33

3.5K 216 0
                                    

             💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 34

Jin motsin takun mutum yasakashi d'agowa, dararan idanunnan nasa masu haske yasauke akanta, wad'anda ayanzu sukad'an canja kala zuwa jaa.
     Da sauri takauda nata idon Dan bazata juri kallonsaba, lokuta da dama idanunsa suna saurin rikita mata lissafi.
     Lafiya dai?, bobo yay maganar fuska ad'aure.
   Yanayinsa yasaka jikinta yin sanyi, danya d'aure mata fiye da kullum, amma saita fuske, ta ce, "kayi hak'uri inaso muyi maganane Dan ALLAH.
     Idonsa yamaida ga littafin tareda jan d'an k'arami tsaki, da hannu yanuna mata wajen zama batareda yad'agoba.
      Safna tagyara kujera tareda d'aukar handky d'insa dake gefen k'afarsa ta goge kujerar sannan tazauna.
     Shikam cigaba yayi da karatunsa.
    Saida tayi masa kallon tsaf, sanye yake da kayan barci wandonsa iya guywa sai k'aramar riga mara hannu kayan duka jajayene sunyi bala'in haska farar fatarsa, aranta ta ce, " kai guy d'in nan yahad'u tako ina, komai nasa maik'yawune, kowacce irin sutura yasaka takan zauna daidai da tsarin hallittarsa, kallidai yanda kayan barci suka masa k'yau, shiyyasa idan yad'auki ainahin dressing yake rikita kwanyar mata........
      Jin tayi shiru saiya d'ago idanunsa yana kallonta, saiyaga tak'ura masa ido, k'ara d'aure fuska yayi fiye da d'azu, ina saurarenki, yayi maganar cikeda karsashi..
    Tuni safna tashiga hankalinta, ta tattaro nutsuwarta guri d'aya, tawani lankwashe murya tamkar wadda take agaban mijinta.
    _“ya Abdulmaleek Dan ALLAH da farkodai ina mai neman gafararka.”_
    Idonsa nakan buk ya ce, "dakikaimin mi?, ince sai anma mutum laifi ake bashi hak'uri?, nikuma bakiminba.
      Tunda yafara maganar tak'urama bakinsa idanu, Dan inbaka kasa kunnenkaba bazakaji abinda yake fad'aba, itama kanta Dan darene gari yayi tsit shiyyasa takejinsa, ahankali yake maganar kuma muryarsa cikin wani yanayi, mai lurane kawai zai fahimceshi ko kuma fahimtar halin dayake ciki.
     Ahankali tasauke ajiyar zuciya tareda gyara zama, takuma marairaice murya can k'asan mak'oshi ta ce, "namaka laifi my Boboo!,".
     yanda tafad'i sunan nasa tareda jansa cikin salo saida yad'ago Jan idonsa yakalleta, baidaice komaiba yamaida idanunsa yalumshe.
      Wani murmushi safna tasaki sannan tacigaba dafad'in nikuwa namaka laifi Dan ance na aureka amma nak'i, alokacin bansan kai baneba wlhy dabazan k'iba.
    Ya maleek tunranar Dana fara ganinka a school d'inmu nakamu da sonka mai tsanani.
     Da sauri yad'ago kai yana kallonta, saidai yakasa furta komai Dan mamakinta.
    Tacigaba, wlhy sonkane yahana nayima iyayena biyayya dakuma rashin sanin kaine mijin dasuka za6amin.
    Saidai randa ummi ta aikoni wajen Rahma nashiga matuk'ar rud'ani danadamar bijirema iyayena, lallai ranar zuciyata yayi tamkar zata fashe......
        Bobo yakatseta da fad'in no wonder shiyyasa kikamana pretending wai kina jin juwa koma mine?, yafad'a yana yatsine fuska tamkar yaga wani tutu.
    Safna tasakko tatsugunna agabansa tana hawaye, Dan ALLAH my boboo kataimakeni ka aureni?.
     Wata uwar harara bobo yajefeta dashi, cikin kaushin murya ya ce, "bakida hankaline?, kokin manta nid'in *_MIJIN K'ANWARKI NE!!?._*
     Itama cikin d'aga murya ta ce, " inacikin hankalina kuma INA kan sani, Maleek nasan bakason Rahma, itama batasonka, Niko ina Sonka.......
    Da Sauri yakatseta dafadin ubanwaye yagaya miki?.
      Tazaro manyan idanunta, ta ce, "zamankune yafad'amin, Dan wlhy ko rantsuwa nayi bazanyi kaffaraba baku ta6a had'a shimfid'a da Rahma ba, wannan yana cikin dalilin zamanka anan gurin, idan kuma nayi k'arya karantse mini da ALLAH kata6a had'a shinfid'a da ita, nikuma indai kayi zan hak'ura dakai nabar mata.
     Harara bobo yasakar mata, to ina ruwanki?.
    Tayi wani murmushin mugunta, daruwana maleek harda d'an tsaki, domin kuwa Sonka nakeyi, sokuma mai tsanani, Dan ALLAH kasaki Rahma kamaye gurbinta dani, wlhy namaka alk'awarin maka biyaya, zankuma cire maka duk wani kunci da damuwar dake tare da kai....
     Cikin tsawa bobo ya ce, " Dallah malama yimin shiru, yay murmushin nan nasa na munguta sannan yasauke k'afarsa k'asa, Yakuma gyara rungumar fillonsa yana kallonta, ya ce, "yarinya bakida abinda zaki iya mayemin gurbin my cute dashi, dantafiki komai wlhy, k'yawun sura ilimin addini iya zama da mutane hankali nutsuwa k'yak'yk'yawan tunani uwa uba hankali, yoni nayi canjinki da Rahma aina fad'o wlhy nakuma ci baya arayuwata, kisa azuciyarki dama can ALLAH yarubuta Rahma CE matata bakeba, ubangiji yagwada kine kawai danyaga k'arfin imaninki, amma saikika Nuna masa kinfisa wayo, to wallhy kisani kullum godema ALLAH nake dakikace bazaki aureniba, mahalliccina maisona da nasara yabani Rahma amadadinki, zuciyarki tadaina shirya miki k'aryar zan iya rabuwa da Rahma, wlhy yaudararki kawai takeyi, nida Rahma mutu karaba takalmin kaza.
   _Yay k'asa da murya tamkar mai rad'a, ya ce, "Rahma sai Abdulmaleek, Abdulmaleek kuma sai Rahma k'yak'yk'yawa mafi k'yawu acikin mata._
    Yafigi filonsa da littafi yay cikin gida yana 'Yar dariyar mugunta.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now