'a bakinta.....
    Babu zato ya ce, "nikikema murgud'e da harara?.
    Kanta tadafe Dan batasan yana kallontaba, aranta ta ce, " kai mutumin nan ya iya munafikin kallo wlhy, afili kuma ta ce, "nifa ban hararekaba, tak'are maganar da turo baki gaba.
    Murmushin gefen baki yayi batareda yace komaiba.
      Tunda suka shiga harabar gidan sukai karo da motoci reras, wannan alamace ta basawan gidan duksun zo kenan, shima guri yasamu yay fakin suka fiffito.
     Yana gaba suna biye dashi, da sallama suka shiga falon daya k'awatu da haske.
  Ya sulaiman ya ishaq ya Hamza duk suna gidan, hannu bobo yashiga basu suna gaisawa, su Rahma ma suka gaishesu tareda hayewa sama Dan gaida Ammi.
   Ya Hamza ya ce, " kace tare kuke gaba d'aya, bobo dake k'ok'arin zama ya ce, "yana iya baby tamak'ale saitazo, nikuma bazan iya barin Rahma ita kad'aiba shine na ce, kawai tataho mu tafi.
   Ya ishaq ya ce, " kai bobo banwani yardaba, kaid'innan baban soyayya.
   Murmushi bobo yayi ALLAH Yaya kunyi bala'in sakamin ido agidannan amma babu komai dukzan ramane.
   Dariya sukayi gaba d'aya ya sulaiman yad'an daki kafad'ar bobo yana dariya, autan Ammi barsu kaji, sumafa suna soyayyarnan.......
   Sakkowar Ammi daga sama ta tsaida dariyar tasu, bobo yarissina ya gaidata, bayan sun gama gaisawa ta ce, "tom kutaso Appan naku yakammala.
    Gaba d'aya suka mik'e abin sha'awa da burgewa, cikeda fara'a Appa yatari matasan samarin 'yayan nasa, suma duk suka zauna suka zagayesa, Ammi ta ce, "to akawo abinci ko?.
    Kowa ya CE, " a'a.
Appa ya hararesu bangane a'a ba, tuni nak'icin abinci saboda nasan zakuzo shine yanzu zakuce wani A'a.
   Dariya sukayi sukace to akawo ko kad'an suci.

    Tare sukaci abinci da Appan su, bayan sun kammala sukashiga tattauna abinda yakawosu, dama akan bikinsu Khursiyyane, antsaida sati hud'u kacal, dama shi Appa haka yake saka bikin yaransa bayaso danisa d'innan, anan take suka tsara komai data dace, kowa yad'auki abinda zai iyayi, Appa sai sakamusu albarka yakeyi shida Ammi, daganan hira sukad'an k'ara ta6awa sannan suka mik'e zasu wuce, bobo ya ce, "Ammi ina yarannan muwuce.
      Suwaye yara? Ya ishaq yatambayi bobo.
     Rahma da Nawal.
    Lah matarka kakecema yarinyar? cewar Appa.
    Dariya sukayi gaba d'aya, bobo  kam murmushi kawai yayi, ya ce, " Appa yarinyace mana shekarartafa 17.
    O Dan shekararta 17 saika ringa cemata yarinya?, to aii yanzu tagirmi wannan sunan, cewar ya Sulaiman.
     Bobo yaturo Baki gaba nidai kunga tafiyata saida safe, suduka dariya suka saka harda Appa da Ammi shidai yayi tafiyarsa d'akin Ammi, a can kuwa yasamesu sunata rubuce²  itadasu kahiriyya yana shigowa suka 6oye, kallonsu yayi ya ce, "mikuke 6oyewane?.
      Babu komai Rahma tayi maganar dasauri tana mik'ewa, yasan basuda gsky amma yayi fitowarsa yak'yalesu, azatonsa ko tsare tsaren biki sukeyi.
    Rahma tad'auki Nawal datayi barci, saida taje tagaida Appa tamusi sallama sunata sakamata albarka sannan ta iske bobo aharabar gidan shida sauran 'yan uwansa.
    Mota tashiga tajirashi, bayan sun kammala kowa yashiga mota sai gida.
    Tunda suka tafi babu mai magana, daga Rahma har Nawal barci sukeyi, dahakadai suka k'arasa gida, harya kashe motar yafito babu Wanda yamotsa, yaduk'o yana kallonsu Yoshi yanzu yama zaiyi dasu?, d'an tsaki yayi yad'auki Nawal yanufi cikingida, har d'akinsu yakaita ya kwantar bisa gado sannan yadawo, azatonsa zai Tatar Rahma ta tashi amma INA barcinta taketa shek'awa da Alama kuma yanamata dad'i.
    Aransa ya ce, " kegaki orobo amma sai son d'auka.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now