27

3.3K 207 1
                                    

             💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 28

Washe gari Safna sukayi sammakon tafiya wajen malam da'u, yauma dai k'arya tashirya ma Abba da ummi harta samu damar fitowa da sanyin safiyarnan.
    Ak'ofar gida suka had'u Baseera tabud'e tashigo.
   Kallon safna take cike da mamaki, Safna kinga kuwa yanda idonki ya kumbura?, amma dai kinyi kuka?.
   Humm baseera kenan, aii jiya kukan jijine kawai banyiba wlhy, amma fa yanda naga rana haka naga dare, nayi nadamar zuwa gidan banzar yarin yarnan jiya, Dan dabanjeba dabanyi gamo da abinda zai dameniba, amma kuma hakan alkairine Dan koba komai naga farin cikina, nakumasan Inda zan sameshi yanzu, ta k'are maganar da share hawaye.
   Kiyi hak'uri kibar kuka, komai zai daidaita nasan aikin malam da'u saikinyi farin ciki.

“nikam na ce, "shi d'in banza, shima ga ALLAH yake nema”.
     Mtsoooooow!!.

Suna tafiya sunad'an hirarsu, baseera ta ce, " amma ummi bata saniba ko?.
   Kai yazanyi tasani, kinsanma kuwa yanda takeji da shegiyar Rahma d'innan yanzu, kenifa inaga duk cikinmu ummi tafison Rahma ayanzu.
      Kai Safna aiiko bazakice hakaba, duk gidannan babu Wanda akaima gata sama dake, kitunafa, ummi tabamu labarin tunkan tayi aure take addu'ar ALLAH yasa tahaifi mace haihuwar farko, amma ALLAH saiyabata maza, bayan ummi ta haifi ya Shaheed da ya Munneer taso haihuwar mace sosai, saikuma haihuwar tatsaya ma gaba d'aya, saida ya munneer yay shekara 7 sannan ALLAH yabata cikinki, kullum itace addu'a da sallar dare, har umara sukaje itada Abba saboda ALLAH yabasu 'ya mace.
    ALLAH mai k'yauta da k'ari aka silli6oki duniya, gatadai kinshashi fiye da kowa agidan, abinda kikeso shi ake miki, shiyyasa kika taso 'yargata ta6ararriya, wlhy tsiyar dakikeyi agidanku Inda Rahma takeyinta datuni tashiga wani hali.
   Amma harzaki bud'i baki kice anfison Rahma, duk Wanda yasan tarihin gidanku to bazai yarda da maganar kiba wlhy.
    Shiru Safna tayi, Dan tasan gaskiya Baseera tafad'a.
   Da hakadai suka k'arasa gidan malam da'u.

°*°*°*°*°*°*°*°*°*°*°
         Tunda tatashi take hidimar gyaran gidan, bayan tahad'a breakfast tayima Nawal wanka tashiryata tsaf cikin kayan makaranta, tsaf yarinyar tafito tamkar kasaceta ka gudu, dama ga k'yau d'an asali, tana girma kamaninta nasake fitowa da mahaifinta.
   Rahma ta kalli agogo 7:6am, ta ce, "baby bara nayi wanka nima kafin papa yafito.
    To momy, Nawal tayi maganar tana k'ara gyara igiyar takalminta.
   Cikin d'an lokaci k'alilan tayi wankan tai shirinta cikin siket da riga 'yan kanti, d'an tsaki tayi Dan ganin rigar batada tsawo, aranta tace yanzu kanayin kuskuren d'aga hannu sai anga cikinka, da wannan mitar aranta suka fito falo.
    Harta zauna a dinning itada Nawal saikuma tamik'e Dan hangen labulen windown Kusada su ya nannad'e.
    Wani d'an kujera dake gefe wadda Bobo kan zauna idan baya buk'atar hayaniya ta janwo ta taka Dan tsawonta bazai kaiba, hawanta keda wahala koma labulen bata gyaraba tadai mik'a hannu zata gyara taji takun fitowarsa kwass kwass, tsintar kanta tayi da k'urama hangar tahowarsa idanu.
    Ya salam tafad'a yayinda bobo yabayyana, sanye yake cikin wando dariga farare tas, ya d'ora rigar suit jaa mai laushi, takalminsa agogonsa duk jajayene, sai zabga uban k'amshi yakeyi, sajen nan yakwanta luf luf sai shek'i yakeyi.
    Tashagala sosai akallonsa batareda tasaniba, shima gareshi hakan take, tsaye yake k'yam tamkar andasashi, idonsa nakan farar fatar cikinta data bayyana sakamakon d'aga hannu datayi zata gyara labulen daya nannad'e.
    Ganin ya motsa yasa ta firgita, abisa tsautsayi kukerar tad'an goce tayi baya kamar zata fad'i amma tayi nasarar rik'e k'arfen window.
    Ahankali yatako har inda take, fuskarsa babu yabo babu fallasa, baya murmushi bakuma a d'aure takeba, ahankali yayi maganar tamkar bayaso ko ammasa dolene.
    Mikike kallo haka? Dahar kike shirin fad'uwa?.
   Turo baki Rahma tayi, danta gaji wlhy, gashi Idan ta ce, "zatayi yunk'urin sauka fad'owa zatayi, Dan kad'an k'afarta take d'ofane akujerar.
    Yanda ta turo baki cikeda shagwa6a saita k'ara burgesa, dama ga kwalliyarta ta tafi dashi, yad'an lumshe idanunsa ya bud'e akanta, bazakiyi maganaba ko?, Ashe zan barki kifad'o d'iyarki tamiki dariya, yayi maganar yana kallon Nawal da hankalinta baya kansuma gaba d'aya, wasanta takeyi da cokulan da Rahma ta ajiye a dinning.
     Dawo da kallonsa yayi ga Rahma, cikin sanyin nan NATA tareda shagwa6a ta ce, " ALLAH hannuna zai karye please help me.
    Wani k'asaitaccen murmushi yayi tareda ajiye jakar aikinsa, yatura hanuwansa duka biyu a aljihu, idan na taimakeki kedami zaki biyani?.
     Shiru tayi tana kallonsa, can kuma ta ce, "mikake so nabaka amatsayin ramako?.
    Yad'an d'age kafad'a yana ta6e baki, nikomi kika bani fine.
    Ta marairaice murya tamkar zatayi kuka, ALLAH nagaji zan fad'o.
   Kauda kansa yayi gefen Nawal yana murmushi, ganin har yanzu hankalinta baya kansu yad'auke kai. Matsowa yayi Kusada Rahma tareda zare hannunsa daga aljihu ya tallafota, daga ita harshi lumshe idanu sukayi, tallafota yayi tamkar jaririya, ahankali yabud'e idonsa akanta, amma ita har yanzu nata alumshe suke, yakalli k'irjinta dayayi d'as a pink d'in rigar, ajiyar zuciya yasauke sannan yadireta ak'asa, saiyanzu tabud'e idanunta masu matuk'ar burkitashi, thanks tafad'a tana k'ara juya idanun.
   Shi ganima yake tamkar da gayya tamasa haka, lumshe idanu kawai yayi yana jinjina kai Dan bakinsa yayi masa nauyi, cikin salonsa ya ce, " nawafa?.
   Ta ce, "me?.
Ramakona mana, kokin manta da yarjejeniya mukayi.
    Kauda fuskarta tayi gefe Dan bazata juri kallonsaba, mikaso to?.
     Abu biyune kawai, kuma marasa wahala.
   Kafad'a inji idan zan iya.
    Nafarko dai gyaran d'akina, Dan yayi datti, nabiyu kuma..... Saikuma yayi shiru, tajuyo tana kallonsa miye na biyun?.
    Wani murmushin basarwa yayi, murya kasa k'asa ya ce, " kiss me".
    Idanu tazaro, saikuma tajuya zata gudu, da Sauri yadamk'o hannunta, tsayawa tayi cak amma takasa juyowa.....
     Momy papa!!!!. Zanyi latti fa.....
    Muryar Nawal ta riski kunnuwansu, da Sauri yasaki hannun Rahma, itama tayi Saurin k'arasawa ga Nawal.
    Break fast tashiga had'a musu, Bobo yak'araso dinning d'in, kujera yagyara tamkar zai zauna yakai bakinsa Kusada kunnen Rahma, kitabbata idan nadawo saikinyi, inba hakaba zanmiki abinda yafi kiss.
   Kafin tad'ago yaja kujera ya zauna.
    Dukta daburce, itafa mamaki bobo take bata cikin 'yan kwanakinnan, tamkar bashiba, awaje idan kagansa dolene kaji tsoronsa da masa kallon mutum mai Girman kai da tsabar shariya, amma daka zauna dashi nad'an wani lokaci saika fiskanci shi mutumne mai sauk'i da iya zama da mutane, tasauke ajiyar zuciya tareda tura musu abincin kowanne agabansa.
     Sunacin abinci yana mata munafukin kallon nan nasa, dukta takura awajen, adaddafe dai aka kammala suka mik'e.
    Takama hannun Nawal suka fice shikuma yana binsu abaya har wajen mota.
     Rahma ta rissuna taima Nawal kiss akumatu kamar yanda tasaba, itama Nawal Tamata, bobo yak'araso yana fad'in saura ni.
    Shiru Rahma tayi tamkar bama tajishiba, bata ankaraba taji yabata  summba (kiss) akumatu, dasauri tad'anja baya tareda lumshe ido, saikuma tajuya dagudu zuwa cikin gidan.
    Murmushi yayi tareda binta da kallo harta shige ciki, shima yabud'e mota yashiga yana murmushi.
    Saida yafara ajiye Nawal amakaranta sannan yanufi wani waje.
    Adaidai wani k'ofar shago yatsaya, batareda yafitoba, yamik'a hannu ta windown shagon aka mik'o masa wasu takardu.
     “banga  fuskar wayeba nima.”
     burka motarsa yayi yay gaba yana bin karatun alkur'anin dake tashi amotar ahankali.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
     Su Safna sun samu shiga wajen malam da'u, bayan gaisuwa ta labarta masa yanda komai yafaru tundaga randa suka bar wajensa, duk cikin matsanancin kuka takeyin bayani.
   Shima Kansa malam da'u yarazana dajin batun na Safna, amma dayake yana son cin kud'i saiya dake abinsa.
   Ya ce, "toke yama akayi haka tafaru dake kika kamu dason mijin k'anwarki?.
   Safna tashare hawayenta, cikin rawar murya ta ce, " malam katuna da labarin farko Dana Baka, saikuma kahad'a Dana yamzu zakagane bansan  *_“ABADUL-MALEEK”*_ BOBO me iyayena sukaso na auraba, sai yanzu daga baya.
     Jin jina kai malam da'u yayi, ya ce, "lallai kinyi Sake yarinya, amma zanyi iya bakin k'ok'arina Dan ganin kin mallakesa, Dan naga itama bata sonsa shima haka, Dan haka zamuyi nasarar rabasu cikin sauk'i, kid'aukama kinzama matarsa kawai.
   Wasu kayan tsubbunsu yabata, yamik'a mata wani ruwa a 'Yar jarka, ga wannan duk yanda zakiyi to kiyi Dan yasha abunnan, wannan kuma acikin abinci, sau uku zakiyi duka, Indai har yaci Yakuma sha tozaice ke yakeso, kuma zai saki k'anwarki.
   Wannan kwallin kuma kiringa sakawa a idonki, kiyi k'ok'ari kuma Ku kalli juna ido cikin ido.

To malam ngd sosai Safna tafad'a tana washe baki, to amma malam duk tayaya zanyi wannan aiki nida ba gida d'aya mukeba?.
   Malam yayi dariya, kekam saikace ba maceba, kiyi duk yanda zakiyi ki aikata, wannan yarage naki, nidai nagama nawa.

Tunda suka baro gidan malam babu mai magana da wani tsakaninta da baseera, kowa da abunda yake sak'ama zuciyarsa.
   Safna dai tunaninta nakan yanda zataci nasarar ciyar da BOBO wad'an nan magungunan.
    Amma zata gwada wata dabara tagani.
  
*_(“ni bilyn Abdul na ce, " hummmmm, muje zuwa Safna.”)._*

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
       Jikake keyyyyyyyyyy yaja wani wawan birki da k'arfin tsiya Dan ganin wasu zaratan samari majiya k'arfi agabansa, sai faman huci suke suna mummurd'ewa, alamar jin karin k'aimi akan burinsu.
   d'an tsaki yaja tareda cije le6ensa na k'asa, afili ya ce, "wad'annan k'ananun karnukanfa nawaye?.

“na ce, " hummmmm.”

Murfin motar yabud'e cikeda Isa yafito, kuma fuskarsa tana nuna alamar hankalinsa kwance yake, yarufe murfin sannan yajingina ajikin motar, hannayensa yatura cikin aljihun farin wandonsa, ya hard'e k'afafunsa biyu dake sanye cikin Jan takalmi sau ciki mai k'yawun gsk, idanunsa sanye da siririn farin gilas, yad'an karkace kansa gefe yana k'are musu kallo d'aya bayan d'aya, shi dariyama suka bashi, Dan haka yasaki wani lallausan murmushi mai birkita ma'abocin kallonsa Wanda Ammar yasakama suna murmushin mugunta, Dan yafi bomb had'ari.
   Cikin muryarsa mai taushi da amo ya ce, ''yan samari halan lafiya dai?.
     Zaratan samarin suka k'ara babban k'aro k'irji gaba had'eda hura hancinansu danjin furucin BOBO maicikeda rainin wayo.
   d'aya daga cikin samarin ya ce, "lafiya idan kabamu abinda muke nema, amma babu lafiya idan kace zakayi kuskuren hanamu.
   Tofa, yafad'a yana k'ara sakin lallausan murmushi, lokaci d'aya kuma yahad'e fuska tamkar hadarin gabas, yasaka d'anyatsa d'a yajawo gilashinsa k'arshen hanci, saikuma yasakeyin murmushi, Yakuma gyara tsayuwarsa, ya ce, "to  yan samari miye buk'atar taku?.
    Kallon juna sukayi Dan aganinsu yaji tsoro, nafarkondai yasake yin magana, d'an uwa takardun dake cikin motarka Daka kar6a yanzu muke buk'ata.
   'Yar dariya yayi akaro na farko, yakai hannunsa na dama ya shafa lallausar k'asunbarsa ya ce, " tofa, aikin babbane Ashe, hannunsa yacire daga aljihu, yatako ahankali yak'araso har Inda suke, yakuma binsu da kallo d'aya bayan d'aya, sannan yamaida kallonsa akan mai maganar, Wanda nake k'yautata zaton shine ogansu.
   Cikeda Isa ya ce, "yan samari bayan takardu mikuke buk'ata?.
      Wata mahaukaciyar dariya babban yasaki, saida yayi mai isarsa, BOBO na tsaye yana binsa da kallo, shima yakalli BOBO cikeda izza ya ce, "d'an saurayi konace matashin lauya bama buk'atar komai bayan takardunnan dai, sukad'ai sun wadatar damu..............
    Kafin yarufe baki yaji wani shegen naushi akumatunsa na haggu.
   Tuni oga yazube ak'asa a sandare, BOBO yabishi da kallo yana murmushi tareda shafa gemunsa na gayu, 'yan samari har wannanma bakwa buk'atane????.
   Gaba d'aya sauran zaratan samarin sukayo kan BOBO, wani juyi yayi akansu saiga biyu ak'asa.
    ����‍♀sum sum nakoma bayan motarsa namak'ale kafin a maujeni���� kurasa mai d'akko muku rahoton kuma.
     Tabd'ijan masu karatu nifa azatona a film kawai ake irin wanga Abu, Ashe afilima anayi, cikin 'yan mintuna saiga 'yan samarin nan kwance ak'asa gaba d'ayansu.
   Daga mai karyayyen hannun saimai karyayyar k'afa, saimai zubabben hak'ori.
    Amma gwarzon naku ko zoben dake yatsansa bai fad'iba barema ayi zaton yaji ciwo.
    Yataka hannun wani yana tsaki mtsowwwwww shashashu k'ananan karnuka kawai.... Uban waye ya aikoku gareni??, Ku karnukan farautar wayeeeee!!!!!!?. Yay maganar cikin k'araji!!!!!..............
  
  " wayyo masu karatu, tsawar BOBO tarazanani, tuni nakwasa da gudu na6uya bayan wata bishiya, inaga kuyi hak'uri kawai zuwa gobe idan nasamu nutsuwa saina idabaku rahon yanda BOBO yak'are da karnukan farautarnan kamar yanda yake fad'a musu........

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now