46

3.6K 199 0
                                    

            💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 47

Ganin yanufi wata hanya daban yasa Rahma tsura masa idanunta dasuka k'ank'ance saboda kuka, yana kallonta tagefen ido kuma yakula magana takesonyi amma takasa, shima bai iya cemata komaiba, gudu kawai yake shararawa, ganin sunshigo cikin asibitin Rahma takuma yarda mafarkinta ya tabbata, guri bobo yasamu yay fakin kowa yafito jiki a sanyaye, banda Nawal dabatasan wainar da'ake toyawaba, cikin asibitin suka shiga kowa da abinda yake sak'ama zuciyarsa, Rahma takan share hawaye lokaci lokaci.
    A Reception suka tsaya bobo yakira ya shaheed.
    Babu dad'ewa saigashi yazo, Rahma tana ganinsa tafad'a jikinsa tana kuka, cirota yayi daga jikinnasa yana fad'in haba Autar Ummi bakisan kin girma bane?, kinga share hawayenki kinji.
   Cikin shashshekar kuka ta ce, ''yaya waye bashida lfy?.
   Ya ce, "safna CE."
K'ara share hawayenta tayi ta ce, "yaya nasamma aunty Safna tarasu ko?.
   Idanunsa yazaro ya CE, "haba auta wayace miki tarasu?, a'a tana nan da ranta har yanzudai tana tareda doctor's ne.
    Ta share hawayenta tana kallonsa, to yaya miya sameta?.
   Muma bamu saniba Rahma saidai idan likitoci sun fito muji.
   To muje kokin manta bake kad'ai baceba?.
   Ita saima yanzu ta tuna tare suke da bobo Dan haka takalli Inda yake tsaye rik'eda hannun Nawal dake kuka tunda taga Rahma na kuka.
   Da sauri tazo taja Nawal jikinta ta rungumeta tana lallashi, bobo dai da ya Shaheed suna tsaye suna kallonsu.
     Ganin abun bana k'are bane yasa bobo matsawa kusada ita ya CE, " yakamata mu k'arasa ko.
    d'agowa tayi ta kalleshi saikuma takama hannun Nawal suka shiga ciki.
   Acanma tana ganin su Abba taje tafad'a jikinsa tana kuka, dak'yar ya lallasheta tayi shiru, bayan sun gama gaggaisawa suma sukabi sahun 'yan zaman tagumi.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
       Har akayi sallar magriba likitoci nakan Safna, su bobo dasu Abba suka nufi masallacin cikin asibitin,  sudai su ummi da matansu ya Shaheed duk suna nan zaune jigum jigum, Nawal kam tuni tayi barci, ummi taciro d'ankwalin kanta dayake yanada girma tabama Rahma ta ce, "ta Goya Nawal, amsa Rahma tayi tacika umarnin ummi, gama goyon babu dad'ewa saigasu ya Muneer sun dawo daga masallaci, hakan kuma yayi daidai dafitowar doctors d'in kowa yana yarce gumi, da Sauri kowa yanufesu yana tambayar halinda safna take ciki, duk zame jiki sukai suka gudu akabar doctor Kaleel kawai, kallonsu yayi d'aya bayan d'aya yana share gumi, ganin duk 'yan gidane ya sauke ajiyar zuciya, ya ce, " Alhmdllh munsami nasarar ceto ranta, yanzu haka tasamu barci, yanzuma za'a wuce da'ita d'akin Hutu danhaka Ku kwantar da hankalinku alhaji, komai yazo da sauk'i aii alhaji, sauran bayani kuma sai zuwa gobe idan ALLAH yakaimu.

Alhamdllh suka fad'a gaba d'aya, godiya sukaima doctor Kaleel sannan yawuce office d'insa.
     Tafiyarsa babu dad'ewa aka gunguro Safna a d'an gadon marasa lfy, kwance take sharkaf tana barcin wahala, cikeda tausayi da addu'ar samun lafiya suka bita.
    Zuwa yamzu fuskokin kowa garage damuwa bakamar d'azunba.
    Bobo yamatso kusada Rahma ya ce, "My Nusfulhayat ki sauketa mana, aii yanzu Nawal tawuce goyo karkizo k'irjinki yana ciwo.
    Girgiza MASA kai tayi ta ce, "bafa tada nauyi ALLAH.
     YA munnir dake kusadasu yana jinsu ya ce, "aidama gida kuka tafi tunda anga yanda jikin NATA yake.
    Abba ya ce, " gaskiyarka muneer, Abdulmaleek kutafi gida hakanan, kuma su Muneer kud'auki iyalanku Ku tafi gida saboda yara dakuka bari..
    Rahma ta turo baki gaba cikin shagwa6a ta ce, "Abba nidai anan zan kwana gsky.
     A'a auta bazai yuwuba, idan anbarki kin kwana anan mijinkifa, bobo yad'an shafa Kansa idonsa ak'asa ya ce, "Abba abarta ta kwana Indai Dan tanine babu wata matsala.
    A'a a aiba hauka akeba Cewar ummi dake Harar Rahma.
    Abba ya ce, "kutafi gida kinji auta, ALLAH yay muku albarka gaba d'aya, gobe idan ALLAH yakaimuma aii ranace ko.
    Bobo ya ce, " to Abba bara muyi sallar isha'i, Dan komun tafi a hanya zata riskemu.
   Eh gsky ne to kubari ayid'in.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now