47

3.5K 197 1
                                    

              💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 48

Kasancewar yau weekend bobo yana gida, yanzu ma haka yana kwance bisa gadonsa dagashi sai wando 3½ da t-shirt mara nauyi, gefensa Nawal ce kwance tana barci, sai Rahma dake d'an kai kawo atsakar d'akin tsakanin dirowa da gado, kayan bobo damai wanki yakawo take shiryawa, kad'an kad'an takan yamutse fuska da cije le6enta, bobo daketa binta da kallo tun d'azun danba k'aramin tafiya dashi dressing nata yayiba, sanye take da jins blue yasha adon duwatsu daga saman cinyarta saikuma Riga pink t-shirt ta mata, kanta babu d'ankwalli tadaiyi farking nasa da pink d'in ribom, gashin yaywani Tim atsakkiya saboda kasancewarsa roba roba, yad'an lumshe idonsa yana shak'ar kamshinta daya baza d'akin, dukkuma motsin datayi saiya bigi hancinsa.
    Rahma dake gyara linkin wasu kaya ta ce, "oga me wannan kalonfa?.
    d'an murmushi yayi yana k'ara gyara kwanciyarsa har yanzu idonsa akanta, murya akasalace ya ce, "my cute zokiji wata magana mana.
    'Yar dariya tayi tareda nok'e kafad'a ta ce, " nak'i wayon, nakula yau sokake kawai mushiririce agidannan batareda nayi aikin komaiba, kallifa agogo har 12 tayi amma banshiga kicinba, mikakeso muci da rana?.
      Wata Narkakkiyar dariya yayi sannan Yakuma juya kwanciyarsa zuwa gareta Dan yanzun takoma jikin dirowa.
    Ya ce, "to aii Indai dan tanine yau kiwuni ajikina kina bani ni'imtaccen k'amshinki ina shak'a tareda jin d'umin lallausar fatarki sannan naringa kallon k'yawawan idanunnan naki fararen wad'anda sai antara mata dubu ake samun mace d'aya mai irinsa, hakan kawai ya wadatar dani kuma zai k'osar dani fiyeda abincin dazanci.
       Yabama Rahma dariya, Dan haka dariya takeyimasa sosai harda wata shashsheka mai d'aukar hankali dakuma kashe jiki, aikodai idanma tarkone Rahma keson d'anawa to tayi kamu, Dan kuwa tuni bobo ya narke agadon yana binta da wani shu'umin kallo, itakam dariyarta tacigaba dayi batareda tasan tarkonta Yakama zaki ba, kayan dasuka rage ta ida kwashewa tasaka adirowa, ganin yana niyyar sakkowa daga gadon yasata fita ad'akin dad'an gudunta, dariya tabashi yazauna abakin gado yanayi.
    Itakam kichin tanufa domin d'ora girkin rana, Abu naga tasamu tarufe hancinta sannan ta kunna gas, yau wajen kwana biyu kenan batason kamshin gas d'innman, idan zatayi girki saita to she hanci shima a daddafe take gamawa, yau kuma ga abun yana Neman had'e mata biyu Dan cikinta ciwo yakeyi yana daurewane kawai.
     Ruwan shinkafa tafara d'orawa sannan tabud'e firij tad'ebo naman kaji zata wanke, wani wuntsilawa da cikinta yayi ya tilasta mata rik'e murfin firij d'in, tadafe cikinta jitake tamkar tafasa kuka.
     Daidai nan bobo yashigo kichind'in da zummar tayata aikin dan dama duk weekend tare suke aikin gidan, haka zaita tayata tana hanashi, amma saiyace yana koyi da ANNABIN ALLAH ne, Dan wannan sunnace mai k'arfi, tun tanajin kunyar idan yana tayata suyi bak'i harma yanzu tasaba abin yazamemata jiki.
    Ganin takifa kanta tayi shiru yasa bobo fad'in lfy kuwa my Nusfuhayat?.
     Bata iya basa amsaba saidai tad'aga MASA hannu, da Sauri ya iso Inda take, tabaya ya rungumota yana k'ok'arin juyo da ita, aijitayi tamkarma yak'ara mata ciwonne, tai saurin k'adandaneshi tana fad'in wayyo ALLAHna dadyn Nawal cikina, wayyo kamar ana tsitstsinkamin hanjina, da Sauri yazame abinda tarufe hanci dashi, aiko tana shak'ar k'amshin gas d'in sai yunk'urin amai, da gudu ta fisge jikinta daga gareshi ta arce waje, shima take mata baya yayi.
     Abayin dake falon taja birki amai tafara zazzagawa kamar zata amayar da kayan cikinga, bobo dukya rud'e yarik'eta sai sorry yake mata.
     Saida tagama yataimaka mata tawanke jikinta shikuma ya wanke Inda ta 6ata, cak yad'auketa suka nufi falo, zaunar da ita yayi ajikinsa yana fad'in sorry my cute duk-ya rud'e tamkar zaiyi kuka, cikinne yak'ara murd'a mata takuma k'ank'amesa tana kuka.
      Shima sosai ya tallafota jikinsa, tuni ya janye hannunta daga kan cikin ya maye gurbin wajen danasa yana shafawa ahankali, can azab ta isheta takuma k'ank'amesa tana ambatar sunan ALLAH, tare suka k'arashe da bobo Daka gansa kasan yana cikin damuwa.
      Ganin abun NATA k'ara gaba ya ce, "my Nusfulhayat Kodai asibiti zamuje?.
     Da Sauri ta girgiza MASA kai tana cije le6e, hawaye da gumi kam sun jik'e fuskarta sharkaf dukda da AC dake aiki a falon.
       Hijjab d'inta datakan ajiye afalo Indai tasan k'ananun kayane ajikinta, gudun kar bak' yazo yasa takan ajiye, bobo yajawoshi yana share mata gumi da hawayen dasukaima fuskarta ado, wata damk'a data MASA yasakashi fad'in uchch my cute, ita batamasan yanayiba takanta take kawai, wayarsa yad'auka yakira ya sulaiman, ko gaisuwa bai tsaya sunyiba yafad'a MASA abinda ke faruwa, da Sauri shima ya sulaiman ya ce, "ganinan zuwa to.
            Cikin mintuna k'alilan ya sulaiman ya iso gidan, har yanzu Rahma tana jikin bobo, kai tsaye cikin gidan ya sulaiman yashigo.
       Bobo yad'auki hijjab d'inta yasakamata, hakan yayi daidai dashigowar ya sulaiman, basu tsaya ko gaisuwaba yashiga dubata, 'yan tambayoyi yafara mata wad'anda duk cikin kuka da zafin ciwo take amsa masa.
     Ya sulaiman yabama bobo wata kwalba, Abdulmaleek kakaita tayo fitsari mugani.....
     Aibaima bari ya sulaiman ya k'arasaba Yasureta sai bathroom d'in dake falon, fitsari tayi a 'Yar kwalbar sannan suka fito, nanmadai d'akkota yayi dukda tanata nok'e nok'e wai bataso yabarta zata iya da kanta, bai saurareta yasunkuceta suka fito.
     Saman doguwar kujera ya direta sannan yamik'ama ya sulaiman kwalba.
         Ya sulaiman yayi gwajin ciki, ganin abinda tsinken yanuna yad'ago yana fad'in Alhmdllh, fuskarsa cikeda murmushi.
     Bobo dake binsa da kallon mamaki ya ce, "yaya lfy dai?.
    Jinjina kai ya sulaiman yayi ya ce, "congratulations my lil bobo, Nawal tasamu k'ani ko k'anwa.
   Rahma jitayi cikinta yak'ara juyawa Dan tsoro, shikam bobo Baki ya washe tareda d'aga hannu sama ya ce, "Alhmdllh ala kulli halin", yataso suka rungume juna shida ya sulaiman, ya sulaiman dai sai dariya yake masa.
    Nandai yarubuta maganin dazata buk'ata sannan yamata allura wadda saida akasha fama tayarda akayi, sai sinne kai take Dan kunya tak'i yarda su had'a ido da bobo barema ya sulaiman.
        Cikin mintuna kad'an barci ya d'auketa.
   Ya sulaiman yakalli bobo, Abdulmaleek kamarfa k'auri nakeji.
   Da Sauri bobo yamik'e yana fad'in ya ilahi wallahi na manta tad'ora girki.
    Cikin hanzari ya sauke tukunyar datasaka ruwan zafin shinkafa harya k'one kamas shine tukunyar tafara k'auri.
   Kashe gas d'in yayi yafito.
   Ya sulaiman yamik'e, Abdulmaleek bara nawuce gida.
    Kai yaya tun yanzu?, koma 'Yar hira bazaka tsaya ayiba?.
   Dafa kafad'ar bobo yayi sorry bobon Ammi zanje wajen antynka kasan irin wannan ranarce kawai mukeda damar kasancewa da iyali.
   Murmushi bobo yayi ya ce, " hakane kam yayana.
   fita sukayi suna dariya, saida bobo yaga fitarsa sannan yadawo gida.
   d'aukar Rahma yayi yamaida d'akinsa, shima yakwanta suka hau barci abinsu.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now