28

3.5K 206 1
                                    

             💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 29

*_Assalamu alaikum. Happy new Islamic year 1439AH. Wish you all the best in this new Islamic year. Amen thumma Amen._*
4⃣8⃣

Mota yakoma yad'auki d'aya daga cikin wayoyinsa, sai hura hanci yakeyi, bugu biyu akad'aga, ad'an kausashe ya ce, "Ammar ina buk'atar yaranka.
    My guy lfy kuwa?.
  Mtsooowww wasu wawaye aka turomin, so nad'an koyar dasu zaman tarbiyya ne.
   Murmushi Ammar yayi, Dan yasan waye abokin nasa, okey kabani 15m. Katsal.
   Baice k'alaba ya yanke wayar, cikin motar yakoma ya zauna, amma murfin abud'e yake, k'afafunsa duk suna k'asa.
   Mintuna kad'an saiga motar police, tuni aka yayibi karnukan farauta acewar BOBO aka watsa amota.
   Bobo yakalli police d'in ya ce, " kukaisu asibiti, abasu kulawa ta musamman, zuwa gobe kuma natsincesu a Stations, yana gama fad'a yashige motarsa.
   Suma 'yansan Dan mota suka shiga, harya tada mota wani police ya kwankwasa MASA, sauke gilas d'in yayi yana kallon matashin police d'in batareda yayi maganaba.
  Umm yaya dama cewa nayi kozamu fara rakaka inda zaka tukunna.
   Fararen idanunsa yad'ago, wad'anda ahalin  yanzu sukad'an canja kala zuwa jaa, no karka damu Musadiq kuje kukaisu asibiti, sune keda buk'atar taimako baniba, saidai zuwa gobe kutabbatar da sunk'ara cin ubansu, harsai sunfad'i wanda yaturosu.
    d'an murmushi Musaddiq yayi wanda daga gani akwai sanayya tsakaninsa da bobo, ya ce, "ok yaya ALLAH ya tsare.
   Shima bobon murmushi yayi tareda jinjinama musaddiq sannan yaja mota yay gaba.
    Musaddiq yabi motar da kallo yana murmushi, shidai arayuwarsa yana k'aunar ya Abdulmaleek domin mutumin kirkine, yanzudai kalli anturo mutane dansu cutar dashi, yakuma sassanbad'esu amma saboda adalaci ya ce, " akaisu asibita abasu kulawa ta musamman, (ALLAH sarki aunty Ni'ima, ALLAH yajik'anki, inama kina darai har yanzu, daduk gidanmu sainace kinfi kowa dace da miji nagari).
   “araina na ce, "kenan k'anin marigayiya Ni'imane shi?.”🤔

   Guri yasamu yay farking cikeda tak'ama yanufi office d'insa, sai rissinawa ma'aikatan wajen suke suna kwasar gaisuwa, ransa a6ace yake danhaka ko amsa musu bayayi, hannu kawai yake d'aga musu.
    Sakatariyarsa ta jinjina kai, aranta ta ce, " yau kuma boss afusace akazo?.
   Zama tayi bayan yashige, turare tad'auka tak'ara fesama jikinta tareda k'ara gyara  fuskarta, sannan tanufi office d'in.
       Kamilu masinja yata6e baki yana fad'in yarinya wahala bata ishekibane, nasan ko matan duniya sun k'are wlhy oga bazai sokiba.
    Ahankali ta tura k'ofar tashiga, yana zaune akan kujerarsa ta alfarma, kwance yake acikin kujerar idonsa alumshe yanad'an lilawa ahankali, tabishi da kallo zuciyarta na zungurarta da wani Abu, a zuciyarta ta ce, "ALLAH ya mallaka minkai amatsayin mijina.
 
Na ce, " hummm."

K'arasawa tayi Inda firij yake, tad'akko drinks da cup tanufi inda yake.
    Saida tagama tsiyaya lemon sannan ta ce, "oga ga abinsha ko kana buk'ata?.
    Baice mata komaiba, saidai yabud'e idanunsa dasukayi d'anja Dan 6acin rai.
   Waye yazo nemana?, yafad'a cikeda karsashi.
    Tuni takama kanta, cikin d'ari² ta ce, ''mutum 3 sunzo nemanka amma biyu sun had'u da yalla6ai Kamal.
   Ya ce, "d'ayanfa?.
Ta had'iye yawu kuut, d'yan Ra'is ned'an gidan........ Hannu yad'aga mata alamar baya buk'atar k'arin bayani, yay mata nuni tatafi.
   Tafiya take cikeda salo tana juya mazaunai, hartakai k'ofa ya ce, "k zonan.
   Cak tatsaya k'irjinta na dukan uku², ahankali tajuyo saitaga bama ita yake kalloba waya yake dannawa, jiki a sanyaye tace sir gani.
     Idanunsa akan waya ya ce, "k sau nawa zan fad'a miki karki sake zuwamin nan da k'ananun kaya office?.
   A zuciyarta ta ce, " danka k'yasane, amma afili saitace sorry sir zan kiyaye.
   Tsaki yaja, har yanzu idonsa nakan waya ya ce, "wlhy daga yau kika sake banzar shiga kikazomin office abakin aikinki, 6acemin anan!!!!.
    Dasauri tafice Dan atsawace yay maganar.
   Yay kwafa tareda fad'in stupid gal kawai.
    Waya ya d'auka yakira kamal, bugu d'aya ya d'auka, kamal kana office ne?. Eh Abdulmaleek, ka isone?.
   " eh yanzu na k'araso".
   Okey ina zuwa.
     Laptop yajawo yafara danne dannensa, bayan wasu 'yan mintuna saiga kamal, hannu yabashi suka gaisa, sannan ya zauna.
   Wai ina ka mak'alene?.
   Laptop d'in gabansa ya ture gefe, yadafe tebir yana kallon Kamal, kabari kawai d'an uwa inacan an ritsani za'a kashe.
    Ban ganeba?, kisa kamar ya?.
    Ajiyar zuciya bobo ya sauke, ya CE, "wlhy kuwa kamal, wasu k'anan karnukan farauta aka turo waisu kar6i takardu a hannuna, nasandai bai wuce aikin wawayennan ba.
     Suwa kenan?.
Ra'ees da babansa mana, Dan babu wasu takardu ahannuna saina kes d'insa, kuma sakatariyata tace yazo nemana.
   Kwarai kuwa d'azu Nazo danmuyi magana baka nan, to ayayin shigowata mun had'u, zaifita nikuma zan shigo.
    Humm, kamal lokaci yayi dazan fito naci uban mutanen nan fa.
   A'a Abdulmaleek karkayi haka, har yanzu munada sauran bincike kaima kasani.
   Hakane, amma wlhy natsanesu.
   Wlhy nima hakantake, yanzudai bara naje, inada wata shari'a anjima kad'an, idan mungama zan dawo.
   Okey saika dawo to.
    
Tunda kamal yafita yabar office d'in bobo yafad'a duniyar tunani, tunanin Rahma ya kanainaye zuciyarsa gaba d'aya, haka kawai yarinyar tana birgeshi, ko kad'an batada damuwa.
    Murmushi yayi tareda kauda tunaninta yamaida hankalinsa ga tuno Wanda zai iya turo masa 'yandaba,  yamik'e Dan har yanzu ransa a6ace yake, wani wawan huci yafurzar tareda naushin iska, waini za'a turoma 'yan daba yafad'a cikin k'araji, yacije le6ensa yana gyad'a kai humm zanyi maganin koma wane d'an iskane.
     K'arasawa yayi gaban firij ya tsiyaya lemo akofi yakoma jikin windown office d'in na gilas ya tsaya, hannunsa d'aya a aljihu d'aya rik'eda kofin.
    Ahankali yakai kofin bakinsa yakur6i lemon, idonsa akan mutanen dake fitowa awasu bak'ak'en jeep,  Alhaji Abdurazak yafad'a yana gyad'a kai tareda ta6e baki, yad'anyi shiru alamar tunani, amma miyasa tunanina bai kawomin kai acikin wad'anda zasu iya turamin 'yan daba ba?.
   Yasaki murmushin nan nasa na mugunta.
    Sakatariya taturo k'ofar da sallama.
   Bai juyoba amma ya amsa sallamar.
   Ta ce, "sir.......
Hannu yad'aga mata, ya ce, " kice yashigo.
            Tad'an zaro ido Dan abin yabata mamaki, bayau Alhaji abdurrazak yafara zuwa office d'innan ba, kuma duk sanda yazo oga baya bashi damar shigowa, Amman yau tunkan tafad'i ko waye yace yashigo, kuma tasan yagansa ta inda yake tsaye, kai lamarin da mamaki.
  Itadai haka tak'arasa tasanar da Alh Abdurrazak, shima abin yabashi mamaki amma saiyayi tunanin ko bobo yaji tsorone.
     
Bobo yana tsaye baikuma juyoba har Alhaji ya zauna, saida yaja tsawon Minti biyu sannan yajuyo, taku yakeyi cike da isa harya k'araso mazauninsa.
    Abin ya harzuk'a Alhaji amma saiya dake.
      Bobo dake lila kujerarsa ahankali, idonsa akan alhajin ya ce, "Alhaji mike tafe dakaine?, yay maganar cikin salonsa na isa.
      Alhaji yacije le6en jin haushi, saikuma yayi murmushi Barrister nazo maka da Business ne.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz