35

3.8K 225 2
                                    

             💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 36

Ana cikin sallar isha'i safna ta shigo gidan, babu kowa afalon sai k'arar TV  tawuce d'akin Rahma suna sallah itada Nawal.
     Da sauri tadawo baya dan tanada tabbacin Rahma bata gantaba, kai tsaye wajen abincin kan dinning tanufa, ta bud'e abinci tayi barnad'e barbad'enta tamaida tarufe sannan tanufi d'akin.
     Zuwa sannan sun idar da sallah, Rahma ta ce, "kai aunty har hankalina yatashi wlhy, naga dare yafarayi kuma nakira wayarki tak'i tafiya.
     Safna ta ce, " ayya my lil motatace tasamu matsala gashi wajen babu network.
     To ALLAH ya kiyaye gaba.
    Ummi takiraki kuwa?.
    A'a safna tafad'a cikin kallon Rahma, miya farune?.
    Babu komaifa d'azu bayan tafiyarkine takirani wai Abba yanata fad'a yakamata ki koma gida tunda nasamu sauk'i, shine nace suyi hak'uri ayi bikinsu khairiyya saiki koma ko?.
       Numfashi safna ta sauke, azuciyarta ta ce, "su ummi fa kuna k'ok'arin 6atamin aiki, amma zanyi k'ok'ari acikin 'yankwanakin dasuka ragemin nayi duk abinda yadace, afili kuma saitayi murmushi haka yayi Rahma, abinda tafad'a kenan kawai tamik'e zata shige bayi.
     Bobo yak'arasa shigowa d'akin Dan tund'azun yana bakin k'ofa tsaye yana sauraren firar tasu.
     Safna dake k'ok'arin shiga bayi tajuyo tana kallonsa, suna had'a ido tasakar masa wani lallausan murmushi, ya Bob ngd fa da d'akkoni ALLAH yabar zuminci tak'arashe maganar da d'aga masa gira.....
     Bobo kam ya daskare atsaye miyarinyar nan take nufi?, agidan uwarwa nad'akkota d'in?.....
     Rahma madai kallon tuhuma take masa, Dan duk abinda Safna tamasa akan idonta, tuni idonta yaciko da kwalla saboda kishi, ita kanta batasan tanada kishi mai zafiba kamar haka, ta had'iye wani Abu mai d'aci daga mak'ogoronta, mik'ewa tayi tafice daga d'akin kawai.
      Da sauri yajuyo yabi Rahma da kallo harta fice, Nawal ma dabatasan bikin da akeba tatashi tabi bayan Rahma, daidainan Safna tafito daga bayi, murmushin mugunta tasaki sannan ta tako ahankali har zuwa gabansa, my jaan rago baya zama gwani, nasan kaima kana sona, amma bansan mike hanaka nunawaba?, so karka damu ni bana tsoron Rahma zan fahimtar da ita ta kurman bak'i, idan bata ganeba zan mata fassara.
     Tunda tafara maganar kallonta kawai yakeyi, yama rasa wane mataki zai d'auka akanta, kafin yafarga tafice abinta, haka shima yabi bayanta tamkar soko.
        A dinning suka tarar da Rahma da Nawal sunacin abincinsu, bobo yaja kujerar dake kusada Rahma ya zauna, itama safna tazauna akusa dashi suka sakashi tsakkiya, tunda suka fito ko Inda suke Rahma batama kallaba, abincinta kawai takeci.
      Safna taja filet tafara zubama bobo abinci, tunda yafahimci shiitake zubamawa saiya d'auki cokali kawai yafaraci acikin filet d'in Rahma.
     Abin yak'onama Safna rai, amma saita dake tafaracin abincin data zuba masan, Rahma kam koda bobo yasaka hannu a abincinta bata kulashiba, shikam mamaki take bashi Dan baita6a ganin fushintaba saiyau.
      Bayan sun k'are cin abinci bobo yamik'e zaitafi d'aki, Safna tai saurin cewa ya Bob maganarmufa ta d'azu?, kosai ka kaini makaranta gobe?.
     Juyowa yayi yana kallonta kamar zaiyi magana saikuma yafasa yajuya yatafi.
      Rahma tayi saurin share hawayen dasuka cika mata ido, ita tama kasa fahimtar inda maganganun Safna suka dosa, kuma takasa fassara yanayin fuskar bobonta bare tagane mike faruwa?.
      Hakadai takama hannun Nawal suka koma falo, kallo takunna musu sukeyi dukda ita hankalinta baya a wajen, hotunan mutane kawai take kallo, amma bata fahimtar komai.

Safna kam tana d'aki tanata zuba tsallen murna Dan dad'i aikobabu komai tasaka rud'ani atsakaninsu, gashi kuma yau bobo yaci abinci da maganin data zuba, tadaka wani tsalle tareda fad'in saini Safna ikon ALLAH, k'adangaruwar baking tulu nake, akasheni akar tulu, abarni na 6ata ruwan, takuma tuntsurewa da dariya.

Na ce, "hummm safna kenan ba girin girin badai tayi mai."

Bobo madai yana d'akinsa, sai safa da marwa yakeyi, yamarasa tunanin dazaiyi akan Safna da kaidinta, ganin Kansa ya tushe yad'auki waya yakira Ammar.
      Cikin zolaya Ammar yad'aga wayar, kaga barrister dodon 'yan iska, mijin Rahma baban Nawal ya yadai my guy?.
      Numfashi Bobo ya sauke tareda fad'in Ammar ajiye wasa gefe inaso muyi maganane.
         To inajinka Ammar yafad'a cikin gyara nutsuwarsa.
    Ammar wata matsalace agidana nakeson kanemamin hanyar maganinta danni kaina gaba d'aya ya kulle.
    Ammar ya ce, "kaida Rahma ne.
     A'a no Rahma batayimin komaiba yayartace Safna.
   Haba bobo tokai miya had'aka da safna kuma?, bayan kai yanzu mijin k'anwartane.
    Hakane Ammar ni mijin k'anwartane, amma yarinyar tana Neman shigowa rayuwata, yakwashe kaf abinda Safna tamasa yafad'ama Ammar, yanzun zancennan danake maka nadawo daga masallaci na Tatar tana barbad'a magani a abincinmufa, amma bata ganniba, Rahma kuma suna d'aki itada Nawal suna sallah.
     Ammar yaja wani gwauron numgashi, lallai yarinyarnan hatsabibiyace, to amma kunci abinci?, a tomizai hana, sammu yakanyi tasirine da izinin ALLAH, Dan haka zuba maganinta bazai hanani cin abinciba nikam.
    Hakane Abdulmaleek, ammafa natayaka murna da aurenka bai kasance da yarinyarnan ba wlhy.
   Aikodai nima haka naketa godema ALLAH akullum Ammar, Dan nasan da itace matar tawa nasan saita rabani da Nawal.
   Wlhy kuwa zata iya. ni yanzu hanya d'aya nake ganin mafita kuma maganin yarinyarnan.
    Da sauri bobo ya ce, " minene?.
    Maganinta  d'ayane Wanda zata gane lallai kamata nisa fintin kawau shine kayi k'ok'arin kusantar matarka, ka ajiye batun Barin Rahma sainan gaba, Dan wlhy Idan kayi sake sai shaid'aniyar yayarta d'in nan taci galabar rabaku nan gaba, Dan kuwa 6arakar ta hango har take iya tunkararka kasaki 'Yar uwarta ka aureta, inhar tabud'e ido taga Rahma daciki, tom dolene tasakama zuciyarta salama ko itace shigabar jaheelai ta duniya, kuma yakamatama ta tattara takoma gida tunda su Rahman sun sami sauk'i.
      Duk abinda kafad'a gsky ne Ammar, saidaifa gsky Rahma yarinyace.
    Ammar yay dariya to abokina yaza'ayi, yaran k'auye da'akemusu aure shekara 12/13 fa?.
    Hummm kai asuma mazan yarane shiyyasa.
     Wata dariyar shak'iyanci Ammar yasaki cikin dariya ya ce, "kaikuwa gaka k'ato ko?, so kabimusu yarinyarnan ahankali wlhy Dan nasanka sai a slow.
    Kai d'an iska saida safe, dankasamu nafad'a maka sirrina shine zakamin wulak'anci.
    Hhhhhhh haba angon Daren yau maida wuk'ar mana.
    Murmushi bobo yayi tareda yanke wayar yana fad'in kai Ammar mafa d'an iskane wlhy.
          Jiyayi zuciyarsa yayi wasai kamar anyaye masa damuwarsa, mik'ewa yayi yashiga bayi ya salla wanka tareda d'auro alwala, bayan fitowarsa yad'an shafa mai da turarur rukansa yazira doguwar Riga ya zauna yana jiran shigowar Rahma.
     Jareda yad'auka yana karantawa, saidai lokaci lokaci yakan kalli agogo, tun yana saran shigowarta harya fara mamakin miya hanata zuwa Dan 11:47pm, yad'anyi tsaki tareda gyara kwanciya yamaida Kansa ga jaredar, sai yakasa cigaba da karantawa, wayarsa yajawo yakirata amma bata shigaba yakumayin tsaki, afili yace mi yarinyarnan take nufi danine?.
    Ganin wankin hula zai kaishi dare yasakashi mik'ewa yafito, fitilir falo yakunna Dan har ankashe alamar sunma kwanta kenan, le6ensa yacije yanufi d'akin Rahman.
    Nanma fitilar akashe take saida ya kunna, yakai dubansa ga gadon Safna da Nawal ne kawai kwance suke barci, ad'an kid'ime yafara baza idanu, can yahango Rahma zaune akan sallaya tana karatun alkur'ani mai girma, ajiyar zuciya yasauke ahankali.
     Itakam Rahma tun shigowarsa tana jinsa amma ko d'agowa ta kalleshi batayiba.
    Ahankali yataka har inda take, wani d'an tsugunnon gayu yayi agabanta, ido tad'ago ta kalleshi, kallo d'aya tayi masa ta kauda kai, wani d'an murmushi yayi mai had'eda ta6e Baki, yay wani k'asa da murya yana mata kallon nan nasa na k'asan ido, Sayyada yau baza'a bani shayibane?, konayi laifine?.
    Idanunta dake cike tabda hawaye tad'ago suka had'a ido, tai saurin juya k'wayar idonta Wanda yabama Hawayen damar zubowa, alkur'anin ta ajiye tamik'e batareda ta tanka masaba tafice.
    Shima mik'ewa yayi yana murmushi azuciyarsa ya ce, "yammata kwantar da hankalinkima yanzun bada dad'ewaba zakiyi kukan mai dalili.

Ficewa yayi yakoma d'akinsa.
    Itakam tana kichin, bayan tadafa masa shayi tad'ora atire tareda yanka lemon tsami kamar yanda tasaba, d'auka tayi tanufi d'akinsa.
    Yana zaune abakin gado yajingina da fuskar gadon yana latsa waya tashigo, idanunsa yad'ago yana kallonta, itakam ko Inda yake bata kallaba taje saman dirowar gefen gado ta ajiye tiren shayin, batareda ta tanka masaba takama hanyar juyowa, da sauri bobo yarik'e hannunta, cak tatsaya amma bata juyoba, yawani narke murya can k'asan mak'oshi, miyake damunki?.
    Hawayene suka k'ara zubo mata akumatu, dama Rahma akwai arhar kuka, ganin bazata amsashiba yajawota tafad'o jikinsa, mutsu mutsun kwacewa tafara amma yay mata nagartaccen rik'o, hannunsa yasaka yakama ha6arta yarike yanamai fuskanto da fuskarta gareshi my cute kishi ko?.
   Da sauri tad'ago idonta dayay ja tana kallonsa, ya akayi yagane asirin zuciyarta, ita kanta tana mamakin yanda ta nuna kishinsa ayau, wani 6angare na zuciyarta ya ce, "kin kamu da sonsane, da sauri ta ta6e baki.
    Bobo yamatso da fuskarsa gabda tata tamkar zaimata kiss murya k'asa k'asa ya ce, " miyasa kike ta6e Baki?, kobaki yardaba kina kishina?.
    K'ok'arin mik'ewa tafarayi tana fad'in shayinkafa zai huce.
   K'ara k'ank'ameta yayi, cikin salon maganarsa ya ce, "aii shayi yagama aikinsa daga yau, saidai idan nasha da marmari amma badan damuwaba, daga yau kece zaki zama shayina.
    Da sauri ta kalleshi saikuma ta kauda kai yayinda suka had'a ido, bata fahimci Inda zancen nasa yadosaba amma taji aranta akwai shak'iyanci aciki.
   Yunk'urawa tasakeyi zata tashi, ta ce, " tonaji kabarni naje nacigaba da karatuna.
   Ayya aynanma karatu zamuyi kuma jira kigani, tashi kiyi alwala kizo.
    Dukda gabanta yafad'i amma saita dake Dan batason rud'a kanta da zargin abinda ba hakaba.
    Inada alwatafa. Tayi maganar kamar zata fasa kuka.
    OK tom tashi muyi sallah, bata musa masaba tamik'e suka hau sallaya, shine yajasu jam'i, raka'a hud'u sukayi kafin daga bisani yafara kwararo addu'oi Wanda ita bama tata6a zaton ya iyaba, daganan yadafa kanta yay addu'a da *Annabi tsira da amincin ALLAH su tabbata agareshi* ya koyar damu, yayi musu addu'oi sosai sannan suka shafa tareda mik'ewa.
    Da sauri Rahma takama hanyar ficewa, bobo yay azamar shan gabanta, idanu tad'ago tana kallonsa, yad'aure fuska tamau tamkar bashine yagama lalla6ataba yanzun, k miye haka wai?, yaushe raini yashiga tsakaninmune?.
     Yanda yacanja mata lokaci d'aya saitaji tsoransa yak'ara kamata, murya na rawa ta ce, "kayi hak'uri zanje nacanja kayane.
    Hannunta yakama zuwa gado, karki damu bama saikin canjaba yay maganar yana k'ok'arin zame dogon hijjabin dake jikinta.
    Idanu kawai Rahma ta runtse, zuciyarta sai faman bugawa takeyi da k'arfi............

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now